Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Ci gaba da Kasancewa da Aminci ga Mulkin Allah

Ka Ci gaba da Kasancewa da Aminci ga Mulkin Allah

Ba na duniya suke ba.”YOH. 17:16.

WAƘOƘI: 63, 129

1, 2. (a) Me ya sa kasancewa da aminci yake da muhimmanci ga Kirista, kuma yaya hakan zai shafi halinmu game da abubuwa da ke haddasa rigima? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Waɗanne abubuwa ne mutane suke kishinsu, amma mene ne sakamakon yin haka?

BAYIN Jehobah ba sa saka hannu a yaƙi da siyasa, ba sa nuna bambancin launin fata da kuma al’ada. Ƙari ga haka, ba sa kishin ƙasa. Me ya sa? Domin duka bayin Jehobah sun yi alkawari cewa za su so shi da zuciya ɗaya, su kasance da aminci a gare shi kuma su yi masa biyayya. (1 Yoh. 5:3) Ko da wace ƙasa ce muke, ko da ina ne muka fito, burinmu ne mu bi ƙa’idodin Allah. Muna nuna aminci ga Jehobah da kuma Mulkinsa fiye da kome. (Mat. 6:33) Saboda haka, bai kamata mu saka hannu a abubuwa da ke haddasa tashe-tashen hankula a duniyar nan ba.—Isha. 2:4; karanta Yohanna 17:11, 15, 16.

2 Mutane da yawa a duniya suna ƙishin ƙasarsu ko yarensu ko kuma al’adarsu, har ƙungiyar wasanni ta ƙasarsu. Abin baƙin ciki shi ne, irin wannan ƙishin ya hadassa gasa da ƙiyayya, kuma a wasu lokatai ya kai ga zub da jini har ma da kisan kāre dangi. Ko da ba ma saka hannu a irin waɗannan abubuwan, a wani lokaci yana shafanmu da kuma iyalanmu. Allah ya halicce mu da halin ƙin rashin adalci. Saboda haka, yana da sauƙi mu soma nuna goyon bayanmu game da wani al’amari idan gwamnati ta ɗauki wasu matakai da muke gani bai dace ba. (Far. 1:27; K. Sha. 32:4) Wane mataki ne ya kamata mu ɗauka a irin wannan yanayin? Za mu kasance tsaka tsaki ne ko kuma za mu goyi bayan wani rukuni?

3, 4. (a) Me ya sa Kiristoci ba sa saka hannu a tashe-tashen hankula da ake yi a wannan duniyar? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Sa’ad da ake rigima, hukumomi suna iya matsa wa mutane da yawa su nuna wariya. Amma Kiristoci na gaskiya ba sa hakan. Ba ma saka hannu a harkokin siyasa da kuma yaƙi. (Mat. 26:52) Kiristoci na gaskiya sun san cewa babu wata ƙungiya ko gwamnati a duniyar nan da ta fi wani kyau. (2 Kor. 2:11) Sa’ad da muka kasance tsaka tsaki a harkokin duniya, ba za mu saka hannu a tashe-tashen hankula da mutane suke yi ba.—Karanta Yohanna 15:18, 19.

4 Da yake mu ajizai ne, wataƙila wasu a cikinmu suna ƙoƙari su kawar da ra’ayin wariya da suke da shi a dā. (Irm. 17:9; Afis. 4:22-24) Saboda haka, za mu tattauna wasu ƙa’idodin da za su taimaka mana mu sha kan irin waɗannan ra’ayoyin. Za mu kuma bincika yadda za mu horar da kanmu don mu kasance da aminci ga Mulkin Allah.

DALILIN DA YA SA BA MA SAKA HANNU A HARKOKIN DUNIYAR NAN

5, 6. Yaya Yesu ya ɗauki mutane da suka fito daga wurare dabam-dabam a lokacin da yake duniya, kuma me ya sa?

5 Idan ka rasa abin da ya kamata ka yi a wani yanayi da ka sami kansa, zai dace ka tambayi kanka, ‘Da a ce Yesu ne, mene ne zai yi a wannan yanayin?’ Al’ummar da Yesu ya zauna a cikinta tana ƙunshe da mutane daga ɓangarori dabam-dabam, mutane daga Yahudiya da Galili da Samariya da kuma wasu wurare. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa an sami rashin jituwa tsakanin mutane da suka fito daga waɗannan wuraren. (Yoh. 4:9) Ƙari ga haka, an sami saɓani tsakanin Farisawa da Sadukiyawa (A. M. 23:6-9), tsakanin talakawan da masu karɓan haraji (Mat. 9:11), tsakanin Malaman addinin Yahudawa da kuma waɗanda ba malamai ba. (Yoh. 7:49) A ƙarni na farko, Romawa ne suke mulkin Isra’ilawa, saboda haka Isra’ilawa sun tsane su ba kaɗan ba. Duk da cewa Yesu ya yaɗa gaskiya game da Allah kuma ya ambata cewa Allah ya ɗauki Isra’ila a matsayin al’ummarsa, bai koya wa almajiransa cewa wasu mutane sun fi wasu ba. (Yoh. 4:22) A maimakon haka, ya umurce su su ƙaunaci dukan mutane.—Luk. 10:27.

