Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Waye ne mahaifin Yusufu?

Kafintan nan Banazarat mai suna Yusufu ne maigidan Maryamu mahaifiyar Yesu. Amma wane ne mahaifin Yusufu? Linjilar Matta ta nuna cewa Yaƙub ne. Amma Linjilar Luka ta ce shi “ɗan Heli” ne. Me ya sa aka sami bambanci a waɗannan nassosi biyu?​—⁠Luka 3:​23, Littafi Mai Tsarki; Matta 1:⁠16.

Littafin Matta ya ce: ‘Yaƙub ya haifi Yusufu,’ kuma a nan an yi amfani da kalmar Helenanci da ta nuna dalla-dalla cewa Yaƙub ne ya haifi Yusufu. Saboda haka, Matta ya yi magana ne a kan ainihin zuriyar Yusufu, wato zuriyar sarki Dauda daga inda Yesu ma ya gāji gadon sarauta.

Akasin haka, littafin Luka ya ce: Yusufu “ɗan Heli” ne. Wannan furucin ‘ɗa’ yana iya nufin “suruki” ma. An samu irin wannan furucin a Luka 3:​27, inda Littafi Mai Tsarki ya kira Sheyaltiyel “ɗan Niri.” Amma ainihin mahaifin Sheyaltiyel Yekoniya ne. (1 Labarbaru 3:17; Matta 1:​12, LMT) Mai yiwuwa Sheyaltiyel ya auri ‘yar Niri da ba a ambata sunanta ba, kuma shi ya sa ya zama surukinsa. Hakazalika, za a iya ce Yusufu “ɗan” Heli ne da yake shi ya auri Maryamu ‘yar Heli. Don haka, za mu ga cewa Linjilar Luka ta yi magana ne a kan ainihin zuriya na “jiki,” wato zuriyar da aka haifi Maryamu. (Romawa 1:⁠3) Don haka, mun ga cewa Littafi Mai Tsarki ya yi magana a kan zuriya biyu na Yesu, wato zuriyar Yusufu da na Maryamu.

Waɗanne irin tufafi da kuma rini ne ake amfani da su a zamanin dā?

Ulun da aka yi masa rini a Shekara ta 135 B.H.Y. da aka samo a wani ƙogon Dutse kusa da tekun gishiri

A Gabas ta Tsakiya ta dā, ana yawan yin tufafi da gashin raguna da na awaki da kuma na rakumai. Ulu ne abin da aka fi amfani da shi, kuma Littafi Mai Tsarki ya yi magana a kan tumaki da aske gashin dabbobi da kuma tufafin da aka yi da ulu. (1 Sama’ila 25:2; 2 Sarakuna 3:4; Ayuba 31:20) Ana noman rama da ake yin tufafi da shi a ƙasar Masar da Isra’ila. (Farawa 41:42; Joshua 2:6) Wataƙila ba a noman auduga a ƙasar Isra’ila, amma Nassi ya ambata cewa ana amfani da shi a ƙasar Fasiya. (Esther 1:6) Siliki tufafi ne mai tsadar gaske a dā kuma wataƙila ana samun sa a wurin ’yan kasuwa da suke fitowa daga Gabashin Asiya kaɗai.​—Ru’ya ta Yohanna 18:11, 12.

Wani littafi mai suna Jesus and His World (Yesu da Zamaninsa) ya ce: “Ana iya samun ulu mai kala dabam-dabam, yana iya zama fari sol ko kuma mai ruwan ƙasa da ke da layi-layi.” Ƙari ga hakan, ana yawan yi wa ulu rini. Wani rini mai tsada kuma da ake amfani da shi yana da launin shunayya kuma ana samun sa ne daga wani irin dodon koɗi. Ana kuma samun wasu kayan rini daga ƙananan bishiyoyi da jijiyoyi da ganyaye da kuma ƙwari. Kalolin da ake samu daga cikinsu su ne ja da ruwan ɗorawa da ruwan bula da kuma baƙi.