Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Nuna Godiya don Alherin Allah

Ka Nuna Godiya don Alherin Allah

‘Mu duka mun karɓi alheri . . . biye da alheri.’YOH. 1:16.

WAƘOƘI: 95, 13

1, 2. (a) Ka bayyana kwatancin mai gonar inabi. (b) Ta yaya kwatancin ya nanata halin karimci da alheri?

WATA rana da safe, wani mai gonar inabi ya je kasuwa don ya nemi mutanen da za su yi aiki a gonarsa. Mutanen da ya samu sun amince da yawan kuɗin da ya ce zai biya su kuma suka soma aiki a gonar. Da yake mai gonar yana bukatar ƙarin ma’aikata, sai ya koma kasuwa kuma ya ci gaba da neman ma’aikata har kusan yamma. Ya gaya wa duk ma’aikacin da ya samu cewa zai biya shi hakkinsa. Sa’ad da yamma ta yi, sai ya tara dukan ma’aikatan don ya biya su hakkinsu. Kuɗin da ya biya waɗanda suka soma aiki da safe ɗaya ne da na waɗanda suka soma aiki kusan da yamma. Sa’ad da waɗanda suka soma aikin tun da safe suka ga haka, sai suka soma gunaguni. Mai gonar inabin ya tambaye su: ‘Ba kun amince da yawan kuɗin da na ce zan biya ku ba? Shin ba ni da izinin biyan ma’aikatana abin da na ga dama? Ko kuna kishi ne don karimci da na nuna?’—Mat. 20:1-15.

2 Wannan kwatancin Yesu ya tuna mana da wani halin Jehobah da ake yawan ambatawa a cikin Littafi Mai Tsarki, wato “alheri.” (Karanta 2 Korintiyawa 6:1.) Kamar dai ma’aikatan da suka yi sa’a ɗaya kawai ba su cancanci a ba su kuɗin yini ba, amma mai gonar inabin ya nuna musu alheri ba kaɗan ba. Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya bayyana ma’anar kalmar nan “alheri” cewa: “Wannan kalmar tana nufin kyautar wani abu da aka ba wa mutumin da bai cancanci a ba shi kyautar ba.”

KYAUTAR JEHOBAH DA BA TA MISALTUWA

3, 4. Me ya sa Jehobah ya nuna alheri ga dukan ’yan Adam kuma ta yaya ya yi hakan?

3 Littafi Mai Tsarki ya ce “alheri na Allah” kyauta ce. (Afis. 3:7) Me ya sa Jehobah ya ba mu wannan “kyautar”? Ba mu cancanci samun alherin Allah ba domin mu ajizai ne. Shi ya sa Sarki Sulemanu ya ce: “Babu wani mai-adalci ko ɗaya cikin duniya, wanda yana aika nagarta, ba tare da zunubi ba.” (M. Wa. 7:20) Hakazalika, manzo Bulus ya rubuta cewa: “Dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” Ƙari ga haka, “hakkin zunubi mutuwa ne.” (Rom. 3:23; 6:23a)

4 Amma Jehobah ya nuna ƙaunarsa ga ’yan Adam masu zunubi a wata hanya mai ban al’ajabi. Ya aiko “Ɗansa, haifaffe shi kaɗai,” don ya ba da ransa a madadinmu. (Yoh. 3:16) Manzo Bulus ya rubuta cewa an naɗa Yesu “da daraja da girma, domin bisa ga alherin Allah ya ɗanɗana mutuwa sabili da kowane mutum.” (Ibran. 2:9) Saboda haka, “kyautar Allah rai na har abada ce cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.”—Rom. 6:23b.

5, 6. Mene ne sakamakon barin (a) zunubi ya mallake mu? (b) alherin Allah ya mallake mu?

