Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KOMAWA ZIYARA

Yoh. 7:​3-5; 1 Kor. 15:​3, 4, 7

DARASI NA 8

Hakuri

Hakuri

Ƙaꞌida: “Ƙauna tana da haƙuri.”—1 Kor. 13:4.

Abin da Yesu Ya Yi

1. Ka kalli BIDIYON, ko ka karanta Yohanna 7:​3-5 da 1 Korintiyawa 15:​3, 4, 7. Saꞌan nan ka yi tunani a kan tambayoyin nan:

  1.    Da farko, yaya ꞌyanꞌuwan Yesu suka ji game da waꞌazinsa?

  2.   Mene ne ya nuna cewa Yesu bai fid da rai a kan ɗanꞌuwansa Yaƙub ba?

Mene ne Abin da Yesu Ya Yi Ya Koya Mana?

2. Muna bukatar mu yi haƙuri don yakan ɗauki dogon lokaci kafin wasu mutane su amince da saƙonmu.

Ka Yi Koyi da Yesu

3. Ka yi amfani da wata hanya dabam. Idan mutumin bai amince a yi nazari da shi nan da nan ba, kada ka sa shi dole. Idan ka ga ya dace, ka yi amfani da talifofi ko bidiyoyi don ka taimaka masa ya ga yadda muke nazari da mutane da kuma yadda nazarin zai amfane shi.

4. Kar ka gwada shi da wani. Mutane ba iri ɗaya ba ne. Idan wani a iyalinku ko wani da ka yi masa waꞌazi yana jinkiri, ba ya so ka yi nazari da shi ko ya amince da wata koyarwar Littafi Mai Tsarki, ka yi ƙoƙari ka san dalilin da ya sa yake hakan. Shin yana jinkiri ne don akwai wani abin da ya yi imani da shi da yake da muhimmanci a gare shi? Ko dai danginsa ko maƙwabtansa ne suke takura masa? Ka ba shi lokaci don ya yi tunani a kan abin da ka ce kuma ya ga muhimmancin koyarwar Littafi Mai Tsarki.

5. Ka sa mutumin a cikin adduꞌa. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka kada ka fid da rai, kuma ya ba ka basira. Ka roƙe shi ya taimaka maka ka san wanda ba ya son waꞌazin da gaske da kuma lokacin da ya dace ka daina ziyartar sa.—1 Kor. 9:26.

KA KUMA KARANTA

Mar. 4:​26-28; 1 Kor. 3:​5-9; 2 Bit. 3:9