Koma ka ga abin da ke ciki

Ka Yi Burin Yin Abubuwan da Za Su Taimaka Maka a Ibadarka

Ka Yi Burin Yin Abubuwan da Za Su Taimaka Maka a Ibadarka

Ka Yi Burin Yin Abubuwan da Za Su Taimaka Maka a Ibadarka

WANI masani a dā ya ce: “Idan matukin jirgin ruwa bai san inda za shi ba, ba yadda za a yi ya isa wurin, ko da yana da abubuwan da za su taimaka masa ya yi hakan.” Kalmomin nan sun nuna cewa idan muna son rayuwarmu ta zama da kan gado, dole ne mu zama da burin yin wasu abubuwa.

Littafi Mai Tsarki ya ba mu labaran mutane da yawa da suka zama da burin yin wani abu kuma suka yi iya kokarinsu don su yi shi. Alal misali, Nuhu ya yi wajen shekaru 50 yana aiki don ya “shirya jirgin ruwa domin a ceci iyalinsa.” Musa ma “ya kafa ido ga ladan da yake a gaba.” (Ibraniyawa 11:​7, 26) Magajin Musa mai suna Joshua ya yi burin cin kasar Kanꞌana da yaki bisa umurnin Allah.​—Maimaitawar Shari’a 3:21, 22, 28; Yoshuwa 12:​7-24.

A karni na farko, manzo Bulus ma ya zama da burin yin wasu abubuwa. Ya san da umurnin nan da Yesu ya bayar cewa “za a ba da wannan labari mai dadi na mulkin sama domin shaida ga dukan alꞌumma.” (Matiyu 24:14) Manzo Bulus ya yi aikin nan da kwazo domin Yesu ya gaya mishi ya yi waꞌazi game da shi ga dukan alꞌummai. Waꞌazin nan da manzo Bulus ya yi ya sa an kafa ikilisiyoyi da yawa a kasashe da yawa.​—Ayyukan Manzanni 9:15; Kolosiyawa 1:23.

Ba shakka, bayin Jehobah sun saba zama da burin yin wasu abubuwa kuma suna yin su. Ta yaya za mu zabi abubuwan da za mu yi a hidimar Jehobah? Wadanne abubuwa ne za mu iya sa a gaba a matsayin burinmu? Kuma me zai taimaka mana mu yi su?

Ta Yaya Za Mu Yi Zabin da Ya Dace?

Mutane sukan yi burin yin abubuwa dabam-dabam a rayuwa. Amma abin da mutanen Jehobah suke sa a gaba ya bambanta da abin da sauran mutane suke sakawa a gaba. Mutane da yawa a yau burinsu shi ne su sami kudi da iko. Amma ba abin da ya kamata bayin Jehobah su a gaba ba ke nan. Za mu daukaka Jehobah idan muka zama da burin yin abubuwan da za su taimaka mana mu bauta masa da kyau. (Matiyu 6:33) Kuma kaunarmu ga Jehobah da mutane ne yake sa mu zama da irin wannan burin.​—Matiyu 22:​37-39; 1 Timoti 4:7.

Zai dace mu zama da burin kara kwazo a hidimar Jehobah ko kuma mu kyautata halinmu. Ko da me muke niyyar yi, bari ya zama cewa kaunarmu ga Jehobah da mutane ne take sa mu yi shi. Amma ko da mun yi niyyar yin wani abu don muna kaunar Jehobah da mutane, a wasu lokuta yakan zama da wuya mu cim ma burinmu. Me zai taimaka mana mu cim ma burinmu?

Abin da Zai Taimaka Mana Mu Cim ma Burinmu

Za mu iya koyan darasi daga yadda Jehobah ya halicci abubuwan da ke sama da kasa. Jehobah ya kasa ayyukan da zai yi a lokuta dabam-dabam. Littafi Mai Tsarki ya kira lokutan nan ‘kwanaki.’ (Farawa 1:​5, 8, 13, 19, 23, 31) A kowace rana, Allah ya shirya abubuwan da zai yi kuma ya yi su daya bayan daya. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11) Annabi Ayuba ya ce Jehobah yana da “abin da yake so ya yi, ba mai hana shi.” (Ayuba 23:13) Babu shakka, Jehobah ya ji dadi sosai da “ya dubi dukan abin da ya yi, ya ga yana da kyau sosai”!​—Farawa 1:31.

Idan muna so mu yi abin da muka yi niyyar yi, dole ne mu mai da shi ya zama babban burinmu, wato abin da muke marmari mu ga mun yi shi. Me zai taimaka mana mu zama da irin wannan marmarin? Tun kafin duniya ta zama da siffa, kafin a sa wani abu a cikinta, Jehobah ya riga ya hangi yadda duniya za ta yi kyau idan an gama ta. Idan mu ma muka yi tunani a kan amfanin da za mu samu daga cika burinmu, hakan zai sa mu yi marmarin cika shi. Abin da ya faru da wani matashi dan shekara 19 mai suna Tony ke nan. Da Tony ya je yawon bude ido a wani ofishi na Shaidun Jehobah. Ya yi tunani sosai a kan abin da ya gani a wurin. Tun daga lokacin ya yi ta ce ma kansa, ‘da a ce ni ne nake zama a nan kuma ina hidima, yaya zan ji?’ Wannan tunani da ya yi ta yi a kan abubuwa masu kyau da ya gani a wurin ya sa ya dage don ya cancanci zuwa wurin. Ya yi farin ciki sosai da bayan wasu shekaru aka ce ya je ya yi hidima a wurin.

Wani abu kuma da zai taimaka mana mu cim ma burinmu shi ne yin tarayya da wadanda suka taba yinsa. Akwai wani mai suna Jayson da shekarunsa 30 ne. Da yake karami, baya son yin waꞌazi. Amma a kwana a tashi, ya so yin waꞌazi sosai. Har ya zama majagaba da ya gama makarantar sakandare. Ya aka yi Jayson ya so yin hidimar majagaba? Shi kansa ya ce: “Yin hira da majagaba da yin waꞌazi tare da su ya sa ni ma na so in yi hidimar.”

Rubuta Abin da Muke Burin Yi Zai Taimaka

Idan muka furta abin da muke niyyar yi, hakan zai sa mu fahimce shi da kyau. A Littafi Mai Tsarki, Sulemanu ya ce kalmomin mutane masu hikima za su taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau. (Mai-Wa’azi 12:11) Idan muka rubuta wadannan kalmomin, zai yi wuya mu manta su. Shi ya sa Jehobah ya umurci sarakunan Israꞌila su kofe dokokinsa da hannunsu. (Maimaitawar Shari’a 17:18) Za mu iya rubuta abin da muke burin yi da kuma matakin da za mu dauka don mu yi shi. Ban da haka ma, zai dace mu rubuta matsalolin da za mu iya fuskanta da yadda za mu magance su. Har ila, idan akwai abin muke bukatar mu koya don mu cim ma burinmu, yin bincike da kuma neman shawara za su taimaka mana.

Akwai wani danꞌuwa mai suna Geoffrey da ya dade yana hidimar majagaba na musamman a kasar Asiya. Burin yin wasu abubuwa ya taimaka masa ya sami kwanciyar hankali. Da matarsa ta rasu ba zato ba tsammani, rayuwa ba ta yi masa sauki ba. Bayan ya dan saba da sabon yanayinsa, Geoffrey ya zabi wasu abubuwa kuma ya ce zai yi su don ya ci gaba da yin hidimarsa da kwazo. Ya rubuta abubuwan da yake so ya yi kuma ya sa su cikin adduꞌa. Geoffrey ya ce yana so ya soma nazari da mutane uku kafin watan ya kare. A kowace rana, yakan tuna wa kansa abin da yake da burin yi. Bayan kwana goma kuma, sai ya duba ya ga inda ya kai. Geoffrey ya yi nasara kuwa? Kwarai kuwa. Geoffrey ya yi farin ciki sosai domin ya sami dalibai hudu ba ma uku ba.

Ka Zabi Kananan Abubuwan da Za Ka Yi don Ka Iya Cim ma Burinka

Za mu iya zama da burin yin wani abu, amma sai mu ga kamar ba za mu iya yinsa ba. Tony da aka ambata a baya ya so ya yi hidima a wani ofishin Shaidun Jehobah, amma da farko ya ga kamar ba zai iya yin hakan ba. Me ya sa? Domin irin rayuwar da yake yi a lokacin. Bai ma tsai da shawarar bauta wa Allah ba ko. Amma a kwana a tashi Tony ya canja halinsa don ya cancanci yin baftisma. Da ya yi baftisma, sai ya soma hidimar majagaba na dan lokaci. Daga baya, sai ya shiga hidimar majagaba na kullum. Me ya taimaka masa ya yi abubuwan nan? Ya rubuta abubuwan nan da kuma kwanan watan da zai soma yinsu a kalandarsa. Da Tony ya shiga yin hidimar majagaba, sai ya ga cewa da gaske zai iya cim ma babban burinsa na yin hidima a ofishin Shaidun Jehobah.

Mu ma za mu iya cim ma babban burinmu idan muka soma da yin kananan abubuwa da za su taimaka mana. Idan muka yi niyya kuma muka yi kananan abubuwan nan, hakan zai ba mu kwarin gwiwar cim ma babban burinmu. Yayin da muke yin hakan, zai dace mu rika dakatawa muna duba ci gabar da muka samu, hakan ma zai sa mu kara kwazo. Idan mun ci gaba da rokon Allah ya taimaka mana mu yi abubuwan nan da muka yi niyyar yi, ba shakka zai taimaka mana. Manzo Bulus ya shawarce mu da cewa: “Ku yi ta yin adduꞌa babu fasawa.”​—1 Tasalonikawa 5:17.

Ka Dāge Har Sai Ka Cika Burinka

Idan muna da niyya kuma muka yi shiri da kyau, hakan zai taimaka mana. Amma a wasu lokuta, kila mu ga cewa ba za mu iya cim ma babban burinmu ba. Abin da ya faru da wani mabiyin Yesu mai suna Markus ke nan. Ya so ya bi manzo Bulus a karo na biyu da ya je waꞌazi a kasar waje. Amma Bulus ya ki. Ba shakka Markus bai ji dadi ba. (Ayyukan Manzanni 15:​37-40) Da yake Markus ya kasa cika burinsa, ya bukaci ya canja wannan burin, kuma ya yi hakan. Da alama cewa Markus ya dauki darasi daga abin da ya faru, don daga baya manzo Bulus ya fadi abubuwa masu kyau game da shi. Har ya sami damar yin hidima da manzo Bitrus a Babila. (2 Timoti 4:11; 1 Bitrus 5:13) Wata babbar albarka da Jehobah ya yi wa Markus ita ce ya yi amfani da shi ya rubuta labarin Yesu.

Za mu iya fuskantar matsaloli saꞌad da muke kokarin cika burinmu. Idan hakan ya faru, kada mu yi sanyin gwiwa, mu dāge sai mun cika burinmu. Mu bincika kokarin da muke yi kuma mu ga ko akwai wasu abubuwa da ya kamata mu gyara. Sarki Sulemanu mai hikima ya ce: “Danka wa Yahweh ayyukanka, shirye-shiryenka kuwa za su kai ga nasara.”​—Karin Magana 16:3.

Duk da haka, a wasu lokuta zai yi wuya mu cika burinmu. Alal misali, rashin lafiya da hakkin kula da iyali za su iya sa mu kasa cika burinmu. Kada mu manta cewa babban burinmu shi ne mu sami rai na har abada. (Luka 23:43; Filibiyawa 3:​13, 14) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana yadda za mu cika wannan burin. Manzo Yohanna ya ce: “Wanda ya aikata nufin Allah zai rayu har abada.” (1 Yohanna 2:17) Ko da yanayinmu ya sa mun kasa cika wani buri da muke da shi, duk da haka za mu iya ‘jin tsoron Allah, kuma mu kiyaye umarnansa.’ (Mai-Wa’azi 12:13) Amfanin zama da burin yin wasu abubuwa a ibadarmu shi ne, zai taimaka mana mu mai da hankali ga yin nufin Allah. Don haka, bari mu zama da burin yin abubuwa da za su sa mu daukaka Jehobah Mahaliccinmu.

[Akwati]

Wasu Abubuwa da Za Mu Iya Yi

○ Karanta Littafi Mai Tsarki Kowace Rana

○ Karanta kowane fitowar mujallar Hasumiyar Tsaro da Awake!

○ Inganta adduꞌoꞌinmu

○ Nuna halayen da ruhun Allah yake haifarwa

○ Yin kokari don mu cancanci yin karin ayyuka a hidimar Jehobah

○ Mu inganta yadda muke waꞌazi da koyarwa

○ Koyi wasu abubuwa kamar yin waꞌazi ta waya, da yin waꞌazi a lokacin da muke harkokinmu na yau da kullum, da kuma yin waꞌazi a inda ake kasuwanci