6 Me ya sa Yesu bai nuna wariya kamar sauran Yahudawa ba? Domin shi da Jehobah ba masu nuna bambanci ba ne. Sa’ad da Jehobah ya halicci Adamu da Hawwa’u, ya so su haifi ’ya’ya kuma su mamaye duniya. (Far. 1:27, 28) Ƙari ga haka, Allah ya halicci ’yan Adam a yadda za su iya haifan ’ya’ya masu launin fata dabam-dabam. Saboda haka, Jehobah da Yesu ba sa ganin launin fata ko ƙasa ko kuma yaren wani mutum da muhimmanci fiye da na wani. (A. M. 10:34, 35; R. Yoh. 7:9, 13, 14) Wajibi ne mu yi koyi da su.—Mat. 5:43-48.

7, 8. (a) A wane batu ne ya kamata mu nuna goyon bayanmu? (b) Mene ne ya kamata mu amince da shi a batun magance matsalolin ’yan Adam?

7 Me ya sa ba ma goyon bayan wani mai mulki ko gwamnati? Domin muna goyon bayan Jehobah. Shi ne Maɗaukakin Sarki. Shaiɗan ya zargi Allah a kan yadda yake tafiyar da sarautarsa a lambun Adnin. A yanzu, wajibi ne kowa ya yi zaɓi a wannan batun, ko ya amince da sarautar Allah ko kuma na Shaiɗan. Shin kana nuna goyon bayanka ga sarautar Jehobah ta wajen bin dokokinsa da ƙa’idodinsa a maimakon yin abin da ka ga dama? Ka gaskata cewa Mulkin Allah ne zai magance dukan matsalolin ’yan Adam? Ko kana ganin cewa ’yan Adam za su iya mulkin kansu kuma su yi nasara?—Far. 3:4, 5.

8 Alal misali, idan wani ya tambaye ka mene ne matsayinka game da siyasa ko wasu ƙungiyoyin ’yan Adam, me za ka ce? Mutane da ke goyon bayan waɗannan ƙungiyoyin sun daɗe suna neman mafita ga matsalolin da ke hadassa rashin jituwa tsakanin ’yan Adam. Ƙari ga haka, suna ƙoƙari su magance waɗannan matsalolin da anniya. Duk da haka, Kiristoci sun amince cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai iya magance matsalolin ’yan Adam kuma ya kawar da dukan rashin adalci. Wajibi ne mu bar wannan batun a hannun Jehobah. Domin in da a ce kowane Kirista yana biɗan abin da yake gani ya fi kyau, da ba za a kasance da haɗin kai a cikin ikilisiya ba.

9. Wace matsala ce aka samu a ikilisiyar Korinti na ƙarni na farko, amma wace shawara ce manzo Bulus ya bayar?

9 Ka yi la’akari da matakin da wasu Kiristoci a ƙarni na farko suka ɗauka sa’ad da aka sami wata matsala da ke raba kan mutane. Wasu a Korinti suna cewa: “‘Ni na Bulus ne,’ wani kuwa, ‘Ni na Afolos ne,’ wani kuwa, ‘Ni na Kefas ne,’ ko kuwa, ‘Ni na Almasihu ne.’” Manzo Bulus bai ji daɗi ba sa’ad da ya ji hakan don hakan zai iya jawo babbar matsala a cikin ikilisiya. Saboda haka, Manzo Bulus ya yi wannan tambayar: “Kristi ya rarrabu ne?” Shin ta yaya za su magance wannan matsalar? Bulus ya shawarce su cewa: “Yanzu fa, ’yan’uwa, ina roƙonku, ta wurin sunan Ubangijinmu Yesu Kristi, dukanku ku yi magana ɗaya, kada tsatsaguwa su kasance a tsakaninku; amma ku zama cikakku cikin hankali ɗaya da shasara ɗaya.” Hakazalika, bai kamata mu bar wani abu ya ɓata haɗin kai da muke mora a cikin ƙungiyar Jehobah ba.—1 Kor. 1:10-13; karanta Romawa 16:17, 18.

