Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kyauta da Ta Sa Mutanen Japan Farin Ciki

Kyauta da Ta Sa Mutanen Japan Farin Ciki

A WANI taro na musamman da aka yi a Nagoya a ƙasar Japan a rana ta 28 ga Afrilu, 2013, Anthony Morris, wani memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya yi wata sanarwa da ya sa masu sauraro farin ciki sosai. Ya fitar da wani sabon littafi a yaren Japan mai suna, The Bible—The Gospel According to Matthew (Bishara ta Hannun Matta). Mutane fiye da 210,000 da suka hallara ko kuma suka saurari jawabin ta Intane sun yi tafi sosai saboda murna.

An buga wannan Bishara ta Hannun Matta mai shafuffuka 128 daga fassarar Littafi Mai Tsarki na New World Translation, kuma yana da fasaloli na musamman. Ɗan’uwa Morris ya bayyana cewa an wallafa shi “don taimaka wa mutanen Japan.” Waɗanne abubuwa ne ke cikin wannan littafin? Me ya sa aka wallafa shi? Mene ne mutane suka faɗa game da littafin?

WAƊANNE ABUBUWA NE KE CIKIN LITTAFIN?

Yadda aka tsara littafin ya burge masu sauraro sosai. Ana rubuta harufan yaren Japan a tsaye ko kuma a kwance, kuma an buga littattafai kaɗan da kuma wasu sababbin littattafanmu da harufa na kwance. An bi tsarin rubutun tsaye da ake bi a yawancin jaridu da rubuce-rubucen adabi na ƙasar Japan a wannan sabon littafin. Ga mutanen ƙasar Japan, wannan tsarin yana da sauƙin karantawa. Ƙari ga haka, maimakon kan magana ya kasance a saman kowane shafi, an mai da su ƙananan jigogi a cikin littafin don masu karatu su gane muhimman darussan.

’Yan’uwa maza da mata a Japan sun soma amfani da littafin nan da nan. Wata ’yar’uwa mai shekara tamanin da wani abu ta ce: “Na sha karanta littafin Matta amma wannan tsarin da aka bi da kuma ƙananan jigogin sun sa na ƙara fahimtar Huɗuba bisa Dutse.” Wata matashiya ta ce: “Da na buɗe littafin ban ajiye ba sai da na karance. Na saba da rubutun kwance, amma yawancin mutanen Japan sun fi son rubutun tsaye.”

AN TSARA DON WA’AZI A ƘASAR JAPAN

Ta yaya wannan littafin Matta zai taimaka wa mutanen ƙasar Japan? Ko da yake yawancin mutanen Japan ba su saba da Littafi Mai Tsarki ba, amma suna son karantawa. Wannan littafin zai ba mutanen da ba su taɓa ganin Littafi Mai Tsarki ba damar kasancewa da shi da kuma karanta shi.

Me ya sa aka zaɓi littafin Matta? Ga yawancin mutanen Japan, idan aka ambaci Littafi Mai Tsarki, Yesu Kristi ne yake zuwa zuciyarsu. Shi ya sa aka zaɓi littafin Matta don yana ɗauke da labari game da zuriyar Yesu da haihuwarsa da sanannen Huɗuba Bisa Dutse da kuma annabci game da kwanaki na ƙarshe. Hakika, mutanen Japan da yawa za su ji daɗin karanta waɗannan batutuwan.

Masu shela suka soma rarraba sabon littafin nan da ƙwazo sa’ad da suke yin wa’azi gida-gida da kuma lokacin da suka koma ziyara. Wata ’yar’uwa ta ce: “Yanzu zan iya rarraba wa mutane Kalmar Allah a yankinmu. A yanzu haka ma, na ba wani littafin a ranar da aka yi wannan taro na musamman!”

MENE NE MUTANE SUKA CE GAME DA LITTAFIN?

Ta yaya ’yan’uwa suke gabatar da wannan littafin Matta? Yawancin mutanen Japan suna sane da furuci kamar su “matsatsiyar ƙofa” da ‘lu’ulu’ai a gaban gursunai’ da kuma “kada fa ku yi alhini a kan gobe.” (Mat. 6:34; 7:6, 13) Sun yi mamakin sanin cewa Yesu Kristi ne ya furta waɗannan kalmomin. Yawanci da suka karanta waɗannan kalaman sun ce suna so su karanta Littafi Mai Tsarki ko sau ɗaya.

Mutanen da aka ba su littafin sukan gaya wa ’yan’uwa da suka koma don su ziyarce su cewa sun karanta littafin gaba daya ko kuma wani sashe a ciki. Wani mutum da yake da shekara sittin da wani abu ya gaya wa wani mai shela cewa: “Na karanta shi sau da yawa kuma hakan ya kwantar mini da hankali. Don Allah ku koya min Littafi Mai Tsarki da kyau.”

An saka wannan littafin Matta a cikin littattafan da za a riƙa bayarwa a wa’azi a inda akwai jama’a. Sa’ad da wata Mashaidiya take yin wa’azi, wata mata ta karɓi Littafin kuma ta ba ’yar’uwarmu adireshin Imel ɗinta. Bayan awa ɗaya, sai matar da aika mata saƙo ta ce ta karanta wani sashen littafin kuma tana neman ƙarin bayani. Bayan mako ɗaya aka soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ita kuma daga baya ta soma halartan taro.

An tura wa ikilisiyoyi da ke ƙasar Japan fassarar wannan littafin fiye da miliyan ɗaya da dubu ɗari shida, kuma kowane wata, ’yan’uwa suna rarraba dubban wannan littafin. A gabatarwar wannan littafin, mawallafan sun ce: “Muna fata cewa karanta wannan littafin zai sa ku daɗa son Littafi Mai Tsarki.”