Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Bincike Mafi Muhimmanci da Kake Bukatar Ka Yi

Bincike Mafi Muhimmanci da Kake Bukatar Ka Yi

KANA ɗaukan kanka a matsayin Kirista kuwa? Idan haka ne, kana ɗaya daga cikin mutane fiye da biliyoyi biyu a faɗin duniya da ke da’awa cewa su Kiristoci ne. Muna da dubban ɗariku da suke da’awa cewa su Kiristoci ne amma koyarwarsu da ra’ayinsu ba ɗaya ba ne. Kuma wataƙila abubuwan da ka yi imani da su sun bambanta da na wasu Kiristoci. Shin abin da ka yi imani da shi yana da wani muhimmanci ne? Hakika yana da muhimmanci idan kana son ka yi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce Kiristoci su riƙa yi.

An san mabiyan Yesu na ƙarni na farko da sunan nan “Kirista.” (Ayyukan Manzanni 11:26) Ba a kira su da wasu sunaye ba don imaninsu ɗaya ne a lokacin. Kiristocin sun bi koyarwa da kuma umurnin wanda ya kafa Kiristanci, wato Yesu Kristi. Kana gani cocinku yana koyar da abin Kristi ya ce da kuma abin da Kiristoci na farko suka yi imani da shi? Ta yaya za ka tabbatar da hakan? Littafi Mai Tsarki ne kaɗai zai iya taimaka mana mu san gaskiyar.

Ka yi la’akari da wannan: Yesu Kristi ya daraja Littafi Mai Tsarki kuma ya ɗauke shi a matsayin Kalmar Allah. Bai amince da waɗanda suka yi watsi da koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma suka mai da hankali ga koyarwar mutane ba. (Markus 7:9-13) Amma muna da tabbaci cewa mabiyan Yesu na gaske suna bin koyarwar Littafi Mai Tsarki. Don haka, ya kamata Kiristoci su tambayi kansu, ‘Abin da ake koyarwa a cocinmu ya yi daidai da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa kuwa?’ Idan kana son ka san amsar, zai dace ka gwada abin da cocinku yake koyarwa da kuma wanda Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.

Yesu ya ce ya kamata mu riƙa bauta cikin gaskiya kuma wannan gaskiyar tana cikin Littafi Mai Tsarki. (Yohanna 4:24; 17:17) Kuma manzo Bulus ya ce idan muna so mu sami ceto, ya kamata mu ‘san gaskiya.’ (1 Timotawus 2:4) Don haka, yana da muhimmanci abin da muka yi imani da shi ya zama gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Me ya sa? Don idan ba mu yi hakan ba, ba za mu sami ceto ba!

KA GWADA ABIN DA KA YI IMANI DA SHI DA LITTAFI MAI TSARKI

Muna so ka karanta tambayoyi shida na gaba da kuma amsoshin da ke Littafi Mai Tsarki. Ka karanta ayoyin Littafi Mai Tsarki da ke wurin kuma ka yi tunani sosai a kan su. Bayan haka, sai ka tambayi kanka, ‘Ana koyar da Littafi Mai Tsarki a cocinmu kuwa?’

Wannan ɗan bincike da kuma tunanin da za ka yi za su taimaka maka sosai a bincike mai muhimmanci da kake bukatar yi. Za ka so ka bincika don ka tabbatar da cewa abin da ake koyarwa a cocinku ya jitu da Littafi Mai Tsarki kuwa?Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimaka maka ka bincika ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Zai dace ka gaya wa ɗaya daga cikinsu ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai kyauta. Ko kuma ka shiga dandalinmu na jw.org/ha.