Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ALMAJIRTARWA

Yoh. 3:​1, 2

DARASI NA 10

Yin Niyya Sosai

Yin Niyya Sosai

Ƙaꞌida: ‘Mun ji daɗin yi muku waꞌazin labari mai daɗi na Allah, ba waꞌazi kaɗai ba, amma mun ji daɗin ba da rayukanmu, saboda kun shiga ranmu sosai.’—1 Tas. 2:8.

Abin da Yesu Ya Yi

1. Ka kalli BIDIYON, ko ka karanta Yohanna 3:​1, 2. Saꞌan nan ka yi tunani a kan tambayoyin nan:

  1.    Me ya sa Nikodimus ya gwammace ya je wurin Yesu da dare?—Ka duba Yohanna 12:​42, 43.

  2.   Me ya sa yadda Yesu ya yarda ya haɗu da Nikodimus da dare ya nuna cewa yana da niyyar taimaka wa mutane su zama almajiransa?

Mene ne Abin da Yesu Ya Yi Ya Koya Mana?

2. Muna ƙaunar mutane shi ya sa muna cike da niyyar sa su zama mabiyan Yesu.

Ka Yi Koyi da Yesu

3. Ku yi nazarin a lokaci da kuma wurin da ɗalibin yake so. Wataƙila akwai rana ko kuma lokacin da ya fi so, ko kuma zai fi so ku yi nazarin a wurin aikinsa, ko gidansa ko kuma a inda jamaꞌa suke. Idan zai yiwu, ka canja lokacin da kake ziyartarsa don ku iya yin nazarin a lokaci da kuma wurin da yake so.

4. Kada ka fasa yin nazarin. Idan za ka yi tafiya, kada ka dakatar da nazarin har sai ka dawo. A maimakon haka, ga wasu matakan da za ka iya ɗaukawa:

  1.    Za ku iya yin nazarin a wata rana dabam da wadda kuka saba.

  2.   Za ku iya yin nazarin ta waya.

  3.   Za ka kuma iya gaya ma wani ya taya ka yin nazari da shi.

5. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka kada ka gaji. Ka yi adduꞌa ga Jehobah kuma ka roƙe shi ya taimaka maka kada ka fid da rai a kan ɗalibinka, ko da ba a kullum ne yake yarda ku yi nazari ba, ko kuma yana jinkirin aikata abin da ya koya. (Filib. 2:13) Ba mamaki, ɗalibinka yana da wasu halaye masu kyau. Ka roƙi Allah ya taimaka maka ka mai da hankali ga halayen nan.

KA KUMA KARANTA

K. Mag. 3:27; A. M. 20:35; 2 Kor. 12:15