Jehobah Allah Ne Mai Kauna
“Allah ƙauna ne.”—1 YOH. 4:8, 16.
WAƘOƘI: 18, 91
1. Wane hali na musamman ne Allah yake da shi, kuma ta yaya sanin hakan ya shafi yadda kake ji game da Shi?
LITTAFI MAI TSARKI ya ce: “Allah ƙauna ne.” Mene ne hakan yake nufi? Ƙauna ita ce halinsa na musamman. Ba kawai yana ƙaunar mutane ba, amma Shi ne ƙauna. (1 Yoh. 4:8) Abin farin ciki ne cewa Mahaliccin sararin sama da dukan abubuwan masu rai yana ƙaunarmu. Ƙauna ce take sa ya yi dukan abubuwan da yake yi.
2. Mene ne ƙaunar Allah take tabbatar mana? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
2 Allah yana ƙaunar mutane sosai kuma ya tabbatar mana cewa zai cika nufinsa ga ’yan Adam a yadda zai amfani dukan waɗanda suka amince da sarautarsa. Alal misali, saboda yadda Jehobah yana ƙaunarmu, “ya sanya rana, inda zai yi wa duniya duka shari’a mai-adalci ta wurin mutum wanda ya ƙadara,” wato Yesu Kristi. (A. M. 17:31) Mun tabbata cewa zai cika wannan alkawarin kuma hakan zai sa mutanen kirki da ke yi masa biyayya su ji daɗin rayuwa har abada.
ABIN DA TARIHIN ’YAN ADAM YA NUNA
3. Da a ce Allah bai nuna ƙauna ga ’yan Adam ba, kana ganin yaya rayuwa za ta kasance a nan gaba?
3 Kana ganin yaya rayuwa za ta kasance a nan gaba idan Allah bai ƙaunaci ’yan Adam ba? Ka yi la’akari da abubuwan da suka faru a tarihin gwamnatocin ’yan Adam da ke ƙarƙashin mugun nan da ya ƙi jinin ’yan Adam, wato Shaiɗan. (2 Kor. 4:4; 1 Yoh. 5:19; karanta Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12.) Da a ce Allah bai nuna mana ƙauna ba, da rayuwa a nan gaba za ta yi muni sosai.
4. Me ya sa Jehobah ya ƙyale ’yan Adam da Shaiɗan su yi sarauta?
4 Shaiɗan ya yi tawaye ga sarautar Allah kuma ya yaudare Adamu da Hawwa’u su yi hakan. Ya zargi Allah da yin sarauta da rashin adalci. Ta yin hakan, Shaiɗan yana da’awa cewa sarautarsa ta fi sarautar Allah wanda ya halicci kowa da kome. (Far. 3:1-5) Da yake Jehobah Allah ne mai hikima, ya ƙyale Shaiɗan ya yi sarauta na ɗan lokaci don ya nuna ko hakan gaskiya ne. Tarihi ya nuna cewa babu wanda zai iya yin sarauta cikin adalci kamar Allah. Munanan abubuwan da suka faru sun nuna cewa Shaiɗan ko ’yan Adam ba za su iya yin sarauta da adalci ba.
5. Mene ne tarihin ’yan Adam ya nuna?
5 A cikin shekaru 100 da suka shige, mutane fiye da miliyan 100 ne aka kashe a yaƙe-yaƙe. A yau, yanayin duniya sai daɗa muni yake yi. Abin da Littafin Mai Tsarki ya ce zai faru a “kwanaki na ƙarshe” na wannan zamanin ke nan don “miyagun mutane da masu-hila za su daɗa mugunta gaba gaba.” (2 Tim. 3:1, 13) Tarihi ya nuna cewa abin da Littafin Mai Tsarki ya ce gaskiya ne sa’ad da ya ce: “Ya Ubangiji, na tabbata hanyar mutum ba cikin nasa hannu take ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.” (Irm. 10:23) Hakika, Jehobah bai halicci ’yan Adam da baiwa ko izinin yin sarauta ba tare da ja-gorarsa ba.
6. Me ya sa Allah ya ƙyale mugunta na ɗan lokaci?
6 Ta wajen ƙyale ’yan Adam su yi sarauta na ɗan lokaci, Allah ya nuna cewa sarautarsa ne kawai zai yi nasara. A nan gaba Allah zai kawo ƙarshen mugunta da mugaye. Bayan haka, idan wani ya sake ƙalubalantar yadda yake sarauta, za a halaka shi nan da nan domin a lokacin, ba a bukatar a sake tabbatar da ko sarautar wane ne zai amfani ’yan Adam. Tarihi ya riga ya nuna cewa sarautar Allah ce ta fi kyau. Saboda haka, Allah ba zai bar mugunta ta sake kasancewa ba.
ABUBUWAN DA SUKA NUNA CEWA JEHOBAH YANA ƘAUNAR MU
7, 8. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya nuna ƙaunarsa?
