Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

FARA MAGANA DA MUTANE

A. M. 26:​2, 3

DARASI NA 4

Saukin Kai

Saukin Kai

Ƙaꞌida: “Cikin sauƙin kai kuma bari kowa ya ɗauka ɗanꞌuwansa da muhimmanci fiye da kansa.”—Filib. 2:3.

Abin da Bulus Ya Yi

1. Ka kalli BIDIYON, ko ka karanta Ayyukan Manzanni 26:​2, 3. Saꞌan nan ka yi tunani a kan tambayoyin nan:

  1.    Saꞌad da Bulus yake magana da Sarki Agiriffa, ta yaya ya nuna sauƙin kai?

  2.   Maimakon manzo Bulus ya girmama kansa, ta yaya ya sa Sarki Agiriffa ya mai da hankali ga abin da Kalmar Allah ta ce?—Ka duba Ayyukan Manzanni 26:22.

Mene ne Abin da Bulus Ya Yi Ya Koya Mana?

2. Mutane za su ji daɗin saƙonmu idan muka yi musu magana cikin daraja da kuma sauƙin kai.

Ka Yi Koyi da Bulus

3. Kada ka rena mutumin. Kada ka yi kamar ka san kome kuma mutumin da kake magana da shi bai san kome ba. Ka yi magana a hanyar da za ta nuna cewa kana girmama mutumin.

4. Ka nuna cewa abin da kake gaya wa mutumin daga Littafi Mai Tsarki ne. Kalmar Allah za ta iya taɓa zuciyar mutum kuma ta canja tunaninsa. Idan muka yi amfani da ita, za mu ba mutane dalili mai kyau na kasancewa da bangaskiya.

5. Kada ka yi fushi. Kada ka nace cewa sai mutumin ya yarda da abin da kake faɗa. Kuma kada ka yi gardama da shi. Idan ba ka yi fushi ba kuma ka kyale mutumin saꞌad da gardama ta taso, hakan zai nuna cewa kana da sauƙin kai. (K. Mag. 17:14; Tit. 3:2) Kuma idan ka yi magana da faraꞌa, hakan zai iya sa mutumin ya saurare mu a nan gaba.

KA KUMA KARANTA

Rom. 12:​16-18; 1 Kor. 8:1; 2 Kor. 3:5