5 Ta yaya ’yan Adam suka gāji zunubi da kuma mutuwa da ke addabar dukanmu? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ta wurin mutum ɗaya . . . mutuwa ta mallaki” dukan ’yan Adam. (Rom. 5:12, 14, 17) Abin farin ciki shi ne, muna da zaɓi. Za mu iya yanke shawara cewa ba za mu ci gaba da barin zunubi ya mallake mu ba. Idan muka yi imani da fansar Kristi, hakan zai sa alherin Allah ya mallake mu. Ta yaya? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Inda zunubi ya yawaita, alheri ya daɗa yawaita ƙwarai da gaske: domin, kamar yadda zunubi ya ja-goranci zuwa mutuwa, haka nan kuma alheri zai kai ga adalci zuwa rai na har abada ta wurin Yesu Kristi.”—Rom. 5:20, 21.

6 Ko da yake mu masu zunubi ne, bai kamata mu bar zunubi ya mallake mu ba. Idan muka yi zunubi, za mu roƙi Jehobah ya yi mana gafara. Manzo Bulus ya yi wa Kiristoci gargaɗi cewa: “Zunubi ba za ya sami mulki bisa kanku ba: gama ba ƙarƙashin shari’a kuke ba, amma ƙarƙashin alheri.” (Rom. 6:14) Mene ne hakan yake nufi? Bulus ya bayyana cewa: “Alherin Allah . . . yana koya mana, da nufin mu rayu da hankali da adalci da ibada cikin wannan zamani na yanzu, yayin da muna ƙin rashin ibada da sha’awoyi na duniya.”—Tit. 2:11, 12.

ALLAH YA YI MANA ALHERI A HANYOYI DABAM-DABAM

7, 8. Mene ne ake nufi da cewa Jehobah yana nuna mana alherinsa a hanyoyi dabam-dabam? (Ka duba hoton da ke shafi na 21.)

7 Manzo Bitrus ya rubuta cewa: “Yayin da kowa ya karɓi baiko, kuna yi ma junanku hidima da shi, kamar nagargarun wakilai na alherin Allah iri iri masu-yawa.” (1 Bit. 4:10) Shin mene ne hakan yake nufi? Hakan yana nufin cewa Jehobah yana taimaka mana mu jimre duk wani gwajin da muke fuskanta a rayuwa. (1 Bit. 1:6) Kuma zai ci gaba da tanadar mana da daidai abin da muke bukata don mu jimre da gwajin.

8 Hakika, Jehobah yana nuna mana alheri a hanyoyi dabam-dabam. Manzo Yohanna ya ce: “Mu duka muka karɓa, alheri kuma yana biye da alheri.” (Yoh. 1:16) Mene ne sakamakon haka? Muna samun albarka masu yawa. Waɗanne albarka ke nan?

9. Ta yaya muke amfana daga alherin Jehobah, kuma a wace hanya ce za mu nuna godiyarmu saboda haka?

9 Jehobah yana gafarta mana zunubanmu. Idan muka tuba kuma muka ci gaba da yin ƙoƙari mu daina yin zunubi, Jehobah zai gafarta mana zunubanmu saboda alherinsa. (Karanta 1 Yohanna 1:8, 9.) Hakika, Allah ya nuna mana jin ƙai. Ya kamata mu riƙa yi masa godiya kuma mu ɗaukaka shi. Sa’ad da Bulus yake rubuta wasiƙa ga ’yan’uwansa shafaffu, ya ce: “Ya tsame mu daga cikin ikon duhu, ya maishe mu zuwa cikin mulkin Ɗa na ƙaunarsa; wanda muke da fansarmu a cikinsa, watau gafarar zunubanmu.” (Kol. 1:13, 14) Allah ya gafarta mana zunubanmu kuma hakan ya ba mu damar morar abubuwa da yawa.

10. Wane gata ne muke da shi saboda alherin Allah?

10 Muna da salama da kuma dangantaka mai kyau da Allah. Da yake mu masu zunubi ne, hakan ya mai da mu maƙiyan Allah daga ranar da aka haife mu. Bulus ya ambaci hakan sa’ad da ya ce: “Tun muna maƙiya muka sulhuntu da Allah ta wurin mutuwar Ɗansa.” (Rom. 5:10) Wannan sulhu da Allah ya yi da mu ya sa mun sami salama da kuma dagantaka mai kyau da shi. Bulus ya bayyana cewa hakan wata hanya ce da Jehobah ya nuna mana alheri. Ya ce: “Bari mu [’yan’uwan Kristi shafaffu mu] kasance da salama wurin Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kristi; wanda mun sami yardan shiga ta wurinsa bisa bangaskiya zuwa cikin wannan alheri inda muke tsayawa.” (Rom. 5:1, 2) Babban gata ne cewa muna da salama kuma muna da dangantaka mai kyau da Jehobah!