7 Jehobah ya nuna ƙaunarsa ga ’yan Adam a hanyoyi da yawa. Ka yi la’akari da yadda abubuwan da Allah ya halitta a sararin sama suke da girma da kuma tsari. An tsara taurari dami-dami kuma kowane dami yana ɗauke da biliyoyin taurari da kuma duniyoyi. Rana tauraro ne da ke cikin damin tauraro da ake kira Milky Way galaxy, wanda duniyarmu ke ciki. Idan babu rana, babu abin da zai yi rai a duniya. Waɗannan abubuwan sun nuna cewa Allah ne ya halicce mu kuma sun bayyana ikonsa da hikimarsa da kuma ƙaunarsa. Hakika, “al’amuran Allah da ba su ganuwa, wato ikonsa madawwami da Allahntakarsa, a sarari ake ganinsu; ta wurin abubuwa da an halitta ana gāne su.”—Rom. 1:20.
8 Jehobah ya halicci dukan abubuwa Ru’ya ta Yohanna 4:11.) Ƙari ga haka, ‘yana ba da abinci ga dukan masu-rai, gama jinƙansa har abada ne.’—Zab. 136:25.
don halittunsa na duniya su amfana. Ya yi ’yan Adam da kamiltaccen jiki da hankali don su yi rayuwa har abada, kuma ya saka su a cikin wata aljanna mai kyan gaske. (Karanta9. Mene ne Jehobah ya tsana duk da cewa shi Allah ne mai ƙauna, kuma me ya sa?
9 Jehobah Allah ne mai ƙauna, duk da haka ya tsani mugunta. Alal misali, Zabura 5:4-6 sun ce game da Jehobah: “Gama kai ba Allah mai-yarda da mugunta ba ne. . . . Dukan masu-aika mugunta ka ƙi su.” An daɗa bayyana cewa: “Ubangiji yana ƙyamar mutum mai-neman zub da jini, mai-algus.”
ZA A KAWO ƘARSHEN MUGUNTA NAN BA DA DAƊEWA BA
10, 11. (a) Mene ne Jehobah zai yi wa miyagun mutane? (b) Wane lada ne Jehobah zai ba wa waɗanda suke yi masa biyayya?
10 Da yake Jehobah Allah ne mai ƙauna kuma ya tsani mugunta, ya yi alkawari cewa zai kawo ƙarshen mugunta a lokacin da ya dace. Kalmar Allah ta ce: “Gama za a datse masu-aika mugunta: amma waɗanda ke sauraro ga Ubangiji, su ne za su gāji duniya. Gama in an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi: . . . Maƙiyan Ubangiji kuma za su zama kamar kitsen ’yan raguna. Za su ƙare; kamar hayaƙi za su watse.”—Zab. 37:9, 10, 20.
11 Kalmar Allah ta daɗa cewa: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.” (Zab. 37:29) Waɗannan masu aminci “za su faranta zuciyarsu . . . cikin yalwar salama.” (Zab. 37:11) Allahnmu zai cika wannan alkawarin don yana son amintattun bayinsa su yi farin ciki a koyaushe. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah “zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” (R. Yoh. 21:4) Babu shakka, dukan waɗanda suka amince da sarautarsa kuma suna masa godiya saboda ƙaunarsa za su ji daɗin rayuwa a nan gaba!
12. Wane irin mutum ne “kamili”?
12 Jehobah ya gaya mana a cikin kalmarsa cewa: “Ka lura da kamili, ka duba kuma adili: Gama ƙarshen wannan mutum salama ne. Zancen masu-zunubi fa, za a hallaka su gaba ɗaya: Za a datse ƙarshen miyagu.” (Zab. 37:37, 38) “Kamili,” wato mai hankali yana nazarin kalmar Allah don ya san Allah da Ɗansa kuma ya yi nufin Allah da zuciya ɗaya. (Karanta Yohanna 17:3.) Irin wannan mutum ya gaskata da abin da aka rubuta a 1 Yohanna 2:17 cewa: “Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” Yayin da ƙarshen duniya yana gabatowa, yana da muhimmanci mu ‘yi sauraro ga Ubangiji, mu kiyaye tafarkinsa.’—Zab. 37:34.
WATA HANYA TA MUSAMMAN DA ALLAH YA NUNA MANA ƘAUNA
13. Wace hanya ce ta musamman Allah ya nuna mana ƙauna?
13 Ko da yake mu ajizai ne, za mu iya bin ‘tafarkin’ Jehobah. Ƙari ga haka, za mu iya ƙulla dangantaka ta kud da kud da shi don yadda ya nuna mana ƙauna a wata hanya ta musamman. Ya ba da ɗansa Yesu Kristi don ya fanshe mu daga zunubi da kuma mutuwa. (Karanta Romawa 5:12; 6:23.) Yesu shi ne ƙaunataccen Ɗan Allah kuma ya yi shekaru aru-aru yana yi masa biyayya a sama. Saboda haka, Jehobah ya amince da shi sosai. Da yake yana ƙaunar ɗansa sosai, ya yi baƙin ciki sa’ad da aka wulaƙanta Yesu a duniya. Amma Yesu ya kasance da aminci kuma ya nuna cewa Allah ne ya dace ya yi sarauta. Ƙari ga haka, ya nuna cewa kamilin mutum zai iya kasancewa da aminci ga Jehobah a cikin mawuyacin yanayi.
