Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ALMAJIRTARWA

Mat. 6:​25-27

DARASI NA 11

Ka Koyar a Hanya Mai Sauki

Ka Koyar a Hanya Mai Sauki

Ƙaꞌida: Ku furta “zance mai-sauƙin ganewa.” —1 Kor. 14:​9, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

Abin da Yesu Ya Yi

1. Ka kalli BIDIYON, ko ka karanta Matiyu 6:​25-27. Saꞌan nan ka yi tunani a kan tambayoyin nan:

  1.    Wane kwatanci ne Yesu ya yi da ya nuna cewa Jehobah ya damu da mu?

  2.   Duk da cewa Yesu ya san abubuwa da yawa game da tsuntsaye, wane bayani mai sauƙi ne ya yi? Me ya sa yadda ya yi wannan koyarwar yake da kyau?

Mene ne Abin da Yesu Ya Yi Ya Koya Mana?

2. Idan muna koyar da mutane a hanya mai sauƙin ganewa, koyarwar za ta shiga zuciyarsu kuma ba za su manta da abin da suka ji ba.

Ka Yi Koyi da Yesu

3. Kada ka yi magana da yawa. Maimakon ka gaya wa ɗalibin duka abin da ka sani game da batun da kuke nazari, ka mai da hankali ga abin da littafin da kuke amfani da shi ya ce. Idan ka yi tambaya, ka jira ɗalibin ya ba da amsa. Idan bai san amsar ba ko ya ba da amsar da ba ta jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba, ka ƙara masa wasu tambayoyi don ya sake tunani kuma ya fahimci batun. Da zarar ka ga cewa ɗalibin ya fahimci ainihin darasin, sai ku yi gaba.

4. Ka yi amfani da abin da ɗalibin ya sani don ka taimaka masa ya fahimci sabon abu. Misali, idan za ku soma darasin da ya yi zancen tashin matattu, ka tambayi ɗalibinka don ka ji abin da ya riga ya sani game da matattu.

5. Ka yi amfani da kwatancin da ya dace. Kafin ka yi wani kwatanci, ka tambayi kanka cewa:

  1.    ‘Wannan kwatancin yana da sauƙin ganewa ne?’

  2.   ‘Ɗalibina zai yi saurin fahimtar kwatancin?’

  3.   ‘Zai taimaka masa ya tuna ainihin darasin, ko kuwa kwatancin ne kaɗai zai tuna?’

KA KUMA KARANTA

Mat. 11:25; Yoh. 16:12; 1 Kor. 2:1