Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KOMAWA ZIYARA

Mar. 6:​30-34

DARASI NA 9

Tausayi

Tausayi

Ƙaꞌida: “Ku yi farin ciki tare da masu farin ciki, ku yi kuka tare da masu kuka.”—Rom. 12:15.

Abin da Yesu Ya Yi

1. Ka kalli BIDIYON, ko ka karanta Markus 6:​30-34. Saꞌan nan ka yi tunani a kan tambayoyin nan:

  1.    Me ya sa Yesu da almajiransa suka so su je “wurin da ba kowa”?

  2.   Me ya sa Yesu ya koyar da jamaꞌar?

Mene ne Abin da Yesu Ya Yi Ya Koya Mana?

2. Tausayi zai sa mu damu da mutane, ba abin da muke so mu gaya musu kawai ba.

Ka Yi Koyi da Yesu

3. Ka saurari mutumin da kyau. Ka ba shi dama ya gaya maka abin da yake zuciyarsa. Idan yana gaya maka yadda yake ji, ko abin da yake damun sa, ko cewa bai yarda da abin da ka faɗa ba, kar ka katse shi ko ka yi kamar ba ka ji abin da ya ce ba. Idan ka saurare shi, hakan zai nuna cewa ka damu da shi.

4. Ka yi tunani a kan mutumin. Bisa ga hirar da kuka yi da shi, ka tambayi kanka cewa:

  1.    ‘Me ya sa yake bukatar ya san gaskiya?’

  2.   ‘Ta yaya yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai inganta rayuwarsa a yanzu da kuma a nan gaba?’

5. Ka yi magana a kan abubuwan da za su taimake shi. Ba tare da ɓata lokaci ba, ka nuna masa yadda yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai amsa tambayoyinsa, kuma ya taimaka masa a rayuwarsa ta yau da kullum.

KA KUMA KARANTA

Rom. 10:​13, 14; Filib. 2:​3, 4; 1 Bit. 3:8