Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Bin Gargaɗi Zai Iya Sa Ka Tsira!

Bin Gargaɗi Zai Iya Sa Ka Tsira!

A RANAR 26 ga Disamba, 2004, wata girgizar ƙasa mai ƙarfin awo 9 da ɗigo 1 ta afka wa tsibirin Simeulue da ke arewa matso yammacin Sumatra, a ƙasar Indonisiya. Dukan mazaunan tsibirin sun mai da hankali a kan tekun. Ruwan tekun ya soma koma baya fiye da yadda ya saba. Sai farat ɗaya, kowa ya soma gudu zuwa kan tudu, suna ihu, “Smong! Smong!” wato guguwar tsunami ke nan a yarensu. A cikin mintoci 30, guguwar ta shigo cikin garin kuma ta halaka yawancin gidaje da ƙauyuka da ke tsibirin.

Guguwar tsunamin ta fara afka wa tsibirin Simeulue ne. Amma mutane bakwai kawai cikin mazauna dubu saba’in da takwas ne suka rasa rayukansu. Me ya sa mutane da yawa ba su mutu ba? * Abin da mazaunan tsibirin suka saba cewa shi ne: ‘Idan guguwa ta sa ruwan teku ya koma baya, to kowa ya soma gudu zuwa kan tudu domin idan ruwan ya dawo, zai shiga cikin gari.’ Abubuwan da suka taɓa faruwa sun sa mazaunan Simeulue sun san lokacin da guguwar tsunami take gab da aukuwa. Bin wannan gargaɗin ya sa sun tsira.

Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da guguwar da ke tafe, wato “ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har yanzu, ba kuwa za a yi ba dadai.” (Matta 24:21) Wannan ba ƙarshen doron ƙasa ba ne sanadiyyar ɓatancin ‘yan Adam kuma ba guguwa ba ce. Me ya sa? Domin nufin Allah shi ne wannan duniyar ta kasance har abada. (Mai-Wa’azi 1:⁠4) Amma Allah zai yi amfani da wannan ƙuncin don ya ‘halaka waɗanda ke halaka duniya.’ Wannan ƙuncin zai cire dukan mugunta da kuma wahala. (Ru’ya ta Yohanna 11:18; Misalai 2:22) Babu shakka, za mu sami kwanciyar hankali sosai bayan wannan lokacin!

Bugu da ƙari, wannan halakar da ke tafe ba ta kamar tsunami da girgizar ƙasa da kuma aman wuta domin ba zai kashe mutane marasa laifi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah ƙauna ne,” kuma Allah wanda sunansa Jehobah ne ya yi alkawari cewa “masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.” (1 Yohanna 4:8; Zabura 37:29) Me za ka yi don ka tsira wa ƙunci mai girma kuma ka more albarkun da aka yi mana alkawarinsu? Abin da zai taimaka maka shi ne bin gargaɗi!

KA LURA DA YANAYIN DUNIYA DA KE CANJAWA

Ba za mu iya sanin kwanan watan da za a cire mugunta da kuma wahala ba, domin Yesu ya ce: “Zancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani, ko mala’iku na sama, ko Ɗa, sai Uba kaɗai.” Ƙari ga haka, Yesu ya ƙarfafa mu mu “yi tsaro.” (Matta 24:36; 25:13) Mu yi tsaro a kan me? Littafi Mai Tsarki ya kwatanta abubuwan da za su faru a duniya kafin Allah ya kawo ƙarshen mugunta. Kamar yadda ruwan tekun da ya koma baya ya faɗakar da mazaunan Simeulue cewa guguwar tsunami na nan tafe, hakan ma canje-canjen yanayin duniya zai faɗakar da mu cewa ƙarshe ya kusa. Akwatin da ke gaba ya nuna yanayoyin da Littafi Mai Tsarki ya yi magana a kai.

