Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | A INA ZA KA IYA SAMUN ƘARFAFA?

Samun Karfafa a Lokacin Wahala

Samun Karfafa a Lokacin Wahala

Mutane suna fuskantar matsaloli iri-iri. Saboda haka, ba za mu iya tattauna dukan su a wannan talifin ba. Amma bari mu yi magana a kan huɗu cikinsu da muka ambata ɗazun. Ka yi la’akari da yadda Allah ya ƙarfafa waɗannan mutanen da ke fuskantar matsaloli.

IDAN AN SALLAME KA DAGA AIKI

“Na ga cewa ya dace in yi kowane irin aiki kuma mun rage kuɗin da muke kashewa.”​—In ji Jonathan

Wani mai suna Seth * ya ce: “An sallame ni da kuma matata Priscilla daga aiki a lokaci ɗaya. Bayan haka, muka yi shekara biyu muna biyan bukatunmu ta wajen yin ƙodago da kuma karɓan taimako daga danginmu. A sakamakon haka, matata ta yi baƙin ciki sosai kuma ta gaji da rayuwa.”

“Mene ne ya taimaka mana mu jimre? Matata Priscilla tana yawan tunawa da abin da Yesu ya ce a littafin Matta 6:34. Ayar ta ce kada mu damu don gobe, tun da kowace rana tana ɗauke da nata wahala. Kuma addu’o’in da ta yi sun taimaka mata ta jimre. Ni kuma abin da ya taimaka mini shi ne littafin Zabura 55:22. Na yi koyi da marubucin wannan zaburar domin na gabatar da wahalata ga Jehobah, kuma na lura cewa ya taimake ni. Ko da yake na sami aiki yanzu, amma muna sauƙaƙa salon rayuwarmu cikin jituwa da shawarar da Yesu ya bayar a Matta 6:​20-22. Ƙari ga haka, mun daɗa kusantar Allah da kuma juna.”

Jonathan ya ce: “Hankalina ya tashi sosai sa’ad da sana’armu ta soma noƙewa. Hakan ya sa abubuwan da muka cim ma cikin shekara 20 suka bi iska. Sai ni da matata muka soma gardama a kan kuɗi. Mun ƙi cin bashi domin muna tsoro cewa kamfanonin ba da bashi ba za su yarda su ba mu ba.

“Amma Kalmar Allah da kuma ruhunsa sun taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau. Na ga cewa ya dace in yi kowane irin aiki kuma mun rage kuɗin da muke kashewa. Kuma ʼyan’uwanmu Shaidun Jehobah sun taimaka mana. Sun rufe mana asiri kuma sun taimaka mana sa’ad da muke cikin yanayi mai wuya.”

IDAN AURE YA MUTU

Raquel ta ce: “Na yi baƙin ciki da kuma fushi sosai sa’ad da maigidana ya sake ni. Amma na kusaci Jehobah kuma ya ƙarfafa ni. Allah ya sanyaya zuciyata yayin da na yi addu’a gare shi. Ya magance matsalata.

“Ina farin ciki sosai domin Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki ta taimaka mini in daina fushi da kuma baƙin ciki. Na yi bimbini a kan furucin nan na manzo Bulus da ke Romawa 12:21: ‘Kada ku rinjayu ga mugunta, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.’

“Da ‘akwai lokacin sakewa.’ . . . A yanzu, na kafa wa kaina sababbin maƙasudai.”​—In ji Raquel

“Wani abokina ya taimaka mini in ci gaba da harkokina na yau da kullum. Ya nuna mini Mai-Wa’azi 3:6 kuma ya gaya mini cewa ‘akwai lokacin sakewa.’ Ko da yake shawarar tana da wuyan bi, amma abu ne da nake bukata. A yanzu, na daina damuwa a kan abin da ya faru kuma ina yin abubuwan da ke sa ni farin ciki.”

Wata mai suna Elizabeth ta ce: “Mutane suna bukatar ƙarfafa sa’ad da aurensu ya mutu. Ina da wata ƙawa da ta taimaka mini a kai a kai. Ta yi kuka sa’ad da nake kuka, ta ƙarfafa ni kuma ta nuna mini cewa tana ƙaunata sosai. Ina da tabbaci cewa Jehobah ya yi amfani da ita wajen ƙarfafa ni.”

