Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mene ne Mulkin Allah?

Mene ne Mulkin Allah?

Mene ne Mulkin Allah?

WASU SUN CE sarautar da Allah yake yi a cikin zuciyar mutum ne; wasu kuma sun ce yana nufin ƙoƙarin da ‘yan Adam suke yi don su kawo salama da haɗin kai a duniya. Mene ne ra’ayinka?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, . . . za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki [na ‘yan Adam] ya cinye su.” (Daniyel 2:44) Mulkin Allah gwamnati ce ta gaske.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Mulkin Allah yana iko a sama.​—Matta 10:7; Luka 10:9.

  • Allah yana amfani da Mulkinsa wajen cim ma nufinsa a sama da duniya.​—Matta 6:10.

Yaushe ne Mulkin Allah zai zo?

ME ZA KA CE?

  • Babu wanda ya sani

  • Nan ba da daɗewa ba

  • Ba zai taɓa zuwa ba

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Matta 24:14) Da zarar an yi wa’azin bisharar nan a ko’ina, Mulkin zai cire dukan muguntar da ke faruwa a duniyar nan.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Babu kowa a duniya da ya san ranar da Mulkin Allah zai zo.​—Matta 24:36.

  • Annabcin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Mulkin zai zo nan ba da daɗewa ba.​—Matta 24:​3, 7, 12.