Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

‘Ku Tafi . . . , Ku Almajirtar da Dukan Al’ummai’

‘Ku Tafi . . . , Ku Almajirtar da Dukan Al’ummai’

“Ku tafi . . . , ku almajirtar da dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma, . . . kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.”—MAT. 28:19, 20.

WAƘOƘI: 141, 97

1, 2. Bisa ga abin da Yesu ya ambata a Matta 24:14, waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi?

WASU mutane sun amince da wa’azin da muke yi, wasu kuma suna hamayya da mu. Amma mutane da yawa sun amince cewa Shaidun Jehobah sun shahara a yin wa’azin bishara. Wataƙila ka taɓa haɗuwa da mutane da suka gaya maka cewa ko da yake ba su gaskata da mu ba, suna yaba mana don aikin da muke yi. Yesu ya annabta cewa za a yi wa’azin bishara a dukan duniya. (Mat. 24:14) Amma, ta yaya muka san cewa wa’azin bishara da muke yi yana cika annabcin da Yesu ya yi? Shin gaskiya ne cewa mu kaɗai ne muke yin wannan wa’azin bishara?

2 Rukunin addinai da yawa suna da’awa cewa suna wa’azin bishara. Amma, abin da suke yi kawai shi ne su ba da labarin abin da ya faru da su ko su yi hidimomin coci ko kuma su yaɗa shirye-shiryen coci ta ƙofofin yaɗa labarai kamar talabijin ko kuma Intane. Wasu kuma sun ce ayyukan agaji da suke yi ko kuma abubuwan da suka cim ma a fannonin kiwon lafiya da ilimi daidai ne da yin wa’azin bishara. Amma, shin waɗannan ayyuka ne Yesu ya umurci almajiransa su yi?

3. Bisa ga Matta 28:19, 20, wane abubuwa huɗu ne ya kamata mabiyan Yesu su yi?

3 Shin almajiran Yesu za su jira mutane su zo su same su ne? A’a! Bayan ya tashi daga mutuwa, Yesu ya yi magana da ɗarurruwan almajiransa kuma ya ce: ‘Ku tafi fa, ku almajirtar da dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma, . . . kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.’ (Mat. 28:19, 20) Suna bukatar su yi abubuwa huɗu. Wajibi ne su yi almajirai, su yi musu baftisma kuma su koyar da su. Amma mene ne mataki na farko da za su ɗauka? Yesu ya ce: “Ku tafi”! Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hakkin kowane mai bi ne ya ‘tafi’ ya yi wa’azi ko da a ƙetaren titi ko kuma a hayin teku.”—Mat. 10:7; Luk. 10:3.

4. Mene ne zama “masuntan mutane” ya ƙunsa?

4 Mene ne Yesu yake son almajiransa su yi? Shin yana so su yi wa’azi da kansu ne ko kuma yana so su yi wa’azin bishara a matsayinsu na rukuni? Tun da yake mutum ɗaya ba zai iya yin wa’azi ga “dukan al’ummai” ba, hakan zai bukaci mutane da yawa. Abin da Yesu yake nufi ke nan sa’ad da ya gaya wa almajiransa cewa za su zama “masuntan mutane.” (Karanta Matta 4:18-22.) Kamun kifi da Yesu yake nufi a nan ba wanda mutum ɗaya zai sa tāna a cikin ƙugiya kuma ya jefa a cikin kogi yana jiran kifin da zai ci ba. Maimakon haka, yana nufin yin amfani da taru kuma hakan zai ƙunshi tsari da kuma mutane da yawa masu aiki da haɗin kai.—Luk. 5:1-11.

5. Waɗanne tambayoyi huɗu ne ake bukatar a san amsoshinsu, kuma me ya sa?

5 Don mu san waɗanda suke cika annabcin Yesu a yau ta wajen yin wa’azin bishara, muna bukatar mu amsa tambayoyi huɗu na gaba:

  • Mene ne ya kamata mu yi wa’azi a kai?

  • Me ya sa muke wa’azin bishara?

  • Waɗanne hanyoyi ne ya kamata a bi wajen yin wa’azin bishara?

  • A waɗanne wurare ne za mu yi wa’azin bishara kuma har yaushe?

Amsoshin waɗannan tambayoyin za su taimaka mana mu san waɗanda suke yin wannan aikin da ke sa a ceci mutane kuma zai ƙarfafa mu mu ci gaba da yin wa’azin bishara.—1 Tim. 4:16.

MENE NE YA KAMATA MU YI WA’AZI A KAI?