Hanyoyi da Allah ya nuna mana alheri: Gatan jin bishara (Ka duba sakin layi na 11)

11. Ta yaya shafaffu suke sa “waɗansu tumaki” su kasance da adalci a gaban Allah?

11 Za mu iya kasancewa da adalci a gaban Allah. Dukanmu marasa adalci ne a gaban Allah. Amma Daniyel ya annabta cewa a kwanaki na ƙarshe, “waɗanda ke da hikima,” wato shafaffu da suka rage a duniya za su ‘juya mutane da yawa zuwa adalci.’ (Karanta Daniyel 12:3.) Shafaffu sun sa miliyoyin “waɗansu tumaki” su kasance da adalci a gaban Jehobah ta wajen wa’azin bishara. (Yoh. 10:16) Amma, hakan ya yiwu ne saboda alherin Jehobah. Shi ya sa Bulus ya bayyana cewa: “Ta alherin da Allah ya yi musu kyauta sun sami kuɓuta ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi.”—Rom. 3:23, 24.

Gatan yin addu’a (Ka duba sakin layi na 12)

12. Ta yaya addu’a ta zama wata hanyar da Allah yake nuna mana alherinsa?

12 Za mu iya kusantar Allah ta wurin addu’a. Jehobah cikin alherinsa ya ba mu gatan yin addu’a. Manzo Bulus ya ce za mu iya kusantar Kursiyin Jehobah “da gaba gaɗi” don “kursiyi na alheri” ne. (Ibran. 4:16a) Jehobah ya ba mu wannan gatan ta wurin Ɗansa “wanda cikinsa muna da gaba gaɗi da daman isowa tare da amincewa ta wurin bangaskiyarmu gare shi.” (Afis. 3:12) Allah ya nuna mana alherinsa ta wajen ba mu gatan yin addu’a.

Samun taimako a lokacin da ya dace (Ka duba sakin layi na 13)

13. Ta yaya Allah yake ‘taimakon mu a kan kari’ saboda alherinsa?

13 Za mu iya samun taimako a lokacin da ya dace. Bulus ya ƙarfafa mu mu yi addu’a da gaba gaɗi “domin a yi mana jinƙai, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari.” (Ibran. 4:16b, Littafi Mai Tsarki) A duk lokacin da muke fama da gwaji ko kuma matsaloli a rayuwarmu, za mu iya roƙon Jehobah ya taimaka mana. A yawancin lokaci, Jehobah yana jin addu’o’inmu duk da cewa mu ajizai ne, kuma yana amsa addu’o’inmu ta hanyar ’yan’uwanmu Kiristoci. Saboda haka, za mu iya kasancewa da “gaba gaɗi muna cewa, Ubangiji mai-taimakona ne; ba zan ji tsoro ba: Ina abin da mutum zai mini?”—Ibraniyawa 13:6.

14. Ta yaya alherin Jehobah yake sa mu kasance da kwanciyar hankali?

14 Muna samun ƙarfafawa don mu kasance da kwanciyar hankali. Allah yana ƙarfafa mu sa’ad da muke baƙin ciki, kuma muna samun wannan albarkar domin alherinsa. (Zab. 51:17) Sa’ad Kiristoci da ke Tasalonika suke fuskantar tsanantawa, Bulus ya rubuta musu wasiƙa cewa: “Ubangijinmu Yesu Kristi da kansa, da Allah Ubanmu wanda ya ƙaunace mu, ya ba mu ta’aziya madawwamiya kuma da nagarin bege ta wurin alheri, shi ta’azantar da zukantanku ya ƙarfafa.” (2 Tas. 2:16, 17) Sanin cewa Jehobah yana ƙarfafa mu saboda alherinsa abin farin ciki ne.

