Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Karfafa Abotarku da Jehobah Sa’ad da Kuke Hidima a Inda Ake Wani Yare

Ku Karfafa Abotarku da Jehobah Sa’ad da Kuke Hidima a Inda Ake Wani Yare

“Na ɓoye maganarka cikin zuciyata.”​—ZAB. 119:11.

WAƘOƘI: 142, 92

1-3. (a) Mene ne ya kamata ya fi kasancewa da muhimmanci a gare mu? (b) Waɗanne ƙalubale ne waɗanda suke koyon wani yare suke fuskanta, kuma waɗanne tambayoyi ne za a tattauna? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

A YAU, Shaidun Jehobah da yawa suna cika wannan wahayin da ya ce, za a yi wa’azi “ga kowane iri da ƙabila da harshe da al’umma.” (R. Yoh. 14:⁠6) Kana cikin waɗanda suke koyon wani yare? Kana hidima a wata ƙasa ko kuma inda ake bukatar masu shela sosai? Ka soma halartan taro a ikilisiyar da ake wani yare a ƙasarku?

2 A matsayinmu na bayin Allah, dukanmu muna bukatar mu mai da hankali sosai ga dangantakarmu da kuma na iyalinmu da Jehobah. (Mat. 5:⁠3) A wasu lokatai, yawan ayyukan da muke da shi yakan sa ya yi mana wuya mu yi nazari sosai. Amma waɗanda suke hidima a inda ake wani yare suna fuskantar wasu ƙalubale.

3 Ban da koyon sabon yare, waɗanda suke hidima a inda ake wani yare suna bukatar su tabbata cewa suna nazarin Kalmar Allah a kai a kai da kuma binciken abubuwan da suke da wuyan ganewa. (1 Kor. 2:10) Ta yaya za su iya yin hakan idan ba su fahimci yaren da ake yi a cikin ikilisiya ba? Kuma me ya sa ya kamata iyaye su tabbata cewa Kalmar Allah tana ratsa zuciyar yaransu?

WANI ABU DA ZAI IYA ƁATA DANGANTAKARMU DA JEHOBAH

4. Mene ne zai iya ɓata dangantakarmu da Jehobah? Ka ba da misali.

4 Idan ba ma fahimtar Kalmar Allah a wani yare, hakan zai iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. A ƙarni na biyar kafin haihuwar Yesu, Nehemiya ya damu sosai sa’ad da ya ji cewa wasu yaran Yahudawa da suka dawo daga Babila ba su iya Ibrananci ba. (Karanta Nehemiya 13:​23, 24.) Saboda haka, dangantakar waɗannan yaran da Allah ta soma ɓacewa domin ba sa fahimtar Kalmar Allah.​—⁠Neh. 8:​2, 8.

5, 6. Mene ne wasu iyaye da suke hidima a inda ake wani yare suka lura da shi, kuma me ya sa?

5 Wasu iyayen da suke hidima a inda ake wani yare sun ga cewa dangantakar yaransu da Jehobah ba ta da ƙarfi kamar dā. Abin da ake koyarwa a Majami’ar Mulki ba ya ratsa zuciyar yaransu domin ba sa fahimtar abin da ake faɗa a taro. Pedro, [1] da ya ƙaura tare da iyalinsa daga Amirka ta Kudu zuwa Ostareliya ya ce: “Wajibi ne Kalmar Allah ta taɓa zuciyar mutum idan ana so ya yi amfani da ita.”​—⁠Luk. 24:⁠32.

6 Abin da muka karanta a wani yare ba zai ratsa zuciyarmu kamar wanda muka karanta a yarenmu ba. Ƙari ga haka, idan ba mu iya tattaunawa a wani yare ba, hakan yakan sa mu baƙin ciki kuma yana iya shafan ibadarmu ga Jehobah. Saboda haka, muna bukatar mu kāre dangantakarmu da Jehobah duk da cewa muna son mu bauta masa a ikilisiyar da ake wani yare.​—⁠Mat. 4:⁠4.

SUN KĀRE DANGANTAKARSU DA JEHOBAH

7. Ta yaya mutanen Babila suka yi ƙoƙari su tilasta wa Daniyel ya soma bin al’adarsu da kuma addininsu?

7 Sa’ad da aka kai Daniyel da abokansa zaman bauta, mutanen Babila sun tilasta musu su soma bin al’adarsu ta wajen koya musu yaren Chaldiyawa. Ƙari ga haka, wani ma’aikacin fadar da aka ba shi aikin horar da su ya ba su sunan mutanen Babila. (Dan. 1:​3-7) Sunan da aka ba wa Daniyel yana nufin Bel, wato ainihin sunan allan Babila. Wataƙila Sarki Nebuchadnezzar yana so ya nuna wa Daniyel cewa allan Babila ya fi ƙarfin Jehobah.​—⁠Dan. 4:⁠8.

8. Mene ne ya taimaka wa Daniyel ya ci gaba da ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah sa’ad da yake wata ƙasa?

