Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Koyi Darasi Daga Kwatancin Talanti

Ka Koyi Darasi Daga Kwatancin Talanti

Ga wani ya ba da talent biyar, ga wani kuma biyu, ga wani ɗaya.MAT. 25:15.

1, 2. Me ya sa Yesu ya yi kwatancin talanti?

 A KWATANCIN talanti, Yesu ya bayyana wani abin da ya kamata mabiyansa shafaffu su yi. Muna bukatar mu fahimci ma’anar wannan kwatanci, don ya shafi dukan Kiristoci na gaskiya, waɗanda suke da begen zuwa sama da kuma waɗanda za su zauna a cikin aljanna a duniya.

2 Yesu ya ba da kwatancin talanti a lokacin da yake amsa tambayar da almajiransa suka yi game da ‘alamar zuwansa da cikar zamani.’ (Mat. 24:3) Saboda haka, kwatancin yana cika a zamaninmu kuma ya nuna cewa Yesu yana sarauta kuma muna cikin kwanaki na ƙarshe.

3. Waɗanne darussa ne muka koya daga kwatance-kwatance da ke cikin Matta surori 24 da kuma 25?

3 Kwatancin talanti yana ɗaya daga cikin kwatance-kwatance huɗu masu alaƙa da juna da aka ambata a Matta 24:45 zuwa 25:46. Kwatance-kwatance uku da suka rage, wato na bawan nan mai aminci mai hikima da kwatancin budurwai goma da kuma na tumaki da awaki, suna cikin amsar da Yesu ya ba da game da alamar zuwansa. A duka kwatance-kwatance huɗun, Yesu ya nuna halayen da za a san mabiyansa na gaskiya da su a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Ya ba da kwatance-kwatance na bawan nan mai aminci da na budurwai da kuma na talanti ga mabiyansa shafaffu. A kwatanci na bawan nan mai aminci, Yesu ya nuna cewa ƙaramin rukunin shafaffu da aka ba aikin ciyar da iyalin gidansa a kwanaki na ƙarshe za su kasance da aminci da kuma hikima. A kwatanci na budurwai, Yesu ya nuna cewa ya kamata dukan mabiyansa shafaffu su kasance a shirye kuma su yi tsaro, tun da yake ba su san ranar ko kuma sa’ar da zai zo ba. A cikin kwatancin talanti, Yesu ya nuna cewa ya kamata shafaffu su kasance da ƙwazo a cika umurnin da ya ba su. Yesu ya ba da kwatanci na ƙarshe, wato kwatancin tumaki da awaki ga waɗanda suke da begen zama a duniya. Ya nanata cewa ya kamata su kasance da aminci kuma su tallafa wa ’yan’uwan Yesu shafaffu da ke duniya. a Bari mu tattauna kwatancin talanti.

MAIGIDAN YA BA WA BAYINSA DUKIYA

4, 5. Wane ne mutumin ko kuma maigidan yake wakilta, kuma nawa ne talanti guda?

4 Karanta Matta 25:14-30. Tun da daɗewa, littattafanmu sun yi bayani cewa Yesu ne mutumin ko kuma maigidan a kwatancin, kuma tafiya sama da ya yi a shekara ta 33 yana kama da tafiya zuwa wata ƙasa. A wani kwatanci da Yesu ya yi kafin wannan lokacin, ya bayyana nufinsa na yin tafiya zuwa wata ƙasa don “ya samo mulki.” (Luk. 19:12) Yesu bai zama sarki nan da nan ba a lokacin da ya je sama. b Maimakon haka, “ya zauna ga hannun dama na Allah; daga nan gaba yana tsumayi [jira] har an mayar da maƙiyansa matashin sawayensa.”—Ibran. 10:12, 13.

5 A kwatancin, maigidan yana da talanti guda takwas, wannan kuɗi ne mai yawa a lokacin. c Kafin ya yi tafiya zuwa wata ƙasa, ya rarraba wa bayinsa talantin don yana so su yi kasuwanci da kuɗin. Kamar wannan mutumin, Yesu yana da wani abu mai tamanin gaske kafin ya je sama. Me ke nan? Amsar ta shafi aikin da ya yi sa’ad da yake duniya.