10. Ta yaya manzo Bulus ya nuna cewa bai kamata Kirista ya saka baki a al’amuran da ke hadassa tashe-tashen hankula a wannan duniyar ba?

10 Bulus ya ƙarfafa shafaffun Kiristoci cewa ladansu yana sama, saboda haka, kada su mai da hankali ga “al’amuran duniya.” (Filib. 3:17-20) * Su jakadu ne a madadin Kristi. Jakadu ba sa saka baki a al’amuran ƙasar da aka aika su hidima. A maimakon haka, suna aiki da umurnin ainihin ƙasar da suke wakilta. (2 Kor. 5:20) Kiristocin da suke da begen yin rayuwa a aljanna a duniya ma talakawan Mulkin Allah ne. Saboda haka, ba zai dace su saka baki a al’amuran da ke haddasa tashe-tashen hankula a wannan duniyar ba.

KA HORAR DA KANKA DON KA KASANCE DA AMINCI GA JEHOBAH

11, 12. (a) Wane irin yanayi ne zai iya sa kasancewa da aminci ga Mulkin Allah ya yi wa Kirista wuya? (b) Wane yanayi ne wata ’yar’uwa ta sami kanta a ciki, kuma yaya ta bi da yanayin?

11 A wurare da yawa a faɗin duniya, mutane sukan kasance da tarihi da al’ada da kuma yare ɗaya. Saboda haka, sukan yi alfahari da inda suka fito. A irin wannan yanayin, ya kamata Kiristoci su horar da kansu don su ɗauki matakin da ya dace sa’ad da wani batu da zai haifar da wariya ya tashi. Ta yaya za su iya yin hakan?

12 Ka yi la’akari da Mirjeta * da ta fito daga wani yankin Yugoslaviya ta dā. An tsani Sabiyawa a inda ta girma. Sa’ad da ta koyi cewa Jehobah ba mai nuna bambanci ba ne kuma cewa Shaiɗan ne yake sa mutane su nuna ƙabilanci, sai ta yi ƙoƙari don ta daina nuna wannan halin. Duk da haka, sa’ad da aka soma yaƙi tsakanin ƙabilai dabam-dabam da ke yankin, sai Mirjeta ta soma tsanan Sabiyawa kuma ba ta so ta yi musu wa’azi. Amma ta fahimta cewa tana bukata ta ɗauki mataki idan tana so ta daina ƙabilanci. Ta roƙi Jehobah ya taimaka mata ta sha kan wannan matsalar kuma ta ƙara ƙwazo a hidimarta ta wajen zama majagaba. Ta ce: “Na zo na gane cewa mai da hankali ga hidimata ya taimaka mini ba kaɗan ba. . . . Sa’ad da nake wa’azi, ina ƙoƙari in so mutane kamar Jehobah, hakan ya taimaka min in daina nuna wariya.”

13. (a) Wane abu ne ya faru da ya ɓata wa wata ’yar’uwa rai, amma wane mataki ne ta ɗauka? (b) Wane darasi ne za mu koya daga labarin Zoila?

13 Zoila wata ’yar’uwa ce daga Meziko da ta ƙaura zuwa Turai kuma tana halartan taro a wata ikilisiya a can. Wasu ’yan’uwa da suka fito daga wani ɓangaren Amirka ta tsakiya da ke cikin ikilisiyar, sun yi baƙar magana game da al’ada da kuma kaɗe-kaɗen ƙasar da ’yar’uwa fito daga ciki. In da kai ne, me za ka yi? Hakika, Zoila ba ta ji daɗin abin da suka yi ba. Amma ta roƙi Jehobah ya taimaka mata don kada ɓacin rai ya sa ta yi abin da zai sa yanayin ya daɗa muni. Gaskiyar ita ce, wasu a cikinmu suna fama da irin waɗannan halaye. Ba zai dace mu faɗi ko kuma yi wani abin da zai haifar da rashin haɗin kai tsakanin mu da ’yan’uwanmu ko kuma wasu ba.—Rom. 14:19; 2 Kor. 6:3.

14. Ta yaya Kiristoci za su horar da kansu don su guji nuna wariya?

14 Shin a inda ka girma mutane suna kishin ƙasa da kuma wariya? Hakan ya shafi yadda kake bi da mutane? Bai kamata Kiristoci su bar wariya ta shafi yadda suke bi da mutanen da suka fito daga wani wuri ko wata ƙasa ba. Amma idan ka lura cewa kana da ra’ayin da bai dace ba game da mutanen da suka fito daga wata ƙasa ko al’ada ko yare ko kuma mutanen da launin fatarsu ya bambanta da naka fa? Zai dace ka yi tunani sosai a kan yadda Jehobah yake ɗaukan ƙishin ƙasa da nuna wariya. Kana iya yin bincike kai kaɗai ko kuma a ibada ta iyali game da irin waɗannan batutuwa. Bayan haka, ka yi addu’a don Jehobah ya taimaka maka ka kasance da irin ra’ayinsa a waɗannan batutuwan.—Karanta Romawa 12:2.