15. Wane bege ne muke da shi saboda alherin Allah?

15 Muna da begen yin rayuwa har abada. Idan Jehobah bai taimaka mana ba da yake mu masu zunubi ne, ba za mu kasance da wannan bege ba. (Karanta Zabura 49:7, 8.) Amma Jehobah ya tanadar mana da bege. Yesu ya yi wa mabiyansa alkawari cewa: “Gama nufin Ubana ke nan, kowane mutum wanda ya duba Ɗan, yana ba da gaskiya gare shi kuma, shi sami rai na har abada: ni ma in tashe shi rana ta ƙarshe.” (Yoh. 6:40) Hakika, begen rai na har abada kyauta ce da kuma alheri daga wurin Allah. Bulus ya nuna godiya saboda wannan alherin kuma ya ce: “Alherin Allah ya bayyana, mai-kawo ceto ga dukan mutane.”—Tit. 2:11.

KADA KA YI WASA DA ALHERIN ALLAH

16. Ta yaya wasu Kiristoci a ƙarni na farko suka yi wasa da alherin Allah?

16 Alherin Jehobah ya sa muna jin daɗin abubuwa da yawa. Amma bai kamata mu riƙa yin abubuwan da muka ga dama ko kuma mu riƙa yin zunubi ba. Wasu Kiristoci a ƙarni na farko sun yi ƙoƙarin mai da “alherin Allah zuwa wajen lalata.” (Yahu. 4) Waɗannan Kiristocin sun ɗauka cewa za su iya yin zunubi da gangan kuma su roƙi Jehobah ya gafarta musu. Ƙari ga haka, sun yi ƙoƙarin rinjayar wasu ’yan’uwa su bi halayensu. A yau, duk wanda ya yi hakan “ya rena ruhu na alheri.”—Ibran. 10:29.

17. Wane gargaɗi ne Bitrus ya bayar?

17 A yau, Shaiɗan ya yaudari wasu Kiristoci su ɗauka cewa za su iya yin zunubi da gangan kuma Jehobah ya gafarta musu saboda alherinsa. Ko da yake, Jehobah yana gafarta wa waɗanda suka tuba da gaske, amma yana so mu riƙa aiki tuƙuru don mu guji yin zunubi. Ta hanyar ruhu mai tsarki, Bitrus ya ce: “Ku fa, ƙaunatattu, domin kun rigaya kun sani, ku yi hankali kada ya zama a janye ku bisa ga kuskure na masu-mugunta, har ku fāɗi daga cikin tsayawarku. Amma ku yi girma cikin alherin Ubangijinmu Mai-cetonmu Yesu Kristi.”—2 Bit. 3:17, 18.

WAJIBI NE MU YI WASU AYYUKA DON MU SAMI ALHERIN ALLAH

18. Wane hakki ne muke da shi saboda alherin da Allah ya nuna mana?

18 Muna bukatar mu yi godiya ga Allah saboda alherinsa. Saboda haka, ya kamata mu yi amfani da baiwarmu don mu ɗaukaka Jehobah kuma mu taimaka wa mutane. Ta yaya? Bulus ya ce: “Da yake fa muna da bayebaye dabam dabam, gwargwadon alherin da aka ba mu, . . . ko hidima, mu yi tattalin hidimarmu; wanda yake koyarwa, shi maida hankali ga koyarwarsa, wanda yake gargaɗi, ga gargaɗinsa . . . wanda ya nuna jinƙai, sai da fara’a.” (Rom. 12:6-8) Alherin da Jehobah ya nuna mana ya sa ya zama wajibi mu yi wa’azin bishara da ƙwazo, mu koya wa mutane gaskiyar Littafi Mai Tsarki, mu ƙarfafa ’yan’uwanmu Kiristoci, kuma mu gafarta wa duk wanda ya ɓata mana rai.

19. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

19 Da yake Jehobah ya nuna mana alheri a hanyoyi dabam-dabam, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu yi wa’azin “bishara ta alherin Allah.” (A. M. 20:24) Za mu tattauna yadda za mu yi hakan a talifi na gaba.