6. Me ya sa ka tabbata cewa Shaidun Jehobah ne suke wa’azin bisharar Mulki?

6 Karanta Luka 4:43. Yesu ya yi wa’azin ‘bishara ta Mulki’ kuma ya umurci almajiransa su yi hakan. Wane rukunin mutane ne suke wa’azin bishara ga “dukan al’ummai”? Babu shakka, Shaidun Jehobah ne. Har wasu masu hamayya da mu sun san cewa mu ne muke wa’azin bishara. Alal misali, wani firist mai hidima a ƙasashen waje ya taɓa gaya wa wani Mashaidi cewa ya zauna a ƙasashe dabam-dabam kuma a duk inda ya je, ya tambayi Shaidun Jehobah abin da suke wa’azi a kai. Wace amsa suka ba shi? Firist ɗin ya ce: “Sakarkarin sun ba ni amsa iri ɗaya: ‘Bisharar Mulki.’” Amma, waɗannan Shaidun ba “sakarkari” ba ne, sun faɗi hakan ne don suna da haɗin kai kuma abin da ya kamata Kiristoci na gaskiya su yi ke nan. (1 Kor. 1:10) Ƙari ga haka, Mulkin Allah ne ainihin jigon Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah. Ana wallafa wannan mujallar a cikin harsuna 254 kuma a kowace fitowa, ana buga kusan kofi miliyan 59. Wannan ita ce mujallar da aka fi rarrabawa a dukan duniya.

7. Ta yaya muka san cewa limaman Kiristendam ba sa wa’azin bishara Mulki?

7 Limaman Kiristendam ba sa wa’azi game da Mulkin Allah. Idan ma suka ambaci Mulkin, sukan ce yana nufin yadda mutum yake ji ko kuma wani irin yanayi ne a zuciyar Kirista. Ba sa koya wa mutane cewa Mulkin gwamnati ce a sama kuma Yesu Kristi ne Sarkin. Ba sa gaya wa mutane cewa Mulkin ne zai magance dukan matsalolin ’yan Adam kuma ba da daɗe wa ba zai kawar da dukan mugunta. (R. Yoh. 19:11-21) Maimakon haka, sun fi so su tuna da Yesu a lokacin Kirsimati da kuma Ista. Ba su san abin da Yesu zai cim ma a matsayinsa na sabon Sarkin duniya ba. Tun da yake ba su san saƙon da ya kamata su yi wa’azinsa ba, ba abin mamaki ba ne cewa ba su san dalilin da ya sa ya kamata su yi wa’azin bishara ba.

ME YA SA MUKE YIN WA’AZIN BISHARA?

8. Wane ra’ayi game da yin wa’azin bishara ne bai dace ba?

8 Me sa ya kamata mu yi wa’azin bishara? Bai kamata a yi wa’azi don neman kuɗi da kuma gina manyan gidaje ba. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Kyauta kuka karɓa, sai ku bayar kyauta.” (Mat. 10:8) Bai kamata a mai da wa’azin bishara sana’ar neman kuɗi ba. (2 Kor. 2:17) Saboda haka, bai dace masu wa’azin bishara su riƙa yin haka don su amfani kansu ba. (Karanta A. M. 20:33-35.) Duk da cewa an ba da wannan umurnin, yawancin coci-coci sun mai da hankali ga tara kuɗi don su biya limamansu da kuma ma’aikatansu masu dumbin yawa. Saboda haka, shugabanan Kiristendam sun tara kuɗi ba kaɗan ba.—R. Yoh. 17:4, 5.

9. Me ya sa Shaidun Jehobah suke wa’azin bishara?

9 Ta yaya ake tallafa wa aikin Shaidun Jehobah? Ana tallafa wa aikinsu da gudummawar da ake bayarwa da son rai. (2 Kor. 9:7) Ba a yawo da faranti don karɓan kuɗi a Majami’un Mulki ko a wuraren manyan taronsu. Duk da haka, a shekarar da ta shige, Shaidun Jehobah sun yi amfani da sa’o’i kusan biliyan biyu wajen yin wa’azin bishara kuma sun gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki fiye da miliyan tara a kowane wata. Sun yi hakan ba tare da karɓan ko sisi ba. Abin mamaki shi ne ba a biyan su, a maimakon haka, da farin ciki suna biyan bukatunsu da kansu. Sa’ad da wani mai bincike ke magana game da aikin da Shaidun Jehobah suke yi, ya ce: “Ainihin dalilin da ya sa suke wannan aikin shi ne don wa’azi da kuma koyarwa. . . . Da yake ba su da limamai, hakan ya rage kuɗin da suke kashewa sosai.” Me ya sa muke wa’azin bishara? Muna yin wannan aikin da son rai domin muna ƙaunar Jehobah da kuma maƙwabtanmu. Hakan ya jitu da annabcin da ke littafin Zabura 110:3. (Karanta.)

