Koma ka ga abin da ke ciki

Biyan Haraji—Dole ne?

Biyan Haraji—Dole ne?

Biyan Haraji​—Dole ne?

YAWANCIN mutane ba sa son biyan haraji. Da yawa daga cikinsu suna ganin ba a yin amfani da kudaden da suke biya a hanyar da ta dace. Wasu mutane a wani birni da ke Gabas ta Tsakiya sun ce: “Ba za mu ba gwamnati kudi ta sayi harsashi tana kashe yaranmu da shi ba.”

Mutane da yawa ba sa so a yi amfani da haraji da suke biya a hanyar da ba ta dace ba. Wani dan siyasa a kasar Indiya ya ce zuciyarsa ba ta ba shi ya biya haraji ba. Ya ce, “Duk wanda yake tallafa wa Kasa da take da sojoji, shi ma yana da hannu a cikin mugayen abubuwan da suke yi. Kowane matashi ko tsoho da ya biya haraji don a tafiyar da harkokin kasar, yana da hannu a duk barnar da ake yi.”

Haka ma da wani mai ilimin falsafa a Amirka mai suna Henry David Thoreau. Ya ki biyan haraji don ana amfani da kudin wajen tallafa wa yaki. A nasa ra’ayin, bai kamata ’yan siyasa su rika tilasta wa talakawa su goyi bayan abu mara kyau ba. Mutum ne zai zaba ko zai biya haraji ko ba zai biya ba bisa ga abin da zuciyarsa ta ba shi.

Kiristoci suna daukan biyan haraji da muhimmanci. Me ya sa? Littafi Mai Tsarki ya nuna dalla-dalla cewa ya kamata tunaninmu ko zuciyarmu ya tabbatar mana cewa ba mu da laifi a kowane abu. (2 Timoti 1:3) Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa gwamnati tana da iko ta karbi haraji daga talakawanta. Ya ce: “Kowa ya yi biyayya ga shugabannin gwamnati [hukuma], gama babu wani ikon shugabanci sai dai daga wurin Allah. Kuma duk masu ikon shugabanci da muke da su, Allah ne ya kafa su. Saboda haka dole ne ku yi biyayya ga shugabannin gwamnati. Ba don ku guje wa fushin Allah kadai ba, amma don tunaninku ya kasance babu laifi. Wannan ne kuma ya sa kuke biyan haraji, don shugabannin gwamnati ma’aikatan Allah ne wadanda suke ba da duk lokacinsu saboda aikin shugabanci. Ku biya wa kowa duk abin da yake binku. Idan harajin kanku ne ya kamata ku biya, sai ku biya, idan ma harajin kayanku ne, sai ku biya.”​—Romawa 13:​1, 5-7.

Abin da nassin nan ya fada ne ya sa Kiristoci a karni na farko suka biya haraji, ko da yake ana cire kudi da yawa a ciki don a tallafa wa aikin soja. Shaidun Jehobah ma an san su da biyan haraji. * Me ya sa muke biyan haraji duk da cewa ana amfani da wasu kudaden wajen tallafa wa ayyuka da ba ma goyon bayansu? Shin ya kamata Kirista ya biya haraji ko da yana ganin hakan bai dace ba?

Ka Biya Haraji don Kada Ka Zama da Laifi

A zamanin Kiristoci na farko, ana cire kudi da yawa a harajin da suke biya don a tallafa wa aikin soja. Wannan dalilin ne ya sa mutumin Indiya da na Amirka da muka ambata a baya suka ki biyan haraji.

Ka lura cewa Kiristocin nan da suka bi dokar da ke Romawa sura 13, ba wai sun yi hakan don su guje wa horo ba ne, amma don ‘tunaninsu ko zuciyarsu ta kasance babu laifi.’ (Romawa 13:5) Saboda haka, ko da Kirista ba ya son yadda ake amfani da haraji, yana bukata ya biya in har yana so zuciyarsa ta kasance babu laifi. Don mu fahimci wannan batun da kyau, muna bukatar mu san yadda zuciyarmu take aiki. Zuciyarmu tana kama da wata murya da take gaya mana ko abin da muke yi ya dace, ko bai dace ba.

Thoreau da muka ambata a baya ya ce kowa yana da irin muryar nan, amma ba a kullum muryar take fadan gaskiya ba. Idan muna so mu faranta wa Allah rai, dole ne mu horar da tunaninmu ko zuciyarmu don ta yi daidai da ra’ayin Allah. Da yake Allah ya fi mu hikima, dole mu rika daidaita tunaninmu don ya zo daidai da ra’ayinsa. (Zabura 19:7) Ya kamata mu yi kokari mu fahimci ra’ayin Allah game da gwamnatoci ko hukumomi. Mene ne ra’ayinsa game da su?

Ka tuna cewa manzo Bulus ya ce shugabannin gwamnati “ma’aikatan Allah ne.” (Romawa 13:6) Me hakan yake nufi? Hakan yana nufin cewa suna sa a bi doka kuma suna yin wasu abubuwa masu kyau ga talakawansu. Sukan tanadar da makarantu da masu kashe gobara da ’yan sanda da kuma hanyar da za a rika tura wasiku. Ko da yake Allah ya san abubuwa marasa kyau da hukuma suke yi, ya bar su su yi sarauta. Yana so mu daraja su kuma mu rika biyan haraji.

