Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

FARA MAGANA DA MUTANE

Yoh. 9:​1-7

DARASI NA 3

Kirki

Kirki

Ƙaꞌida: “Ƙauna tana . . . da kirki.”—1 Kor. 13:4.

Abin da Yesu Ya Yi

1. Ka kalli BIDIYON, ko ka karanta Yohanna 9:​1-7. Saꞌan nan ka yi tunani a kan tambayoyin nan:

  1.    Yesu ya fara da yi wa makahon waꞌazi ne, ko warkar da shi?—Ka duba Yohanna 9:​35-38.

  2.   Me ya sa mutumin ya saurari waꞌazin da Yesu ya yi masa?

Mene ne Abin da Yesu Ya Yi Ya Koya Mana?

2. Idan mutum ya ga cewa mun damu da shi, zai so ya saurare mu.

Ka Yi Koyi da Yesu

3. Ka nuna ka damu da mutumin. Ka yi tunanin yadda za ka ji a ce kai ne kake yanayinsa.

  1.    Ka tambayi kanka cewa: ‘Mene ne yake damun sa? Mene ne zai so a yi masa?’ Idan ka yi hakan, za ka iya taimaka wa mutumin daga zuciyarka.

  2.   Idan mutum ya gaya maka yadda yake ji game da wani abu, ko ya ambaci wata matsala da yake fuskanta, kada ka share shi ko ka canja maganar. Ka saurare shi. Hakan zai nuna cewa ka damu da shi.

4. Ka yi magana da alheri kuma ka daraja shi. Yadda kake magana ya nuna cewa ka damu da mutumin kuma kana so ka taimaka masa da gaske. Ka yi tunani da kyau kafin ka yi magana, kuma ka guji faɗan abubuwan da za su ɓata masa rai.

5. Ka zama mai taimako. Ka yi tunani a kan hanyoyin da za ka iya taimaka wa mutumin. Idan ka yi wa mutum kirki, shi ma zai so ya saurare ka.

KA KUMA KARANTA

Rom. 12:​15, 16; Gal. 6:10; Ibran. 13:16