Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ƘARIN BAYANI NA 3

Yadda Za Ka Yi Nazari da Littafin Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!

Yadda Za Ka Yi Nazari da Littafin Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!

An yi adduꞌa sosai da kuma bincike kafin aka wallafa littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Don ka yi amfani da littafin da kyau, ka bi shawarwarin nan saꞌad da kake nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.

Kafin ka soma nazarin

  1. 1. Ka shirya da kyau. Yayin da kake hakan, ka yi tunani a kan yanayin ɗalibinka da kuma abin da ya yi imani da shi. Ka lura da abin da zai iya yi masa wuyar fahimta ko ya yi masa wuyar bi. Ka yi laꞌakari da yadda bayanan da ke sashen “Ka Bincika” za su taimaka wa ɗalibinka. Kuma idan da bukata, ka yi amfani da su saꞌad da kuke nazarin.

Saꞌad da kuke nazarin

  1. 2. Ka soma nazarin da adduꞌa, saꞌan nan ka rufe da adduꞌa, sai dai in ɗalibin ya ce ba ya son hakan.

  2. 3. Kada ka yi magana da yawa. Ka bi bayanan da ke cikin littafin kuma ka bar ɗalibin ya faɗi abin da ke zuciyarsa.

  3. 4. Idan za ku shiga wani sabon sashe, ka karanta bayanin da ke “Abin Lura,” saꞌan nan ka ambata wasu darussan da za ku koya a sashen.

  4. 5. Bayan kun gama nazarin wani sashe, ka yi amfani da bitar sashen don ka taimaka wa ɗalibinka ya tuna wasu abubuwan da ya koya.

  5. 6. Yayin da kuke nazarin kowanne darasi:

    1. Ku karanta sakin layi da ke sashen farko na darasin.

    2. Ku karanta dukan nassosin da aka ce: “Karanta.”

    3. Idan da bukata, ku karanta wasu nassosin da aka ambata.

    4. Ku kalli dukan bidiyoyin da aka ce a kalla (Idan kuna da bidiyon).

    5. Ka yi wa ɗalibin dukan tambayoyin.

    6. Ka nuna wa ɗalibin hoton da ke sashen “Ka Yi Bincike Sosai,” kuma ka ce masa ya gaya maka yadda ya fahimci hoton.

    7. Ka yi amfani da sashen “Maƙasudi” don ka taimaka wa ɗalibinka ya san yadda yake samun ci gaba a ibadarsa. Ka ƙarfafa shi ya yi amfani da maƙasudin da aka ambata, ko ya kafa nasa, ko kuma ya yi biyun.

    8. Ka tambaye shi ko akwai wani talifi ko wani bidiyo da ya ji daɗin sa a sashen “Ka Bincika” saꞌad da yake yin shiri don nazarin.

    9. Ku yi ƙoƙari ku gama kowanne darasi a rana ɗaya.

Bayan kun gama nazarin

  1. 7. Ka ci gaba da tunani game da ɗalibin. Ka roƙi Jehobah ya taimaka wa ɗalibinka ya fahimci abin da yake koya, kuma ya ba ka hikima don ka san yadda za ka taimaka masa.