6, 7. Mene ne talantin suke wakilta?

6 Yesu ya ɗauki wa’azi da koyarwa da muhimmanci sosai. (Karanta Luka 4:43.) Ta hakan ne mutane da yawa suka zama almajiransa, amma da sauran rina a kaba don ya san cewa ƙarin mutane za su saurari bishara. A wani lokaci ya gaya wa almajiransa: “Ku tā da idanunku, ku duba gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi.” (Yoh. 4:35-38) Yana nufin tattara mutane da yawa masu kirki waɗanda za su zama almajiransa. Kamar manomi mai ƙwazo, Yesu ba zai ƙyale gonar da ta isa girbi ba. Saboda haka, ba da daɗewa ba bayan ya tashi daga mutuwa kafin ya je sama, ya ba almajiransa umurni mai muhimmanci cewa: “Ku tafi fa, ku almajirtar” da mutane. (Mat. 28:18-20) Yesu ya danƙa musu dukiya mai tamani, wato wa’azin bishara.—2 Kor. 4:7.

7 Shin mene ne hakan ya nuna? Sa’ad da Yesu yake ba wa almajiransa umurni cewa su almajirtar da mutane, kamar dai yana ba su talanti ne, wato “dukiyarsa.” (Mat. 25:14) Dukiyar ita ce wa’azi da kuma almajirtar da mutane.

8. Ko da yake yawan talanti da aka ba wa kowane bawa ya bambanta, mene ne maigidan ya bukace su su yi?

8 A kwatancin talanti, maigidan ya ba wa wani bawansa talanti guda biyar, ya ba na biyu talanti guda biyu kuma ya ba bawansa na uku talanti guda ɗaya kawai. (Mat. 25:15) Ko da yake yawan talanti da aka rarraba wa bayin ya bambanta, maigidan ya bukace dukansu su yi ƙwazo a yin kasuwanci da talantin, wato yin iya ƙoƙarinsu a wa’azin bishara. (Mat. 22:37; Kol. 3:23) Mabiyan Kristi sun soma yin kasuwanci da talantin a ƙarni na farko, a Fentakos ta 33 daga zamanin Yesu. An rubuta labarin wa’azin bishara da kuma almajirtarwa da suka yi a cikin Littafi Mai Tsarki a Ayyukan Manzanni. dA. M. 6:7; 12:24; 19:20.

YIN KASUWANCI DA TALANTIN A KWANAKI NA ƘARSHE

9. (a) Mene ne bayi biyu masu aminci suka yi da talanti da aka ba su, kuma mene ne hakan ya nuna? (b) Wane aiki ne “waɗansu tumaki” suke da shi?

9 A kwanaki na ƙarshe, musamman daga shekara ta 1919, shafaffu mabiyan Kristi masu aminci da ke duniya suna yin kasuwanci da talantin Maigidansu. Kamar bayi biyu na farko, ’yan’uwa shafaffu sun yi iya ƙoƙarinsu a yin wa’azi. A cikin kwatancin Yesu bawa ɗaya ya karɓi talanti biyar, ɗayan kuma biyu, hakan ba ya nufin cewa rukunin shafaffu dabam-dabam guda biyu ne. Bayi guda biyun sun ninka talanti da maigidansu ya ba su, saboda haka su biyun masu ƙwazo ne. Mene ne aikin waɗanda suke da begen zama a aljanna a duniya? Suna da aiki mai muhimmanci! A cikin kwatancin Yesu na tumaki da awaki, mun koya cewa waɗanda suke da begen zama a duniya suna da gatan taimaka wa ’yan’uwan Yesu shafaffu a yin wa’azi da kuma koyarwa. A waɗannan mawuyacin kwanaki na ƙarshe, rukuni biyun suna aiki tare a matsayin “garke ɗaya” a taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu.—Yoh. 10:16.