Gaskiya ne cewa wasu cikin yanayoyin da aka ambata a cikin wannan akwatin sun faru a zamanin dā. Amma Yesu ya ce sa’ad da muka ga ‘waɗannan al’amura duka,’ mu san cewa ƙarshe ya kusa. (Matta 24:33) Ka tambayi kanka, ‘Yaushe ne dukan abubuwan da aka bayyana (1) suka faru a dukan duniya, (2) suka faru a lokaci ɗaya, kuma (3) suka ci gaba da yin muni?’ Babu shakka, muna rayuwa a wannan lokacin.

YADDA ALLAH YA NUNA YANA ƘAUNARMU

Wani tsohon shugaban Amirka ya ce: “Gargaɗi yana sa mutane su tsira.” Bayan guguwar tsunamin da ta auku a 2004, an saka na’urar faɗakarwa a wuraren da guguwar ta shafa don kada mutane su sake mutuwa haka a nan gaba. Hakazalika, Allah yana faɗakar da mutane kafin ƙarshe ya zo. Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa: ‘Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’an nan matuƙa za ta zo.’​—⁠Matta 24:⁠14.

A shekarar da ta shige, Shaidun Jehobah sun yi wa’azi na sa’o’i wajen biliyan 2 a ƙasashe 240 kuma a harsuna sama da 700. Wannan wa’azin da ake yi ya nuna sosai cewa ƙarshe ya kusa. Shaidun Jehobah suna ƙwazo wajen gargaɗar da mutane cewa ranar da Allah zai hukunta miyagu ya kusa kuma ƙauna ce ta sa muke faɗakar da maƙwabtanmu. (Matta 22:39) Wannan gargaɗin da kake karantawa ya nuna cewa Allah yana ƙaunarka. Ya kamata ka tuna cewa Allah ba ya son kowa ya ‘halaka, amma duka su kai ga tuba.’ (2 Bitrus 3:⁠9) Shin za ka nuna godiya ga Allah ta wajen bin gargaɗinsa?

KA NEMI MAFAKA!

Ka tuna cewa mazaunan Simeulue sun haura zuwa kan tudu don su tsira da zarar sun ga ruwan tekun ya soma koma baya. Matakin da suka ɗauka ya sa sun tsira. Idan kana son ka tsira wa wannan ƙuncin, dole ne ka hau tudu kafin lokaci ya kure. Ta yaya za ka yi hakan? Annabi Ishaya ya yi magana game da gayyatar da ake yi wa mutane “a cikin kwanaki na ƙarshe,” wato a wannan zamanin da muke ciki. Ya ce: “Ku zo, mu hau zuwa dutsen Ubangiji, . . . Za ya koya mana tafarkunsa, mu kuma mu kama tafiya cikin hanyoyinsa.”​—⁠Ishaya 2:​2, 3.

Kasancewa a kan tudu yana ba mutum zarafin ganin gari sosai da kuma samun mafaka. Hakazalika, sanin tafarkin Allah a cikin Littafi Mai Tsarki yana taimaka wa miliyoyin mutane a faɗin duniya a yau su yi canje-canje a rayuwarsu. (2 Timotawus 3:​16, 17) Yin haka yana taimaka musu su yi tafiya ‘cikin hanyoyin’ Allah kuma su sami tagomashinsa da kuma kāriya.

Shin za ka karɓi wannan gayyatar da kuma kāriyar da Allah yake mana a wannan kwanaki na ƙarshe? Muna ƙarfafa ka ka bincika bayanan da suka nuna cewa muna rayuwa a “kwanaki na ƙarshe” a cikin akwatin da ke wannan talifin. (2 Timotawus 3:⁠1) Shaidun Jehobah da ke yankinku za su yi farin cikin taimaka maka ka fahimci abubuwan da nassosi suka ce da kuma yadda za ka bi su. Za ka kuma iya samun amsoshin tambayoyinka a dandalinmu na www.pr418.com/⁠ha. Ka duba ƙarƙashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > AN AMSA TAMBAYOYIN LITTAFI MAI TSARKI.

^ sakin layi na 3 Mutane sama da dubu ɗari biyu da ashirin ne suka rasa rayukansu sanadiyyar wannan guguwar tsunami da ta auku a 2004 kuma ba a taɓa yin tsunamin da ya yi irin wannan ɓarnar ba.