Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

A dā, ana bayyana a littattafanmu cewa wasu labaran Littafi Mai Tsarki suna wakiltar muhimman mutane ko abubuwa, amma a kwanan nan ba a yawan yin hakan. Me ya sa?

An bayyana a cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 1950 cewa a wani lokaci mutane ko yanayi ko abubuwa da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki suna wakiltar wani abu da zai faru a nan gaba. A dā, littattafanmu sun ce bayin Allah kamar su Deborah da Elihu da Jephthah da Ayuba da Rahab da kuma Rifkatu da sauransu suna wakiltar shafaffu ko kuma “taro ma-girma.” (R. Yoh. 7:9) Alal misali, an ɗauka cewa Jephthah da Ayuba da kuma Rifkatu suna wakiltar shafaffu, yayin da Deborah da Rahab suna wakiltar taro mai-girma. Amma, a shekarun baya bayan nan ba ma yin irin wannan kwatancin kuma. Me ya sa?

Wasu ayoyi sun nuna cewa wasu mutane da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki suna wakiltar wasu muhimman abubuwa. Kamar yadda aka rubuta a cikin Galatiyawa 4:21-31, manzo Bulus ya ambaci wani “misali” da ya shafi mata biyu. Hajaratu, baiwa da aka ba Ibrahim tana wakiltar Isra’ila ta dā wadda ta ɗauki alkawarin yin biyayya ga Jehobah ta wajen bin Dokar da aka ba da ta hannun Musa. Amma, Saratu tana wakiltar sashen ƙungiyar Allah da ke sama. A wasiƙar da ya rubuta zuwa ga Ibraniyawa, Bulus ya kwatanta Malkisadik, wani sarki da kuma firist da ke hidima a matsayin Yesu, kuma ya kwatanta takamaiman kamanni da ke tsakanin su biyu. (Ibran. 6:20; 7:1-3) Ƙari ga haka, Bulus ya nuna cewa Ishaya da ’ya’yansa maza suna wakiltar Yesu da kuma mabiyansa shafaffu. (Ibran. 2:13, 14) Allah ne ya hure Bulus ya rubuta wannan bayani, saboda haka, mun amince da abin da ya faɗa game da waɗannan mutane.

ALAMA

Ɗan rago da aka yi hadayarsa a lokacin bikin idin ƙetarewa a Isra’ila ta dā alama ce—Lit. Lis. 9:2

ABIN DA YAKE WAKILTA

Bulus ya yi nuni ga Kristi a matsayin “ɗan Ragonmu na Idin Ƙetarewa.” —1 Kor. 5:7, Littafi Mai Tsarki

Amma, bai kamata mu kammala cewa kowane bayani game da mutum da kuma dukan abubuwa da suka faru a rayuwarsa suna wakiltar wasu muhimman abubuwa ba, ko da Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa wannan mutum yana wakiltar wani abu. Alal misali, ko da Bulus ya gaya mana cewa Malkisadik yana wakiltar Yesu, bai faɗi kome game da lokacin da Malkisadik ya ba Ibrahim gurasa da kuma ruwan inabi ya ci ya sha bayan ya ci sarakuna huɗu a yaƙi ba. Saboda haka, babu wata aya a Littafi Mai Tsarki da ta nuna cewa abin da ya faru yana da wata ma’ana dabam.—Far. 14:1, 18.

Ƙarnuka bayan mutuwar Kristi, wasu marubuta sun kasance da irin wannan ra’ayin, suna ganin cewa kome a cikin Littafi Mai Tsarki yana wakiltar wani abu. Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da koyarwar Origen da Ambrose da Jerome, kuma ya bayyana cewa: “Suna neman wata ma’ana a kan kome da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki, komen ƙanƙantarsa kuma suna samun ma’anarsu. Sun yi da’awa cewa kome yana ɗauke da wata ma’ana da masana ne kawai za su iya fahimta, har ma da abin da bai taka ƙara ya karya ba. Alal misali, wasu sun ce adadin kifi da almajiran Yesu suka kama a daren da ya bayyana a gare su guda 153 ne!”