10. Wane fanni mai muhimmanci ne ya nuna cewa Yesu ya soma sarauta?

10 Maigidan, wato Yesu ya bukaci mabiyansa su kasance da ƙwazo. Kamar yadda aka ambata ɗazu, amintattu almajiransa na ƙarni na farko sun ƙara dukiyarsa. A ƙarni na farko kuma fa, wato a lokacin da kwatancin talanti yake cika? Amintattun bayin Yesu masu ƙwazo sun yi wa’azi da kuma almajirtar da mutane sosai fiye da dā. Saboda ƙwazonsu, dubban mutane suna zama almajirai a kowace shekara, hakan ya sa yin wa’azi ya zama fanni mai muhimmanci da ya nuna cewa Yesu ya soma sarauta. Babu shakka, Maigidansu ya yi farin ciki sosai!

Kristi ya danƙa wa bayinsa gatan yin wa’azi (Ka duba sakin layi na  10)

YAUSHE NE MAIGIDAN ZAI DAWO DON SU YI LISSAFI?

11. Me ya sa muka kammala cewa Yesu zai yi lissafi da bayinsa a lokacin ƙunci mai girma?

11 Yesu zai zo ya yi lissafi da bayinsa gab da ƙarshen ƙunci mai girma da ke nan tafe. Me ya sa muka ce hakan? A annabcinsa da ke rubuce cikin Matta surori 24 da 25, Yesu ya ambata zuwansa sau da sau. Da yake nuni ga hukunci da za a yi a lokacin ƙunci mai girma, Yesu ya ce mutanen “za su kuwa ga Ɗan mutum yana zuwa a bisa gizagizai na sama.” Ya ba mabiyansa da suke zama a wannan kwanaki na ƙarshe shawara cewa: “Ba ku sani ba cikin kowace rana Ubangijinku ke zuwa” kuma “sa’ar da ba ku sa tsammani ba Ɗan mutum yana zuwa.” (Mat. 24:30, 42, 44) Saboda haka, sa’ad da Yesu ya ce ‘ubangijin waɗannan bayi ya zo, ya yi lissafi da su,’ a bayane yake cewa yana magana ne game da lokacin da zai zo ya zartar da hukunci a ƙarshen wannan zamanin. e—Matt. 25:19.

12, 13. (a) Mene ne maigidan ya gaya wa bayi biyu na farko, kuma me ya sa? (b) A yaushe ne za a yi wa shafaffu hatimi na ƙarshe? (Ka duba akwatin nan “ Ba da Lissafi a Lokacin Mutuwa.”) (c) Wane lada ne waɗanda aka yi musu shari’a a matsayin tumaki za su samu?

12 A kwatancin, sa’ad da maigidan ya dawo, ya ga cewa bayi biyu na farko, wato wanda aka ba talanti biyar da wanda aka ba talanti biyu sun kasance da aminci, kowannensu ya ninka talanti da aka ba shi sau biyu. Maigidan ya yaba wa kowannensu ta cewa: “Madalla, bawan kirki, mai-aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa.” (Mat. 25:21, 23, Littafi Mai Tsarki) To mene, zai faru sa’ad da Maigidan, wato Yesu ya zo don ya zartar da hukunci?

13 Za a yi wa almajiransa shafaffu masu ƙwazo waɗanda bayi biyu na farko suke wakilta hatimi na ƙarshe kafin a soma ƙunci mai girma. (R. Yoh. 7:1-3) Kafin yaƙin Armageddon, Yesu zai ba su ladarsu na zuwa sama. Za a yi wa waɗanda suka taimaka wa ’yan’uwan Kristi shari’a a matsayin tumaki kuma za a ba su gatan yin rayuwa har abada a duniya.—Mat. 25:34.

MUGUN BAWA MAI ƘIWUYA

14, 15. Shin Yesu yana nufin cewa ’yan’uwansa shafaffu da yawa za su zama mugaye da kuma masu ƙiwuya? Ka yi bayani.

