Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

FARA MAGANA DA MUTANE

Yoh. 4:​6-9

DARASI NA 1

Ka Fadi Abin da Mutumin Zai So

Ka Fadi Abin da Mutumin Zai So

Ƙaꞌida: “Ƙauna . . . ba ta sonkai.”—1 Kor. 13:​4, 5.

Abin da Yesu Ya Yi

1. Ka kalli BIDIYON, ko ka karanta Yohanna 4:​6-9. Saꞌan nan ka yi tunani a kan tambayoyin nan:

  1.    Mene ne Yesu ya lura game da matar kafin ya fara magana da ita?

  2.   Yesu ya ce mata: “Ba ni ruwa in sha.” Me ya sa ya dace sosai da Yesu ya fara maganar da cewa ta ba shi ruwa?

Mene ne Abin da Yesu Ya Yi Ya Koya Mana?

2. Idan muka soma da zancen wani abu da mutumin yake so, ba mamaki mutumin zai saurare mu da kyau.

Ka Yi Koyi da Yesu

3. Ka yi shirin tattauna batutuwa dabam-dabam. Kar ka nace cewa sai abin da ka shirya ne za ka tattauna da mutum. Za ka iya somawa da abin da yake zuciyar mutane a yau. Ka tambayi kanka cewa:

  1.    ‘Me aka faɗa a ƙaffofin yaɗa labarai?’

  2.   ‘Hirar me maƙwabtana da abokan aikina ko ꞌyan ajinmu suke yi?’

4. Ka dinga lura. Ka tambayi kanka cewa:

  1.    ‘Me mutumin yake yi? Mene ne wataƙila yake tunani a kai?’

  2.   ‘Mene ne tufafin mutumin, da yanayin fuskarsa, ko gidansa suka nuna mini game da imaninsa da kuma alꞌadarsa?’

  3.   ‘Zai dace in yi magana da shi a wannan lokacin?’

5. Ka saurara.

  1.    Kar ka yi magana da yawa.

  2.   Ka faɗi abin da zai sa mutumin ya bayyana raꞌayinsa. Idan ka ga ya dace, ka yi masa tambayoyi.

KA KUMA KARANTA

Mat. 7:12; 1 Kor. 9:​20-23; Filib. 2:4; Yak. 1:19