CIWO KO KUMA TSUFA

“Bayan na gama addu’a, ruhunsa yana ƙarfafa ni.”​—In ji Luis

Luis da muka ambata a talifi na farko yana da ciwon zuciya mai tsanani kuma sau biyu, ya kusan mutuwa. A yanzu, ana saka masa iskar ƙara numfashi, wato oxygen sa’o’i 16 a rana. Ya ce: “Ina addu’a ga Jehobah a kowane lokaci. Kuma bayan na gama addu’a, ruhunsa yana ƙarfafa ni. Addu’a tana hana ni yin sanyin gwiwa domin na yi imani ga Allah kuma na san cewa yana kula da ni.”

Wata da ta ba shekara 80 baya, mai suna Petra ta ce: “Akwai abubuwa da dama da nake so in yi, amma na kasa. Ganin yadda nake kasala yana sa ni baƙin ciki. Ina kasala sosai kuma ina shan magunguna kullum. Ina yawan tunani a kan yadda Yesu ya roƙi Jehobah cewa idan zai yiwu, ya cire wata wahalar da yake gab da fuskanta. Amma Jehobah ya ƙarfafa Yesu. Yin addu’a kullum yana taimaka mini. Ina samun ƙarfi a duk lokacin da na yi addu’a ga Allah.”​—Matta 26:39.

Wani mai suna Julian da ya yi wajen shekara 30 yana fama da ciwon ƙwaƙwalwa da kuma kashin baya, ya ce: “Na bar zama a kan kujera mai kyau, kuma na koma zama a kan keken guragu. Amma rayuwata tana da ma’ana domin ina bauta wa Allah da aminci. Bayarwa zai iya cire wahala, kuma Jehobah yana cika alkawarinsa cewa zai ƙarfafa mu a duk lokacin da muke da bukata. Ina ji yadda manzo Bulus ya ji sa’ad da ya ce: ‘Zan iya yin abu duka ta wurin Kristi da yake ƙarfafani.’ ”​—Filibiyawa 4:13.

SA’AD DA WANI YA RASU

Wani mai suna Antonio ya ce: “Na yi mamaki sosai sa’ad da na ji cewa mahaifina ya rasu sanadiyyar hatsarin mota. A gaskiya, direban ya cuce mu domin a bakin titi mahaifinmu yake tafiya. Amma lamarin ya fi ƙarfina. Ya fita daga hayyacinsa har tsawon kwana biyar kafin ya rasu. Ina riƙe kaina sa’ad da nake tare da mahaifiyata, amma ina kuka sosai sa’ad da ba ta nan. Na ci gaba da yi wa kaina wannan tambayar, ‘Me ya sa hakan ya faru?’

“A waɗannan mawuyacin lokaci, na ci gaba da roƙon Jehobah ya taimaka mini in iya riƙe kaina. Kuma da sannu-sannu, na sami ƙarfin jimrewa. Na tuna cewa Littafi Mai Tsarki ya ce ‘tsausayi’ zai iya afko wa kowannenmu. Ina da tabbaci cewa zan sake haɗuwa da mahaifina sa’ad da ya tashi daga matattu domin Allah ba ya ƙarya.”​—⁠Mai-Wa’azi 9:11; Yohanna 11:25; Titus 1:2.

“Ko da yake ɗanmu ya rasu sanadiyyar hatsarin jirgin sama, amma har ila muna tunawa da abubuwan da muka cim ma tare kuma hakan na sa mu farin ciki.”​—In ji Robert

Robert da aka ambata a talifi na farko ma ya ji hakan. Ya ce: “Addu’ar da muke yi ga Jehobah ta sa ni da matata Maribel mun shaida irin salamar da Filibiyawa 4:​6, 7 suka ambata. Hakan ya taimaka mana mu gaya wa maneman labarai game da begen tashin matattu. Ko da yake ɗanmu ya rasu sanadiyyar hatsarin jirgin sama, amma har ila muna tunawa da abubuwan da muka cim ma tare kuma hakan na sa mu farin ciki. Muna ƙoƙari don mu mai da hankali a kan waɗannan abubuwan.

“Sa’ad da ‘yan’uwanmu Shaidu suka gaya mana cewa sun gan mu a talabijin muna gaya wa maneman labarai abin da muka yi imani da shi, mun gaya musu cewa addu’o’insu ne suka taimaka mana. Ina da tabbaci cewa Jehobah yana yin amfani da su ne don ya ƙarfafa mu.”

Kamar yadda waɗannan misalan suka nuna, Allah zai iya ƙarfafa mutanen da suke fuskantar matsaloli da kuma ƙalubale iri-iri. Kai fa? Ko da wane irin matsala ce kake fuskanta a rayuwa, za ka iya samun ƙarfafa. * Zai dace ka ce Jehobah ya taimaka maka. Shi ne “Allah na dukan ta’aziyya.”​—⁠2 Korintiyawa 1:3.