Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

FARA MAGANA DA MUTANE

A. M. 17:​22, 23

DARASI NA 5

Ka Yi Magana da Basira

Ka Yi Magana da Basira

Ƙaꞌida: “Bari maganarku ta kasance da alheri.” —Kol. 4:6.

Abin da Bulus Ya Yi

1. Ka kalli BIDIYON, ko ka karanta Ayyukan Manzanni 17:​22, 23. Saꞌan nan ka yi tunani a kan tambayoyin nan:

  1.    Yaya Bulus ya ji da ya ga yadda mutanen Atina suna bauta wa allolin ƙarya?—Ka duba Ayyukan Manzanni 17:16.

  2.   Ta yaya Bulus ya nuna basira a yadda ya yi wa mutanen Atina waꞌazi?

Mene ne Abin da Bulus Ya Yi Ya Koya Mana?

2. Mutane za su fi sauraran mu idan muna mai da hankali ga abubuwan da za mu faɗa, da yadda muke faɗin su, da kuma lokacin da muke faɗin su.

Ka Yi Koyi da Bulus

3. Ka yi amfani da kalamai masu daɗin ji. Alal misali, idan kana magana da wanda ba Kirista ba, mai yiwuwa za ka bukaci ka canja yadda za ka yi masa magana game da Littafi Mai Tsarki ko kuma game da Yesu.

4. Kada ka yi saurin yi masa gyara. Ka bar shi ya faɗi abin da ke zuciyarsa. Idan ya faɗi abin da bai yi daidai da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba, ka guji yin mūsu da shi nan take. (Yak. 1:19) Idan ka saurare shi da kyau, za ka san abin da ya gaskata da kuma dalilin da ya sa ya yarda da hakan.—K. Mag. 20:5.

5. Ka yarda da shi kuma ka yaba masa a lokacin da ya dace. Idan ya buga kirji cewa addininsa na koyar da gaskiya. Ka yi ƙoƙari ka yi magana a kan abin da ku biyun kuka gaskata da shi. Sai a-hankali-a-hankali, ka soma koya masa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce.

KA KUMA KARANTA

K. Mag. 25:15; 2 Tim. 2:​23-26; 1 Bit. 3:15