Jehobah yana so mu kasance da aminci ko da ana yi mana barazana (Ka duba sakin layi na 15 da 16)

15, 16. (a) Yaya wasu za su ɗauke mu idan muka fita dabam saboda amincinmu ga Allah? (b) Ta yaya za ka iya taimaka wa ’ya’yanka su kasance da aminci ga Jehobah a wannan batun?

15 A wasu lokatai, bayin Jehobah sukan sami kansu a yanayin da zai bukaci su fita dabam da sauran mutane, kamar abokan aikinsu ko ’yan ajinsu ko maƙwabtansu ko kuma wasu. (1 Bit. 2:19) Wajibi ne mu fita dabam idan hakan ya faru. Saboda haka, kada mu yi mamaki idan mutanen duniya sun tsane mu don Yesu ya ce hakan zai faru. Yawancin mutane da suke gāba da mu ba su san muhimmancin kasancewa tsaka tsaki a matsayinmu na Kiristoci ba. Amma wannan batu ne mai muhimmanci sosai a gare mu.

16 Jehobah yana so mu kasance da aminci ko da mutane suna yi mana barazana. (Dan. 3:16-18) Kasancewa dabam da sauran mutane bai da sauki, musamman ma ga matasa. Idan ’ya’yanka suna fuskantar matsaloli game da sara wa tuta ko kuma saka hannu a bukukuwan ƙasa, ka taimaka musu ba tare da ɓata lokaci ba. Ka taimaka wa yaranka su fahimci batun da kyau a Ibada ta Iyali don su kasance da ƙarfin hali sa’ad da suka fuskanci yanayin. Ka koya musu yadda za su bayyana bangaskiyarsu dalla-dalla kuma cikin sanin yakamata. (Rom. 1:16) Ƙari ga haka, za ka iya tattaunawa da malamansu game da batun idan da bukata.

KA GODE WA ALLAH SABODA DUKAN HALITTUNSA

17. Wane irin hali ne ya kamata mu guje wa, kuma me ya sa?

17 Mukan yi sha’awar mahalli da al’ada da yare da kuma abincin ƙasar da muka girma a ciki. Shin muna ɗauka cewa abubuwan da muke so sun fi na wasu mutane ne? Jehobah yana so mu ji daɗin rayuwa shi ya sa ya halicci abubuwa dabam-dabam. (Zab. 104:24; R. Yoh. 4:11) Saboda haka, ba zai dace mu ɗauka cewa yadda muke yin abubuwa shi ne ya fi kyau ba.

18. Ta yaya za mu amfana idan muka ɗauki mutane kamar yadda Jehobah yake ɗaukan su?

18 Nufin Allah ne dukan mutane su zo ga sanin gaskiya kuma su ji daɗin rayuwa har abada. (Yoh. 3:16; 1 Tim. 2:3, 4) Idan muka so mutanen da suka fito daga wurare dabam-dabam da zuciya ɗaya, za mu ji daɗin kasancewa tare kuma za mu kyautata haɗin kanmu. Yayin da muke ƙoƙarin yin biyayya ga Jehobah, wajibi ne mu guji saka hannu a tashe-tashen hankula da ake yi a wannan duniyar. Ba ma goyon bayan wani rukuni ko wata ƙungiya ta wannan duniya. Muna godiya ga Jehobah cewa ya ceto mu daga duniyar Shaiɗan da ke cike da rashin jituwa da girma kai da kuma abubuwan da ke haddasa rigima tsakanin mutane. Bari mu ƙudiri niyyar zaman lafiya da mutane ta kasancewa da ra’ayin marubucin zabura da ya ce: “Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma, Ga jama’ar Allah su zauna tare kamar ’yan’uwa!”—Zab. 133:1, Littafi Mai Tsarki.

^ sakin layi na 10 Filibi tana ƙarƙashin sarautar Roma. Wataƙila wasu a cikin ikilisiyar da ke wurin suna da ’yancin ’yan ƙasar Roma, saboda haka sun kasance da wasu gata da sauran ’yan’uwansu Kiristoci ba su da shi.

^ sakin layi na 12 An canja wasu sunaye.