Augustine na Hippo ya yi dogon bayani game da lokacin da Yesu ya ciyar mutane 5,000 da gurasan sha’ir biyar da kuma kifi biyu. Tun da ana ɗaukan cewa alkama ta fi sha’ir daraja, Augustine ya kammala cewa gurasa guda biyar tana wakiltar littattafai biyar da Musa ya rubuta amma kuma (sha’ir tana wakiltar “Tsohon Alkawari”). Kifi biyun kuma fa? Ya kamanta su da wani sarki da kuma firist. Wani masani da ke yawan ba wa labaran Littafi Mai Tsarki ƙarin ma’ana ya ce, sayan matsayin Isuwa na ɗan fari da Yakubu ya yi da jan miya yana wakiltar yadda Yesu ya fanshi ’yan Adam da jininsa don su sami gatan zuwa sama ne.

Hakika, idan amincewa da irin waɗannan bayanan za su yi wa mutane da yawa wuya, to akwai matsala. ’Yan Adam ba za su iya sanin labaran Littafi Mai Tsarki da suke wakilta abubuwa da za faru a nan gaba ba, da kuma waɗanda ba za su faru ba. Abin da ya dace da za a yi shi ne, idan Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa wani mutum ko yanayi ko abu yana wakiltar wani abu dabam, mu amince da hakan. Bai kamata mu faɗa cewa wani mutum ko yanayi ko abubuwa yana wakiltar wani abu dabam idan Littafi Mai Tsarki bai faɗi hakan ba.

To, ta yaya za mu amfana daga labarai da kuma misalai da ke Littafi Mai Tsarki? A Romawa 15:4, manzo Bulus ya ce: Dukan ‘abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu, domin ta wurin haƙuri da ta’aziyar littattafai mu zama da bege.’ Bulus yana nufin cewa ’yan’uwansa shafaffu a ƙarni na farko suna iya koyan darussa masu kyau daga abubuwan da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki. Amma, masu bauta wa Allah a kowane zamani za su iya amfana daga dukan “abin da aka rubuta a dā” ko suna cikin shafaffu ko kuma “taro mai-girma,” har da waɗanda suke zama a “kwanaki na ƙarshe.”—Yoh. 10:16; 2 Tim. 3:1.

Saboda haka, ba shafaffu ko taro mai girma ko wani rukunin Kiristoci da suka yi rayuwa a wani zamani ba ne kawai yawancin labaran Littafi Mai Tsarki ya shafa. Amma dukan bayin Allah za su iya amfana daga darussa masu yawa da labaran Littafi Mai Tsarki suka koya mana. Alal misali, bai kamata mu kammala cewa wahalar da Ayuba ya sha tana nuni ga tsanantawa da shafaffu suka fuskanta a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya kawai ba. Bayin Allah da yawa, maza da mata da shafaffu da waɗanda suke cikin taro mai girma sun fuskanci irin yanayin da Ayuba ya fuskanta kuma sun shaida albarkar Jehobah, da yake shi mai “tausayi, mai-jinƙai ne kuma.”—Yaƙ. 5:11.

Alal misali, a cikin ikilisiyoyinmu a yau, muna da tsofaffin mata masu aminci kamar Deborah, da dattawa masu farin jini kamar Elihu, da majagaba masu himma kamar Jephthah da maza da mata masu bangaskiya da kuma jimiri kamar Ayuba. Muna godiya cewa Jehobah ya sa aka adana labaran “abin da aka rubuta a dā” don mu sami ƙarfafa daga “littattafai mu zama da bege.”

Don waɗannan dalilan ne a shekarun baya bayan nan ake nanata darussa da za mu iya koya daga labaran Littafi Mai Tsarki a littattafanmu maimakon a riƙa neman ƙarin ma’ana ga wani batu da kuma abin da yake wakilta.