A WAƊANNE HANYOYI NE YA KAMATA A YI WA’AZIN BISHARA?

Muna zuwa duk inda mutane suke don mu yi musu wa’azi (Ka duba sakin layi na 10)

10. Ta waɗanne hanyoyi ne Yesu da almajiransa suka yi wa’azin bishara?

10 A waɗanne hanyoyi ne Yesu da almajiransa suka yi wa’azin bishara? Sun je gidajen mutane da kuma wasu wuraren da jama’a suke zuwa don su yi musu wa’azin bishara. Muna bin gida-gida don mu yi wa’azin bishara ga waɗanda suke son su saurari saƙonmu. (Mat. 10:11; Luk. 8:1; A. M. 5:42; 20:20) Wannan tsarin da muke bi yana taimaka mana mu yi wa’azin bishara ga dukan mutane ba tare da nuna son kai ba.

11, 12. Ta yaya wa’azin bishara da Shaidun Jehobah suke yi ya bambanta da na Kiristendam?

11 Shin coci-cocin Kiristendam suna yin wa’azin bishara kamar yadda Yesu ya yi? A yawancin lokaci, mabiyan suna barin yin wa’azi ga limamansu da yake suna karɓan albashi. A maimakon su zama “masunta mutane,” limaman Kiristendam sun gamsu kawai da ‘kifayen’ da sun riga sun kama, wato mambobin cocinsu. Hakika, a wasu lokatai wasu limamai sukan yi ƙoƙari su yi wa’azi. Alal misali, a farkon shekara ta 2001, Paparuma John Paul II ya rubuta wasiƙa kuma ya ce: “Shekaru da dama ina faɗa a kai a kai cewa ya kamata mabiyan coci su yi wa’azin bishara. Ina sake faɗan hakan yanzu cewa . . . Wajibi ne mu kasance da ƙwazo kamar Bulus wanda ya ce: ‘Kaitona fa in ban yi wa’azin bishara ba.’” Paparuma ya ci gaba da cewa bai kamata “a bar wa’azin bishara wa limamai kawai ba, wajibi ne dukan mabiyan Allah su ɗauki wannan hakkin.” Amma, mutane nawa ne suka bi wannan shawara?

12 Shaidun Jehobah kuma fa? Su kaɗai ne suke wa’azi cewa Yesu ya soma sarauta tun shekara ta 1914. Kamar yadda Yesu ya ba su umurni, sun ɗauki yin wa’azin bishara da muhimmanci sosai. (Mar. 13:10) Littafin nan Pillars of Faith—American Congregations and Their Partners ya ce: “Shaidun Jehobah sun ɗauki aikin wa’azi da muhimmanci fiye da kowane abu.” Yayin da take ƙaulin wani Mashaidi, mawallafiyar ta ci gaba da cewa: ‘Sa’ad da suka ga mutane cikin yunwa da kaɗaici da rashin lafiya, suna ƙoƙarin taimaka musu, . . .  amma ba su taɓa manta cewa ainihin aikinsu shi ne sanar da saƙon Allah game da ƙarshen duniya da ke tafe da kuma muhimmancin samun ceto.’ Shaidun Jehobah sun ci gaba da wa’azin bishara ta wajen bin tsarin da Yesu da almajiransa suka bi.

A WAƊANNE WURARE NE ZA A YI WA’AZI KUMA HAR YAUSHE?

13. A waɗanne wurare ne za a yi wa’azin bishara?

13 Yesu ya bayyana cewa za a yi wa’azin bishara har zuwa ‘iyakar duniya.’ (Mat. 24:14) Mutane daga ‘dukan al’ummai’ za su zama almajiransa. (Mat. 28:19, 20) Saboda haka, za a yi wannan wa’azin a dukan duniya.

14, 15. Mene ne ya nuna cewa Shaidun Jehobah sun cika annabcin da Yesu ya yi game da wuraren da za a yi wa’azin bishara? (Ka duba hotunan da ke shafi na 8.)

14 Bari mu yi la’akari da wasu bincike don mu fahimci yadda Shaidun Jehobah suke cika annabcin Yesu game da wuraren da za a yi wa’azin bishara. Adadin da aka samu a wani bincike ya nuna cewa akwai manyan malaman coci wajen 600,000 a rukunonin coci dabam-dabam a ƙasar Amirka, amma adadin Shaidun Jehobah da ke wa’azi a ƙasar ya kai miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu. A dukan duniya, adadin firistocin Cocin Katolika ya ɗara 400,000. Yanzu ka yi la’akari da yawan Shaidun da suke wa’azin bisharar Mulki. A dukan duniya, da akwai Shaidu wajen miliyan takwas da suke wa’azi a ƙasashe 240. Hakika, ba ƙaramin aiki ba ne ake yi a wa’azin bishara kuma hakan yana kawo yabo da kuma ɗaukaka ga Jehobah!—Zab. 34:1; 51:15.

