Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Bayani ga Wadanda Suka Halarci Taron

Bayani ga Wadanda Suka Halarci Taron

ASABAR DA AKE TSABTACE MAHALLI Lokacin da ke cikin baka biyu na waɗanda za su yi taron yanki a ranar Asabar da ake Tsabtace Mahalli ne. Idan za a yi taronku a Asabar da ake tsabtacce mahalli, za a yi jerin jawaban nan mai jigo: Mu Yi Amfani da Labari Mai Daɗi don Mu Yi Nasara A Kan Munanan Labarai ranar Jummaꞌa da safe maimakon ranar Asabar da rana.

BAFTISMA Za a keɓe wurin zama kusa da dakalin magana don waɗanda za su yi baftisma. Ya kamata waɗanda za su yi baftisma su zauna a wurin da aka keɓe musu kafin a soma jawabin baftisma a ranar Asabar da safe. Kowa ya zo da tawul nasa da kuma rigar da ta dace don yin baftisma.

GUDUMMAWA An kashe kuɗaɗe da yawa don shirya wajen zama da sauti da kuma wasu abubuwa da suke sa mu ji daɗin taron yankinmu, kuma hakan ya taimaka mana mu daɗa kusantar Jehobah. Idan ka ba da gudummawar kuɗi, za ka taimaka wajen biyan waɗannan kuɗaɗen, kuma za ta taimaka wa hidimar da ake yi a dukan duniya. An saka akwatuna da rubutu a kansu a wurare dabam-dabam a majamiꞌar don ka sa gudummawar ka. Za ka kuma iya ba da gudummawa ta dandalin donate.pr418.com. Muna matuƙar godiya don gudummawar da ake bayarwa. Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana alfahari da yadda kuke ba da gudummawa saboda hidimar Mulkin Allah ta sami ci gaba.

HIDIMAR BA DA KAI Idan kana so ka taimaka da wasu ayyukan da ake yi a wannan taron, ka je Sashen Samun Bayanai da Ayyuka.

JINYAR GAGGAWA Don Allah ka tuna cewa wannan wurin jinyar gaggawa ce kawai.

MATATTARIN TSINTUWA A kai dukan kayayyaki da aka tsinta Sashen Matattarin Tsintuwa. Idan wani abinka ya ɓata, ka je wannan sashen ka nema. A kai yaran da suka ɓace zuwa wannan sashen. Domin a guji shiga mawuyacin hali, muna roƙonku ku kula da ꞌyaꞌyanku, kuma su riƙa kasancewa tare da ku.

TSARIN ZAMA Don Allah, ku nuna sanin yakamata. Ku tuna cewa waɗanda za ku iya kama musu wurin zama su ne, iyalinku, da waɗanda kuke tafiya tare a cikin mota, da waɗanda kuke zama a gida ɗaya, da kuma waɗanda kuke nazari da su. Kada ku ajiye abubuwa a kan kujerun da ba ku kama ba.

ꞌYAN ATENDA Aikin da aka sa ꞌyan atenda shi ne, su taimaka muku. Don haka, muna roƙonku ku bi umurnin da suka ba ku game da faka motoci da shiga da fita daga wurin taro da kama kujera da dai makamantansu.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ce ta shirya wannan taron

© 2024 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania