Koma ka ga abin da ke ciki

Ra’ayin da Ya Dace Game da Giya

Ra’ayin da Ya Dace Game da Giya

Ra’ayin da Ya Dace Game da Giya

WANI mai suna Tony ya fuskanci matsaloli sosai a rayuwarsa don yana da jarabar shan giya. Yakan sha giya mai yawan gaske, kuma ya tashi ya yi tafiyarsa. Ya dauka cewa giyar da yake sha, ba ta shafansa. Me ya sa yake irin wannan tunanin?

Matsalar ita ce yawan giya da yake sha tana shafan tunaninsa. Muddin mutum ya sha giya da yawa, ko ya ki ko ya so, kwakwalwarsa ba za ta yi aiki daidai ba. Abin da Tony bai sani ba ke nan. Yawan giya da yake sha yana rufe tunaninsa, shi ya sa ya kasa ganin yadda giyar take shafansa.

Wani abu kuma da ya sa Tony ba ya ganin laifin abin da yake yi shi ne, domin ba ya so ya daina sha. Abin da ya faru da wani mutum mai suna Allen ke nan. Shi ma ya ki yarda cewa yawan giyar da yake sha yana cutar da shi. Ya ce: “Na yi ta boye-boye don kar mutane su san yawan giya da nake sha. In ma sun gane, sai in soma ba da hujjoji kuma in nuna cewa hakan ba kome ba ne. Ban so wani abu ya raba ni da shan giya ba.” Duk da cewa mutane suna ganin yadda shan giya da yawa yake bata rayuwar Tony da Allen, su biyun sun ci-gaba da yin musu. Abin da Tony da Allen suke bukatar yi shi ne, su dāge kuma su canja wannan halin nasu. Me zai taimaka musu su yi hakan?

Ka Dau Mataki!

Akwai mutane da yawa da suka saba shan giya da yawa amma sun daina. Abin da ya taimaka musu su yi hakan shi ne, sun bi abin da Yesu ya fada cewa: “Idan idonka na dama yana sa ka ka yi zunubi, ka cire shi ka yar. Gara ka rasa wata gaba na jikinka da a jefa dukan jikinka a cikin Ge·hen′na.”​—Matiyu 5:​29, New World Translation.

Ba wai Yesu yana nufin mu ji wa kanmu ciwo a zahiri ba ne. Abin da yake nufi shi ne, mu yi duk wani abin da muke bukatar yi don mu daina duk wani halin da zai sa Allah ya yi fushi da mu. Bai da sauki mutum ya rage yawan giya da yake sha, amma idan ya yi hakan, zai ceto kansa daga zama mashayi. Don haka, idan mutane suna gaya maka cewa giyar da kake sha ta yi yawa, ka saurare su kuma ka yi wani abu don ka rage. * Idan har ka ga cewa ba za ka iya daidaita yawan giya da kake sha ba, zai fi maka alheri ka daina sha kwata-kwata. Ba shi da sauki kam, amma abu ne da zai ceto ranka.

Ko da shan giya bai riga ya zama maka jaraba ba, giyar da kake sha ta soma yin yawa? Idan abin da ke faruwa ke nan, me za ka yi don ka rage yawan giya da kake sha?

Abubuwa da Za Su Taimaka Maka

1. Ka dinga yin addu’a da tabbacin cewa Allah zai taimake ka. Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce masu so su yi wa Allah biyayya su yi ke nan. Ya ce: “A cikin kome ku fada wa Allah bukatunku ta wurin addu’a da roko, tare da godiya. Ta haka kuwa Allah zai ba ku salama iri wadda ta wuce dukan ganewar dan Adam, za ta kuma tsare zukatanku da tunaninku cikin Almasihu Yesu.” (Filibiyawa 4:​6, 7) Me za ka roka don ka sami irin wannan salama ko kwanciyar hankali?

A addu’ar, ka fara da bayyana wa Allah cewa ka san yawan giya da kake sha bai dace ba, kuma ka san kai ne kake da hakkin gyara halinka. Ka gaya wa Allah abin da kake shirin yi don ka magance wannan matsalar, shi kuwa zai taimaka maka ka yi hakan. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk wanda ya rufe zunubansa, ba zai ci gaba ba, amma wanda ya furta ya kuma ki su, zai sami jinkai.” (Karin Magana 28:13) Yesu ma ya ce mu roki Allah cewa: “Kada ka kai mu cikin jaraba, amma ka cece mu daga mugun.” (Matiyu 6:​13, Littafi Mai Tsarki) Me za ka yi bayan ka yi addu’a?

2. Ka dinga karanta Kalmar Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kalmar Allah tana da rai, tana da karfin aiki kuma. . . . Har ma tana gane duk tunani da nufin da suke cikin zuciya.” (Ibraniyawa 4:12) Wani abin da ya taimaka wa mutane da yawa su daina shan giya fiye da kima shi ne sun dinga karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, suna yin tunani a kan abin da suke karantawa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai albarka ne mutumin da ba ya bin shawarar masu mugunta ko ya bi hanyar masu zunubi, ko ya hada kai da masu ba’a. Amma yana jin dadi ya kiyaye Koyarwar Yahweh, yana tunanin Koyarwar dare da rana, . . . a kome kuwa nasara yakan yi.”​—Zabura 1:​1-3.

Allen wanda binciken Littafi Mai Tsarki da yake yi da Shaidun Jehobah ne ya taimaka masa ya daina shan giya, ya ce, “A gaskiya, in ba don taimakon da na samu daga Littafi Mai Tsarki da yadda na bi abin da ya ce ba, da na riga na zama labari.”

3. Ka koyi yadda za ka dinga kame kanka. Littafi Mai Tsarki ya ba mu labarin wasu mutane da a dā su mashaya ne sosai, amma ‘ruhun Allah’ ya taimaka musu su daina. (1 Korintiyawa 6:​9-11) Ta yaya ruhun Allah ya taimaka musu su daina shaye-shaye da buguwa? Ya yi hakan ne ta wurin taimaka musu su iya kame kansu don kar su sha giya har ya yi yawa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada kuma ku bugu da ruwan inabi, wanda zai kai ku ga neman jin dadi na rashin kunya. A maimakon haka ku cika da ruhu.” (Afisawa 5:18; Galatiyawa 5:​21-23) Yesu ya mana alkawari cewa: “Ubanku na sama, zai ba da ruhu mai tsarki ga masu rokonsa.” Don haka, ya ce: “Ku yi ta roko za a ba ku. Ku yi ta nema za ku samu.”​—Luka 11:​9, 13.

Wadanda suke so su faranta wa Allah rai, za su iya kame kansu idan suna karanta Littafi Mai Tsarki kuma suna yin addu’a da zuciya daya. Idan ka soma ji kamar ba za ka iya rage yawan giya da kake sha ba, ka tuna da alkawarin nan da Allah ya yi mana cewa: “Idan mutum . . . ya shuka ta biyan bukatar Ruhu, zai kai shi ga girbin rai na har abada. Saboda haka kada mu gaji da yin abin da yake da kyau. Gama idan ba mu gaji muka bar kokari ba, lokaci zai zo da za mu yi girbi mai albarka.”​—Galatiyawa 6:​8, 9.

4. Ka bi abokan kirki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda ya yi tafiya tare da masu hikima zai kasance da hikima, amma abokin tafiyar wawaye zai lalace.” (Karin Magana 13:20) Ka gaya wa abokanka burinka na daidaita yawan giya da kake sha. Amma ka tuna cewa Littafi Mai Tsarki ya ce idan ka daina “buguwa, da bukukuwan shaye-shaye,” abokanka na dā za su yi ‘mamaki yadda ka daina hadin kai da su cikin yin mugayen abubuwan nan kamar dā, har ma su rena ka.’ (1 Bitrus 4:​3, 4) Ka yi shirin rabuwa da abokan da za su zuga ka ka sha giya da yawa.

5. Ka san yawan giya da za ka rika sha. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku yarda tunani irin na zamanin nan ya bi da hankalinku, amma ku yarda Allah ya canja ku ya sabunta tunaninku da hankalinku. Ta haka za ku iya tabbatar da abin da yake nufin Allah, wato abin da yake mai kyau, abin karba ga Allah, da kuma abin da yake cikakke.” (Romawa 12:2) Don haka, ka tsai da shawara a kan yawan giya da za ka rika sha bisa ga abin da ka koya daga Littafi Mai Tsarki, maimakon ka biye ma abokanka ko tunanin mutanen “zamanin nan.” Idan ka yi hakan, za ka yi rayuwa mai kyau kuma Allah zai yi farin ciki. Amma yaya za ka san yawan giya da ya kamata ka rika sha?

Idan ka sha giya har ta soma shafan tunaninka, to ka san cewa giyar da ka sha ta yi yawa. Don haka, ka tabbata cewa giyar da za ka rika sha daidai-wa-daida ne. Kada ma ya kusan sa ka buguwa. Ka gaya ma kanka gaskiya. Ka san yawan giya da idan ka sha ba zai dame ka ba kuma kar ka sha fiye da hakan.

6. Ka koyi yadda za ka ce a’a idan aka maka tayi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Amma bari zancenku ya zama, I, i; da A’a, a’a: abin da ya wuce waɗannan duka daga wurin Mugun ne.” (Matiyu 5:​37, Tsohuwar Hausa a Saukake) Idan ka riga ka sha giya daidai karfinka kuma wani ya zo zai kara maka, ka ce masa a’a ba tare da ka bata rai ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “A koyaushe, bari maganarku ta kasance da alheri da kuma dadin ji, domin ku san irin amsar da ya yi kyau ku ba kowa.”​—Kolosiyawa 4:6.

7. Ka ce abokanka da danginka su taimake ka. Idan kana da abokan kirki da suke kaunar Jehobah, za su so su taimaka maka ka daina shan giya da yawa. Don haka, ka ce su taimake ka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwamma mutum biyu da mutum daya, gama amfanin aikin mutane biyu ya fi na mutum daya. Gama idan daya ya fādi, daya zai taimaka ya daga dayan.” (Mai-Wa’azi 4:​9, 10; Yakub 5:​14, 16) Wata kungiya a Amirka da ke yin bincike don taimaka ma wadanda suke fama da jarabar shan giya, ta ce: “A wasu lokuta zai iya yi wa mutum wuya ya rage yawan giya da yake sha. Don haka, ka ce abokanka da ’yan gidanku su taimake ka.”

8. Ka dāge har sai ka yi nasara. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku zama masu aikata kalmar Allah, ba masu ji kawai ba, wato kuna rudin kanku. Amma mutumin da ya mai da hankalinsa wajen bincike cikakkiyar koyarwar nan wadda ita ce mai kawo ’yanci, za a sa masa albarka cikin dukan abin da yake yi, idan har bai zama mai ji kawai ya manta ba, amma ya zama mai naciya cikin aikatawa.”​—Yakub 1:​22, 25.

Yadda Mutum Zai Fita Daga Jarabar Shan Giya

Wasu sukan sha giya da yawa. Ko da yake hakan ba kyau, ba ya nufin cewa suna da jarabar shan giya. Wasu kuma yadda suke shan giya da yawa ko yadda suke sha a kai a kai, ya sa ba sa iya rayuwa sai da giya. Idan har shan giya ya zama ma mutum jaraba haka, ba mamaki ya shiga rashin lafiya idan ya daina. Don haka, zai bukaci taimakon likita. Allen da muka ambata dazu ya ce, “A lokacin da nake kokarin daina shan giya, jikina ya min ciwo sosai. A nan ne na gano cewa ina bukatar zuwa asibiti.”

Da yawa daga cikin wadanda suke so su daina shan giya don su faranta wa Allah rai, sukan bukaci taimakon likita. * Zuwa asibiti yakan zama ma wasu dole domin da zarar sun daina sha, sukan soma rashin lafiya. Wasu kuma suna bukatar magungunan da za su taimaka musu su rage kwadayin shan giya kuma su dāge har sai sun daina. Yesu ya ce: “Masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”​—Markus 2:17.

Amfanin da Za Ka Samu Idan Ka Bi Abin Allah Ya Ce

Abin da ya sa Allah ya gaya mana hanyar da ya kamata mu sha giya shi ne, domin yana so mu ji dadin rayuwa yanzu da kuma a aljanna. Bayan Allen ya yi shekaru ashirin da hudu da barin shan giya kuma ya tuna fama da ya yi kafin ya daina, ya gode wa Allah sosai har hawaye suna zuba daga idanunsa. Ya ce: “A dā ban taba tsammanin zan iya canja halina ba, amma sai na gano cewa Jehobah yana so ya taimaka min in gyara halina. Na ga cewa ya fahimci halin da nake ciki, ya damu da ni kuma zai taimaka min. A gaskiya, ina godiya.”

Idan ka lura cewa yadda kake shan giya bai dace ba, wani lokaci za ka ji kamar ba za ka iya dainawa ba. Amma kar hakan ya sa ka daina kokarin da kake yi. Akwai mutane da yawa irin su Allen da su ma suka shiga wannan halin. Amma wasunsu sun rage yawan giya da suke sha, wasu kuma sun daina sha kwata-kwata. Yanzu suna godiya. Kai ma idan ka canja halinka, za ka yi farin ciki.

Idan ka zaba cewa za ka rage yawan giya da kake sha ko za ka daina sha kwata-kwata, ka san cewa Allah yana kaunarka sosai. Ga abin da ya ce: “Ayya! Da a ce kun yi biyayya da umarnaina, da salamarku za ta kasance kamar ruwan rafi, nasarar adalcinku kuma za ta yi ta bullowa kamar rakuman ruwan teku.”​—Ishaya 48:18.

[Karin bayannai]

^ Ka karanta abin da ke akwatin nan  “Giyar da Nake Sha Ta Soma Yin Yawa Ne?” da ke shafi na 8.

^ Akwai wuraren jinya da asibitoci da dai sauransu, da za su iya taimaka ma wadanda suke da jarabar shan giya. Shaidun Jehobah ba sa gaya wa mutane irin jinyar da za su yi. Kowa zai duba ya ga irin jinyar da za a iya masa, sa’an nan ya zabi wadda yake so, muddin bai saba wa ka’idodin Littafi Mai Tsarki ba.

[Akwati/​Hoto]

 Giyar da Nake Sha Ta Soma Yin Yawa Ne?

Ka tambayi kanka:

• Giya da nake sha yanzu, ta fi wadda nake sha a dā?

• Ina sha sau da yawa fiye da dā?

• Giya da nake sha yanzu ta fi na dā karfi?

• Giya ta zama min maganin gajiya, ko ina shan giya don in manta da matsalolina?

• Wani abokina ko wani a gidanmu ya taba ce min giyar da nake sha ta yi yawa?

• Shan giya ya taba sa na shiga matsala a gidana, ko a wurin aikina da dai sauran su?

• Zan iya yin sati daya ban sha giya ba, ko zai min wuya?

• Ba na jin dadi idan ina zama tare da wadanda ba sa shan giya?

• Shin ina boye-boye don kar mutane su san yawan giya da nake sha?

Idan ka ce e ga ko guda daya cikin tambayoyin nan, da alama zai dace ka yi wani abu don ka daidaita yawan giya da kake sha.

[Akwati/​Hoto]

Abin da Zai Taimake Ka Ka Tsai da Shawarar da Ta Dace

Kafin ka sha giya, ka tambayi kanka:

In sha ne ko kar in sha, wanne ne zai fi mini alheri?

Shawara: Idan ba za ka iya shan giya daidai-daidai ba, gwamma kar ka sha kwata-kwata.

Yaya yawan giya da ya kamata in sha?

Shawara: Da yake giya za ta iya hana ka yin tunani da kyau, gwamma ka tsai da shawara a kan yawan giya da za ka sha kafin ma ka soma sha.

Wane lokaci ne ya kamata in sha giya?

Shawara: Bai kamata ka sha giya idan za ka yi tuki ko wasu ayyukan da suke bukatar mutum ya mai da hankali ba. Bai dace ka sha idan za ka yi ayyukan ibada ba. Mace mai ciki bai kamata ta sha ba. Kuma akwai magungunan da idan kana sha, bai kamata ka sha giya ba.

A ina ne ya kamata in sha giya?

Shawara: Kar ka sha a inda mutane suke sha suna buguwa, da kuma inda ake halin banza; kar ka boye kana shan giya; kuma kar ka sha a gaban mutanen da ba sa so.

Da su wa ya kamata in sha giya?

Shawara: Da abokanka da ’yan gidanku da suke da halin kirki; ba da wadanda ba sa kame kansu sa’ad da suke sha ba.

[Akwati/​Hoto]

Littafi Mai Tsarki Ya Taimaka ma Wani Mashayi

Wani mai suna Supot daga kasar Thailand, mashayi ne sosai a dā. A lokacin da ya fara sha, da yamma ne kadai yake sha. A kwana a tashi sai ya soma sha da safe, ana nan kuma sai ya soma sha da rana. Burinsa kawai shi ne ya sha ya bugu. Amma da Shaidun Jehobah suka soma koya masa Littafi Mai Tsarki, sai ya gano cewa buguwa da giya bai dace ba. Don haka sai ya daina sha. Amma daga baya, Supot ya koma gidan jiya. Ya shiga shan giya sosai. Da iyalinsa suka ga haka, ba su ji dadi ba sam.

Duk da halin da Supot yake ciki, can cikin zuciyarsa yana kaunar Jehobah kuma ya so ya bauta masa yadda ya dace. Abokansa su ma ba su gaji da taimaka masa ba. Sun ci-gaba da yin hakan, kuma sun ce wa matarsa da yaransa kar su gaji da taimaka masa. Sun kuma shawarce su cewa kar su dinga barinsa shi kadai. A maimakon haka, su dinga yin abubuwa tare da shi. Yadda 1 Korintiyawa 6:10 ta bayyana dalla-dalla cewa ‘masu buguwa, ba za su shiga mulkin Allah’ ya sa Supot ya ga cewa yanayin da yake ciki ba wasa ba ne. Ya ga cewa dole ya dāge sosai don ya daina shan giya da yawa.

A wannan karon, Supot ya kuddura cewa zai daina shan giya. Da taimakon Allah da Littafi Mai Tsarki da iyalinsa da kuma ’yan’uwa a ikilisiya, Supot ya shawo kan wannan matsalar. Har Supot ya yi alkawarin bauta wa Allah kuma ya yi baftisma. Matarsa da yaransa sun yi farin ciki sosai a ranar da ya yi baftisma. Yanzu Supot ya zama aminin Jehobah, abin da ya dade yana nema. Kuma yana amfani da lokacinsa sosai wajen taimaka wa mutane su ma su kusanci Jehobah.