14, 15. Mene ne aka cim ma ta mutuwar Yesu?
14 Yesu ya kasance da aminci kuma ya goyi bayan sarautar Jehobah har mutuwa duk da cewa ya fuskanci gwaji mai wuya sosai. Muna godiya cewa ta mutuwarsa, ya fanshe mu daga zunubi da mutuwa kuma ya ba mu damar yin rayuwa har abada a sabuwar duniya da Allah yake shirya mana. Manzo Bulus ya bayyana yadda Jehobah da kuma Yesu suka ƙaunace mu sa’ad da ya ce: “Gama tun muna raunana tukuna, da cikar lokaci Kristi ya mutu domin marasa-ibada. Gama da ƙyar wani za ya yarda ya mutu sabili da mutum mai-adalci; wataƙila dai sabili da nagarin mutum wani ya yi ƙarfin hali har shi mutu. Amma Allah yana shaidar ƙaunatasa garemu, da yake, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.” (Rom. 5:6-8) Manzo Yohanna ya rubuta cewa: “Inda aka bayyana ƙaunar Allah gare mu ke nan, Allah ya aike Ɗansa haifaffensa kaɗai cikin duniya, domin mu rayu ta wurinsa. Nan akwai ƙauna, ba cewa mu ne muka yi ƙaunar Allah ba, amma shi ne ya ƙaunace mu, ya aike Ɗansa kuma ya biya hakin zunubanmu.”—1 Yoh. 4:9, 10.
15 Yesu ya bayyana yadda Allah yake ƙaunar ’yan Adam sa’ad da ya ce: “Gama Allah ya yi ƙaunar [mutane da suka cancanci ceto na] duniya har ya ba da Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana ba da gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yoh. 3:16) Saboda yadda Allah yake ƙaunar ’yan Adam, ya ba da Ɗansa don ya fanshe mu duk da cewa mutuwar Yesu ya sa Allah baƙin ciki sosai. Ƙaunar Allah ba ta da iyaka kuma mun tabbata da hakan. Manzo Bulus ya ce: “Gama na kawar da shakka, ba mutuwa, ba rai, ba mala’iku, ba sarautai, ba al’amuran yanzu, ba al’amura na zuwa, ba ikoki, ba tsawo, ba zurfi, ba kuwa wani halittaccen abu, da za ya iya raba mu da ƙaunar Allah, wadda ke cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.”—Rom. 8:38, 39.
SARKIN MULKIN ALLAH YA SOMA SARAUTA
16. Wane Mulki ne Allah ya ƙafa, kuma wane ne Sarkin Mulkin?
16 Allah ya ƙafa Mulkin Almasihu kuma ta hakan ya nuna cewa yana ƙaunar ’yan Adam. Yesu ne Sarkin da Jehobah ya naɗa. Yesu Kristi ya cancanci ya yi sarauta kuma yana ƙaunar ’yan Adam. (Mis. 8:31) Ƙari ga haka, ya zaɓi mutane 144,000 don su yi sarauta tare da Kristi a sama. Sa’ad da aka ta da su kuma suka je sama, za su cancanta su yi sarauta don sun taɓa yin rayuwa a duniya. (R. Yoh. 14:1) Mulkin Allah shi ne abin da Yesu ya yi wa’azinsa sa’ad da yake duniya kuma ya gaya wa almajiransa su yi addu’a cewa: “Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.” (Mat. 6:9, 10) Ba ƙaramin albarka ba ne amintattun ’yan Adam za su samu a lokacin da Allah zai amsa wannan addu’a!
17. Ka fadi bambancin da ke tsakanin sarautar Yesu da na ’yan Adam.
17 Sarautar Yesu ta bambanta sosai da na ’yan Adam. Mulkin ’yan Adam ya hadassa yaƙe-yaƙe da suka yi sanadin mutuwar miliyoyin mutane. Kamar Jehobah, Yesu yana ƙaunar ’yan Adam kuma zai kula da talakawan da za su zauna a ƙarƙashin Mulkinsa. (R. Yoh. 7:10, 16, 17) Yesu ya ce: “Ku zo gareni, dukanku da kuke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗaukar wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma mara-nauyi.” (Mat. 11:28-30) Hakika, wannan alkawari mai ban ƙarfafa ne!
18. (a) Mene ne Allah yake yi tun shekara ta 1914? (b) Mene ne za a tattauna a talifi na gaba?
18 Annabcin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu ya soma sarauta a Mulkin Allah sa’ad da aka soma kwanaki na ƙarshe a shekara ta 1914. Tun daga lokacin, Allah yana tattara waɗanda za su yi sarauta tare da Yesu a sama da kuma waɗanda da za su tsira daga wannan zamanin zuwa sabuwar duniya, wato “taro mai-girma.” (R. Yoh. 7:9, 13, 14) Yaya girma wannan taron yake? Mene ne ake bukata daga gare su? Za a ba da amsa ga waɗannan tambayoyin a talifi na gaba.