Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Tufafinka Suna Daukaka Allah Kuwa?

Tufafinka Suna Daukaka Allah Kuwa?

“Ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.”—1 KOR. 10:31, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 34, 61

1, 2. Me ya sa Shaidun Jehobah suke bin ƙa’idodi masu kyau a batun saka tufafi? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

WATA jarida da aka rubuta da yaren Dutch ta kwatanta irin shigar da shugabanan addinai suka yi a wani taronsu. Ta ce: “Mutane da yawa suna saka tufafin da ba su dace ba, musamman ma sa’ad da ake zafi sosai. Amma ba za ka ga irin wannan shigar a taron Shaidun Jehobah ba. . . . Yara maza da manya suna saka kwat da taye, ’yammata kuma suna saka siket na zamani da ya dace.” Hakika, ana yaba wa Shaidun Jehobah don suna saka “tufafin da ya dace da . . . masu bayyana shaidar ibada” ga Allah. (1 Tim. 2:9, 10, LMT) Manzo Bulus yana magana game da tufafin da ya kamata mata su riƙa sakawa, amma wannan ƙa’idar ta shafi maza ma.

2 A matsayinmu na masu bauta wa Jehobah, saka tufafin da suka dace yana da muhimmanci a gare mu da kuma Allah. (Far. 3:21) Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da tufafi da ado ya nuna cewa Jehobah yana da ƙa’idodin da ya kafa game da irin shigar da masu bauta masa za su yi. Saboda haka, bai kamata mu riƙa saka tufafi ko kuma adon da za su faranta mana rai kawai ba. Ya kamata mu yi la’akari da abin da Jehobah yake so.

3. Mece ce Dokar da Allah ya ba Isra’ilawa ta koya mana game da saka tufafi?

3 Alal misali, a dokar da aka ba da ta hannun Musa, an ba da dokokin da suka kāre Isra’ilawa daga lalatan da al’ummai da ke kusa da su suke yi. Dokar ta nuna cewa Jehobah ya tsani tufafin da ba sa nuna bambancin da ke tsakanin namiji da tamace, amma irin tufafin da ake yayinsu ke nan a yau. (Karanta Kubawar Shari’a 22:5.) Abin da Allah ya faɗa game da tufafi ya nuna cewa ba ya son tufafin da ke sa maza su zama kamar mata ko wanda ke sa mata su zama kamar maza. Ƙari ga haka, ba ya so mu riƙa sa kayan da ba za a iya sanin bambanci tsakanin namiji da tamace ba.

4. Mene ne zai taimaka wa Kiristoci su tsai da shawarwari masu kyau a batun saka tufafi?

4 A cikin Kalmar Allah da akwai ƙa’idodin da za su taimaka wa Kiristoci su tsai da shawarwari masu kyau a batun saka tufafi. Waɗannan ƙa’idodin sun shafe mu a duk inda muke zama ko al’adarmu ko yadda yanayin ƙasarmu yake. Ba ma bukatar a gaya mana irin tufafin da suke da kyau ko marasa kyau. Maimakon hakan, ƙa’idodin da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu tsai da shawara mai kyau a kan irin shigar da muke so mu yi. Bari mu tattauna wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu san “nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma” sa’ad da muke so mu saka tufafi.—Rom. 12:1, 2, LMT.

MU NUNA CEWA MU MASU HIDIMAR ALLAH NE

5, 6. Ta yaya tufafinmu za su shafi wasu?

5 Ta wurin ja-gorar ruhu mai tsarki, manzo Bulus ya faɗi wani abu mai muhimmancin a cikin littafin 2 Korintiyawa 6:4. (Karanta.) Irin tufafin da muke sakawa suna nuna halayenmu. Mutane da yawa suna iya sanin halinmu ta wurin abin da suke gani muna sakawa. (1 Sam. 16:7) A matsayinmu na masu bauta wa Jehobah, mun fahimci cewa bai kamata mu saka tufafi kawai don shi ne abin da muke so mu saka ba. Bin ƙa’idodin da ke cikin Kalmar Allah zai taimaka mana mu guji saka tufafin da za su matse mu ko wanda zai nuna jikinmu ko kuma wanda zai iya sa ’yan’uwa su yi tunanin da bai dace ba. Wannan ya nuna cewa muna bukatar mu guji saka tufafin da ke nuna surar jikinmu. Hakika, ba za mu so mutane su riƙa kawar da idanunsu sa’ad da suka gan mu don tufafin da muka saka ba.

6 Idan muna da tsabta kuma muna saka tufafin da suka dace a matsayinmu na bayin Jehobah, hakan zai sa mutane su daraja mu sosai. Ƙari ga haka, zai sa su so Allahn da muke bauta wa da kuma daraja ƙungiyarsa. Tufafin da muke sakawa za su iya sa mutane su saurari wa’azin da muke yi.

7, 8. A wane lokaci ne musamman ya kamata mu yi shiga mai kyau?