14 A kwatancin, bawa na ƙarshe ya binne talantinsa maimakon ya yi kasuwanci da shi ko kuma ya ba masu juya kuɗi. Wannan mugun bawa ne don bai so maigidan ya sami riba ba. Shi ya sa maigidan ya kira shi “mugun bawa mai-ƙiwuya.” Maigidan ya karɓi talantin daga hannunsa kuma ya ba wa bawa mai goma. Sai aka jefar da mugun bawan “cikin baƙin duhu.” A wurin ne zai “yi kuka da cizon haƙora.”—Mat. 25:24-30; Luk. 19:22, 23.

15 Ɗaya daga cikin bayin maigidan guda uku ya ɓoye talantinsa, shin Yesu yana nuna cewa kashi ɗaya cikin uku na mabiyansa shafaffu za su zama mugaye da kuma masu ƙiwuya? A’a. Ka yi la’akari da mahallin. A kwatancin bawan nan mai aminci mai hikima, Yesu ya yi maganar mugun bawa da yake dūkan ’yan’uwansa bayi. Ba wai yana nufin cewa za a yi wani rukunin mugun bawa ba. A maimakon haka, yana jan kunnen bawan nan mai aminci ne cewa kada ya zama kamar mugun bawa. Hakazalika, a almarar budurwai goma, Yesu ba ya nufin cewa rabin mabiyansa shafaffu za su zama kamar budurwai biyar marasa azanci. A maimakon haka, yana yi wa ’yan’uwansa shafaffu kashedi ne game da abin da zai faru idan suka daina kasancewa a faɗake da kuma a shirye. f Saboda haka, za mu iya cewa a kwatancin talantin, Yesu ba ya nufin cewa ’yan’uwansa shafaffu da yawa za su zama mugaye da kuma marasa ƙwazo. Akasin haka, Yesu yana yi wa mabiyansa shafaffu gargaɗi cewa su guji ayyuka da halayen mugun bawa kuma su yi ‘ciniki’ da talantin da aka ba su, wato su kasance da ƙwazo.—Mat. 25:16.

16. (a) Waɗanne darussa ne muka koya daga kwatancin talanti? (b) Wane ƙarin haske ne muka samu a wannan talifin game da kwatancin talanti? (Ka duba akwatin nan “ Yadda Ya Kamata Mu Fahimci Kwatancin Talanti.”)

16 Waɗanne darussa biyu muka koya daga kwatanci na talanti? Na farko, aikin da Maigidan, wato Kristi ya ba wa bayinsa shafaffu yana da tamani, aikin shi ne yin wa’azi da kuma almajirtar da mutane. Na biyu, Kristi yana so dukanmu mu kasance da ƙwazo a yin wa’azi. Idan muka yi hakan, Maigidan zai albarkace mu don hakan zai nuna cewa muna tsaro kuma muna da bangaskiya da aminci.—Mat. 25:21, 23, 34.

a An bayyana ko wane ne bawan nan mai aminci mai hikima a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2013, shafuffuka na 21-22, sakin layi na 8-10. An tattauna matsayin budurwai na almarar Yesu a talifin da ya gabaci wannan da ke wannan mujallar. An yi bayani a kan kwatancin awaki da tumaki a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1995, shafuffuka na 13-18.

c A zamanin Yesu, talanti guda ya yi daidai da denarii 6,000. Kafin ma’aikaci ya sami talanti guda yana bukatar ya yi aiki tuƙuru na tsawon shekara ashirin.

d Bayan mutuwar manzannin, Shaiɗan ya sa ridda kuma ta haɓaka a cikin ƙarnuka da yawa. A wannan lokacin, ba a mai da hankali ga umurnin da Yesu ya bayar na almajirtar da mutane ba. Amma hakan ya canja a “lokacin kaka,” wato kwanaki na ƙarshe. (Mat. 13:24-30, 36-43) Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2013, shafuffuka na 9-12.

e Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2013, shafuffuka na 7-8, sakin layi na 14-18.

f Ka duba sakin layi na 13 na talifi mai jigo: “Ka Ci Gaba da ‘Yin Tsaro’!” a wannan fitowar.