15 A matsayinmu na Shaidun Jehobah, muna son mu yi wa mutane da yawa wa’azi kafin ƙarshen ya zo. Saboda haka, don mu cim ma wannan aikin, mun fassara da kuma wallafa miliyoyin littattafai da mujallu da warƙoƙi da kuma takardun gayyatar mutane zuwa manyan taro da taron Tuna da Mutuwar Yesu. Kuma muna rarraba wa mutane waɗannan littattafan kyauta. Mun wallafa littattafai dabam-dabam cikin harsuna fiye da 700. Ƙari ga haka, ana buga New World Translation of the Holy Scriptures fiye da kofi miliyan 200 cikin harsuna fiye da 130. A shekarar da ta shige, mun buga littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki biliyan huɗu da miliyan ɗari biyar. Ƙari ga haka, ana tanadar da littattafai a harsuna fiye da 750 a dandalinmu. Shin akwai wani rukunin addini da suke yin irin wannan aikin?

16. Ta yaya muka sani cewa Shaidun Jehobah suna da ruhun Allah?

16 Har yaushe ne za mu ci gaba da yin wannan wa’azin bishara da aka yi annabcinsa? Yesu ya annabta cewa za a ci gaba da yin wannan aikin a duniya har zuwa kwanaki na ƙarshe, “sa’annan matuƙa za ta zo.” (Mat. 24:14) Wane rukunin addini ne suka ci gaba da yin wa’azin bishara a waɗannan muhimman kwanaki na ƙarshe? Wasu da muke haɗuwa da su sa’ad da muke wa’azi suna cewa: “Mu ne muke da ruhu mai tsarki, amma ku ne kuke yin aikin; ku ne masu yin wa’azin bishara.” Da yake mu ne muka nace da yin wannan aikin, hakan ya nuna cewa muna da ruhu mai tsarki. (A. M. 1:8; 1 Bit. 4:14) A wasu lokatai, wasu rukunin addinai sun gwada yin abin da Shaidun Jehobah suka saba yi, amma haƙar su ba ta cim ma ruwa ba. Wasu suna yin aikin wa’azi a ƙasashen waje na ɗan lokaci sa’an nan su koma ga harkokinsu na yau da kullum. Wasu kuma suna iya zuwa gidajen mutane, amma ba sa wa’azi game da Mulkin Allah. Hakan ya nuna cewa ba sa yin aikin da Kristi ya yi.

SU WANE NE AINIHI SUKE YIN WA’AZIN BISHARA A YAU?

17, 18. (a) Me ya sa muke da tabbaci cewa Shaidun Jehobah ne suke wa’azin bisharar Mulki a yau? (b) Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da yin wa’azin bishara?

17 Su waye ne ainihi suke wa’azin bisharar Mulki a yau? Muna da tabbaci cewa “Shaidun Jehobah” ne suke yi wannan aikin. Me ya sa muka ce hakan? Domin mu ne ke wa’azin bisharar Mulkin. Da yake muna zuwa gidajen mutane da kuma inda jama’a suke don mu yi musu wa’azi, hakan na nuna cewa muna bin hanyoyin da suka dace wajen yin wannan wa’azin bishara. Muna da kyakkyawan dalili na yin wannan wa’azin bishara, wato muna yin hakan don muna ƙaunar Jehobah ba don kuɗi ba. Ƙari ga haka, muna yin wannan wa’azin bishara a ko’ina a duniya, kuma muna yin hakan ga dukan al’ummai da kuma harsuna. Za mu ci gaba da yin wannan wa’azin babu fashi, har sai ƙarshen ya zo.

18 Hakika, abin da mutanen Allah suke cim mawa a waɗannan muhimman kwanaki na ƙarshe yana da ban mamaki. Ta yaya ake cim ma dukan waɗannan abubuwa? Manzo Bulus ya ba da amsar a wasiƙarsa zuwa ga Filibiyawa: “Allah ne yana aiki a cikinku da za ku yi nufi har ku aika kuma, zuwa abin da ya gamshe shi.” (Filib. 2:13) Babu shakka, Jehobah zai ci gaba da ƙarfafa mu yayin da muke yin iya ƙoƙarinmu don mu yi wa’azin bishara.—2 Tim. 4:5.