7 Muna so mu riƙa saka tufafin da za su nuna cewa muna daraja Allahnmu da ’yan’uwanmu da kuma mutanen da muke yi wa wa’azi a yankinmu. Ƙari ga haka, tufafinmu suna daraja saƙon da muke gaya wa mutane da kuma ɗaukaka Jehobah. (Rom. 13:8-10) Muna bukatar mu riƙa saka tufafin da suka “dace ga [mutane] masu-shaidan ibada” musamman ma idan za mu halarci taro ko kuma za mu je wa’azi. (1 Tim. 2:10) Hakika, mutane suna da ra’ayoyi dabam-dabam game da irin tufafin da suka dace. Saboda haka, bayin Jehobah a dukan faɗin duniya suna bukatar su guji saka tufafin da suka saɓa wa al’adar wasu.

Tufafin da kake sakawa suna ɗaukaka Allah kuwa? (Ka duba sakin layi na 7, 8)

8 Karanta 1 Korintiyawa 10:31. Muna bukatar mu saka tufafi masu kyau idan za mu halarci manyan taro. Bai kamata mu yi shiga irin yadda mutanen duniya suke yi ba. Ko bayan taron ko kuma sa’ad da muke masauƙinmu, ya kamata mu saka tufafi masu kyau. Idan muka yi haka, za mu yi alfahari cewa mu Shaidun Jehobah ne. Kuma za mu iya yi wa mutane wa’azi a kowane lokaci.

9, 10. Me ya sa ya kamata mu yi la’akari da littafin Filibiyawa 2:4 sa’ad da muke tunanin irin tufafin da muke so mu saka?

9 Karanta Filibiyawa 2:4. Me ya sa yake da muhimmanci Kiristoci su riƙa yin la’akari da yadda tufafinsu za su shafi ’yan’uwa a cikin ikilisiya? Saboda muna iya ƙoƙarinmu don mu bi wannan ayar Littafi Mai Tsarki da ta ce: “Ku matar da gaɓaɓuwanku fa waɗanda ke a duniya; fasikanci, ƙazanta, kwaɗayi.” (Kol. 3:2, 5) Ba ma so mu yi wani abin da zai yi wa ’yan’uwa wuya su bi wannan shawarar Littafi Mai Tsarki. Wataƙila ’yan’uwa maza da mata da suka daina yin lalata har ila suna fama da wannan halin. (1 Kor. 6:9, 10) Hakika, ba za mu so mu zama sanadiyyar hana su daina wannan halin ba, ko ba haka ba?

10 Ya kamata tufafin da muke sakawa sa’ad da muke tare da ’yan’uwanmu su taimaka wajen sa ikilisiya ta kasance da tsabta. Kuma ya kamata mu yi hakan ko da muna wajen taro ko a’a. Muna da ’yancin zaɓan kayan da za mu saka, amma dukanmu muna bukatar mu saka tufafin da ba za su sa wasu su karya dokar Allah ba. (1 Bit. 1:15, 16) Mu tuna cewa ƙauna ta gaskiya “ba ta yin rashin hankali, ba ta biɗa ma kanta.”—1 Kor. 13:4, 5.

TUFAFIN DA SUKA DACE

11, 12. Me ya kamata mu yi la’akari da shi sa’ad da muke tunanin kayan da za mu saka?

11 Bayin Allah suna bukatar su tuna cewa “akwai lokacin kowane nufi da kowane aiki” sa’ad da suke tunani game da tufafin da za su saka. (M. Wa. 3:1, 17) Hakika, sauyin yanayi dabam-dabam yakan shafi tufafin da muke sakawa. Amma ƙa’idodin da Jehobah ya ƙafa ba sa canjawa.—Mal. 3:6.

12 A lokacin zafi, yakan yi wuya mu saka tufafin da suka dace. Saboda haka, ’yan’uwanmu suna farin ciki idan mun guji saka tufafin da suka matse mu ko kuma da suke nuna siffar jikinmu. (Ayu. 31:1) Ƙari ga haka, yana da kyau mu saka kayan yin iyo da suka dace a lokacin da muke hutawa a bakin teku ko kuma muke iyo. (Mis. 11:2, 20) Ko idan mutane da yawa a duniya suna saka kayan yin iyo da ke nuna siffar jikinsu, a matsayinmu na bayin Jehobah, ya kamata mu riƙa damuwa da abin da zai sa a yabi Jehobah.

13. Me ya sa ƙa’idar da ke cikin littafin 1 Korintiyawa 10:32, 33 ta shafi kayan da muke sakawa?

13 Wata ƙa’ida mai muhimmanci da za ta taimaka mana mu riƙa saka kayan da suka dace ita ce yin la’akari da yadda kayanmu za su shafi lamirin mutane. (Karanta 1 Korintiyawa 10:32, 33.) Ya kamata mu guji saka kayan da za su ɓata wa mutane rai. Manzo Bulus ya ce: “Bari kowanenmu ya gami ɗan’uwansa wajen abin da ke nagari, zuwa ginawa.” Bulus ya faɗi dalilin da ya sa ya ce hakan, ya ce: “Kristi kuma bai yi son kai ba.” (Rom. 15:2, 3) Hakika, Yesu ya fi mai da hankali ga yin nufin Allah da kuma taimaka wa mutane. Saboda haka, ya kamata mu guji saka kayan da muke so da za su hana mutane su saurari saƙonmu.