Allah ya dai bar ’yan Adam su yi sarauta na dan lokaci ne. A nan gaba, zai kawo mulkinsa wanda zai maye gurbinsu, kuma ya gyara abubuwan da suka lalatar. (Daniyel 2:44; Matiyu 6:10) Kafin wannan lokacin ya zo, Allah yana son mu yi musu biyayya kuma mu rika biyan haraji.

Idan kana ganin biyan haraji, goyon bayan zunubi ne kamar yadda mutumin nan daga Indiya ya fada, me za ka yi? Ya kamata mu tuna cewa Allah ya fi mu hikima da ilimi, don haka zai dace mu daidaita ra’ayinmu. Ta bakin annabi Ishaya, Allah ya ce: “Kamar yadda sammai suke nesa da kasa, haka nan al’amurana suke nesa da naku, tunanina kuma suke nesa da naku.”​—Ishaya 55:​8, 9.

Wa Ya Fi Kowa Iko?

Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya ce mu rika biyan haraji, hakan baya nufin cewa a kullum za mu rika yi wa gwamnati biyayya. Yesu ya gaya mana cewa ikon da Allah ya ba gwamnati yana da iyaka. A lokacin da wani mutum ya tambayi Yesu ko ya dace ya biya haraji ga Kaisar, wato gwamnatin Roma, Yesu ya ce: “Ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar. Ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”​—Markus 12:​13-17.

Gwamnatoci a yau su ne suke kamar “Kaisar.” Suna buga kudi, don haka bisa ga ra’ayin Allah, ba laifi ba ne su karbi haraji daga wurinmu. Duk da haka, Yesu ya nuna mana cewa ranmu da ibadarmu na Allah ne kadai. Don haka, idan gwamnati ta ce mu yi wani abu da ya taka Dokar Allah, “dole ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mu yi wa mutum.”​—Ayyukan Manzanni 5:29.

Kiristoci na gaskiya ba sa son yadda ake amfani da wasu kudaden haraji da ake karba. Duk da haka, ba sa adawa da gwamnati kuma ba sa kin biyan haraji. Ta haka suna nuna sun dogara ga Allah cewa shi ne zai magance matsalolinmu. Suna hakuri, suna jiran lokacin da Allah zai taimaka musu ta wurin mulkinsa. Yesu ya ce: “Mulkina ba iri na duniya ba ne.”​—Yohanna 18:36.

Amfanin Bin Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce

Idan kana biyan haraji, za ka kāre kanka daga matsaloli da yawa. Ba za ka ji tsoro cewa za a kama ka ba, kuma ba za ka fuskanci hukuncin da ake ma wadanda suka ki biyan haraji ba. (Romawa 13:​3-5) Mafi muhimmanci ma, zuciyarka ba za ta dame ka ba domin kana yin abin da Allah yake so kuma kana daraja shi ta wajen bin doka. Ko da yake biyan haraji zai sa ka rasa wasu kudadenka, ka tuna cewa Allah ya yi alkawari zai kula da bayinsa. Dauda marubucin zabura ya ce: “Dā dai ni yaro ne, yanzu kam na tsufa, amma ban taba ganin Yahweh ya yashe mai adalci ba, ko kuwa a ga ’ya’yansa suna rokon abinci.”​—Zabura 37:25.

A karshe, idan ka fahimci dokar Allah game da biyan haraji kuma ka bi ta, za ka sami kwanciyar hankali. Kamar yadda idan ka biya kudin haya ba za a kama ka da laifi don abin da maigidan ya yi da kudin hayar ba, haka ma Allah ba zai kama ka da laifi don yadda gwamnati ta yi amfani da kudin harajin da ka biya ba. Akwai wani mutum mai suna Stelvio da ke zama a kudancin Turai. Kafin ya san Littafi Mai Tsarki, ya yi kokari ya yaki rashin adalci a kasarsu. Amma daga baya ya daina. Ya ce: “A gaskiya, dan Adam ba zai iya sa a yi adalci, a kasance da salama da kuma hadin kai a duniya ba. Mulkin Allah ne kadai zai iya gyara duniyar nan.”

Idan kai ma ka ba Allah abin da ke nasa kamar yadda Stelvio ya yi, za ka tabbata cewa Allah zai sa a yi gaskiya. Za ka ga lokacin da sarautar Allah za ta sa a yi gaskiya a dukan duniya kuma za ta gyara dukan abubuwan da mulkin ’yan Adam ya lalatar.

[Karin bayani]

^ Don karin bayani a kan yadda aka san shaidun Jehobah da biyan haraji, ka karanta Hasumiyar Tsaro na 1 ga Nuwamba, 2002, shafi na 23, sakin layi na 15, da Na 1 ga Mayu, 1996, shafi na 25, sakin layi na 7.

[Bayani]

Da yake Allah ya fi mu hikima, dole mu rika daidaita tunaninmu don ya zo daidai da ra’ayinsa.

[Bayani]

Idan muna biyan haraji, zuciyarmu ba za dame mu ba. Kuma hakan zai nuna cewa mun dogara ga Allah don ya biya mana bukatunmu

[Hotuna]

Ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar. Ku kuma ba Allah abin da yake na Allah”

[Inda aka dauko hoto]

Copyright British Museum