14. Ta yaya iyaye za su koya wa yaransu su ɗaukaka Allah ta irin tufafin da suke sakawa?

14 Iyaye suna da hakkin koya wa yaransu su bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Suna bukatar su tabbatar da cewa su da yaransu suna ƙoƙari su sa Allah farin ciki ta irin adon da suke yi da kuma kayan da suke sakawa. (Mis. 22:6; 27:11) Idan iyaye suka kafa wa yaransu misalin da ya dace da kuma ba su shawara da gargaɗi masu kyau, hakan zai sa yaran su riƙa daraja Allah. Yana da kyau iyaye su gaya wa yaransu wuri da kuma yadda za su samu tufafin da ya dace! Hakan yana nufin cewa ba kawai kayan da suke so za su saka ba amma da wanda zai iya sa su gaya wa mutane game da Jehobah Allah.

KA YI AMFANI DA ’YANCINKA DA KYAU

15. Mene ne zai taimaka mana mu riƙa saka kayan da suka dace?

15 Kalmar Allah tana yi mana ja-gora don mu yi zaɓi mai kyau da zai ɗaukaka Allah. Duk da haka, mu ne za mu zaɓi tufafin da muke so mu saka. Hakika, tufafin da muke so da kuma wanda za mu iya saya sun bambanta da na wasu mutane. Amma ya kamata kayanmu su kasance da tsabta kuma su dace da kowane yanayi. Ƙari ga haka, su zama waɗanda ake sakawa a wurin da muke zama.

16. Me ya sa ya kamata mu riƙa saka tufafin da suka dace?

16 Ba a kowane lokaci ba ne yake da sauƙi a sami kayan da suka dace, domin kayan yayi ne kawai kantuna da yawa suke sayarwa. Saboda haka, zai ɗauki lokaci kuma kuna bukatar ku ƙoƙarta kafin ku sami siketi da riga da kwat da kuma wandon da ba zai matse ku ainun ba. Duk da haka, ’yan’uwanmu za su lura kuma su yi farin ciki da yadda muke ƙoƙartawa don mu saka kaya masu kyau da suka dace. Ƙari ga haka, za mu sami albarka domin sadaukarwar da muka yi don mu ɗaukaka Ubanmu na sama ta wurin saka tufafin da suka dace.

17. Waɗanne irin yanayi ne za su sa ɗan’uwa ya bar gemu ko kuma a’a?

17 Shin ya dace ’yan’uwa maza su bar gemu? Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta bukaci maza su riƙa barin gemu. Amma, Kiristoci ba sa bin Dokar Musa kuma ba a tilasta musu su yi hakan. (Lev. 19:27; 21:5; Gal. 3:24, 25) A wasu al’adu, ana amincewa da gemun da aka gyara da kyau, kuma hakan ba zai hana mutane saurarar saƙonmu ba. Ƙari ga haka, wasu ’yan’uwa maza da aka naɗa suna barin gemu. Amma, wasu suna iya tsai da shawarar ba za su yi hakan ba. (1 Kor. 8:9, 13; 10:32) A wasu yankuna da kuma al’adu, ba a barin gemu kuma ba shi da kyau masu wa’azi su riƙa barinsa. Hakika, a irin waɗannan wuraren, barin gemu zai hana ɗan’uwa ɗaukaka Allah kuma zai sa ba za a ɗauke shi da mutunci ba.—Rom. 15:1-3; 1 Tim. 3:2, 7.

18, 19. Ta yaya littafin Mikah 6:8 za ta taimaka mana wajen saka tufafin da za su faranta wa Allah rai?

18 Muna godiya cewa Jehobah bai tsara mana ƙa’idodin da za mu riƙa bi game da tufafi da kuma adonmu ba. Maimakon haka, ya ba mu ’yancin yanke shawarwarin da suka yi daidai da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, ko a batun saka tufafi da kuma yin ado, za mu iya nuna cewa muna so mu ‘yi tafiya da tawali’u tare da Allahnmu.’—Mi. 6:8.

19 Kasancewa masu tawali’u zai sa mu ga cewa Jehobah yana da tsarki, kuma ƙa’idodinsa ne za su fi taimaka mana. Hakan ya ƙunshi daraja yadda mutane suke ji da kuma yin la’akari da ra’ayinsu. Saboda haka, muna ‘tafiya da tawali’u da Allah’ idan muka yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodinsa kuma muna daraja ra’ayin mutane.

20. Mene ne tufafinmu ya kamata ya nuna wa mutane?

20 Ya kamata tufafinmu su nuna wa mutane cewa mu bayin Jehobah ne. Jehobah ya kafa ƙa’idodi kuma muna farin cikin bin waɗannan ƙa’idodin. Muna yaba wa ’yan’uwanmu maza da mata don irin shigen da suke yi, kuma hakan yana sa mutane su saurari wa’azin da muke yi. Ƙari ga haka, yana ɗaukaka da kuma sa Jehobah farin ciki. Idan muka ci gaba da saka tufafin da suka dace, za mu ɗaukaka wanda yake “da girma da ɗaukaka.”—Zab. 104:1, 2.