8 Ko da yake an ba wa Daniyel abinci daga cikin wanda sarki da kansa yake ci, “ya yi ƙudiri a zuciyarsa” cewa ba zai “ɓata kansa” da abincin sarkin ba. (Dan. 1:⁠8) Ya ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah yayin da yake zama a wata ƙasa domin ya ci gaba da nazarin “littattafai” masu sarki a yarensa. (Dan. 9:⁠2) Saboda haka, har bayan shekaru 70 a Babila, an ci gaba da kiransa da sunansa na Ibrananci.​—⁠Dan. 5:⁠13.

9. Kamar yadda aka nuna a Zabura 119, yaya Kalmar Allah ta taimaka wa marubucin wannan zaburar?

9 Marubucin Zabura 119 ya jimre sa’ad da waɗanda suke fadar sarki suke masa ba’a. Kuma karanta Kalmar Allah ta ƙarfafa shi da kuma taimaka masa ya fita dabam da su. (Zab. 119:​23, 61) Ƙari ga haka, ya bar Kalmar Allah ta taɓa zuciyarsa sosai.​—⁠Karanta Zabura 119:​11, 46.

KU CI GABA DA ƘARFAFA DANGANTAKARKU DA JEHOBAH

10, 11. (a) Mene ne ya kamata ya zama burinmu yayin da muke nazarin Kalmar Allah? (b) Ta yaya za mu cim ma hakan? Ka ba da misali.

10 Ko da yake muna da ayyuka da hakki da yawa a ƙungiyar Jehobah, dukanmu muna bukatar mu keɓe lokaci don yin nazari na kanmu da kuma ibada ta iyali. (Afis. 5:​15, 16) Amma, bai kamata mu yi nazari don muna so mu karance shafuffuka da yawa ko kuma don kawai mu yi kalami a taro ba. Ya kamata mu tabbata cewa Kalmar Allah tana taɓa zuciyarmu da kuma ƙarfafa bangaskiyarmu.

11 Don mu cim ma hakan, ya kamata mu riƙa mai da hankali ga namu dangantakar da Jehobah sa’ad da muke nazari ba kawai na wasu mutane ba. (Filib. 1:​9, 10) Wajibi ne mu fahimci cewa sa’ad da muke shiri don fita wa’azi ko halartan taro ko kuma ba da jawabi, wataƙila ba za mu yi tunani a kan yadda hakan ya shafe mu ba. Alal misali: Ko da yake mai dafa abinci yakan ɗanɗana abin da ya dafa kafin ya ba wa mutane su ci, ɗanɗanawa kawai ba zai ƙosar da shi ba. Idan yana so ya kasance da koshin lafiya, ya kamata shi ma ya dafa wa kansa abinci mai gina jiki da zai ci. Hakazalika, yayin da muke taimaka wa mutane, ya kamata mu yi ƙoƙari mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai.

12, 13. Me ya sa ‘yan’uwa da yawa da suke hidima a inda ake wani yare suke nazari a kai a kai a yarensu?

12 ‘Yan’uwa da yawa da suke hidima a inda ake wani yare suna ganin cewa yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai a yarensu yana taimaka musu sosai. (A. M. 2:⁠8) Masu wa’azi a ƙasar waje ma sun fahimci cewa idan suna so su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah a inda suke hidima, wajibi ne su riƙa nazari a yarensu ba kawai su gamsu da abin da suke ji a taron ikilisiyarsu ba.

13 Alain, wanda ya yi shekara takwas yana koyon yaren Farisa ya ce: “Idan na shirya taro a yaren Farisa, nakan mai da hankali ga yaren kawai. Tun da yake ina son in koyi yaren, abin da nake karantawa ba ya ratsa zuciyata. Shi ya sa nake keɓe lokaci a kai a kai don na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma wasu littattafai a yarenmu.”

KU RATSA ZUCIYAR YARANKU

14. Mene ne ya kamata iyaye su yi, kuma me ya sa?

14 Ya kamata iyaye su tabbata cewa Kalmar Allah tana ratsa zuciyar yaransu. Bayan sun yi hidima fiye da shekara uku a inda ake wani yare, Serge da matarsa Muriel sun lura cewa ɗansu ɗan shekara 17 ba ya farin ciki sa’ad da ake abubuwan da suka shafi ibadarsu ga Jehobah. Muriel ta ce: “Ba ya jin daɗin fita wa’azi a inda ake wani yare, amma a dā yana son yin wa’azi a yarensa, wato Faransanci.” Serge ya ce: “Sa’ad da muka lura cewa wannan yanayin ya hana ɗanmu samun ci gaba a ƙungiyar Jehobah, sai muka koma ikilisiyarmu ta dā.”

Ku tabbata cewa gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah tana ratsa zuciyar yaranku (Ka duba sakin layi na 14, 15)

15. (a) Waɗanne abubuwa ne za su iya sa iyaye su koma ikilisiyar da ake yaren da yaransu suke ji? (b) Wane gargaɗi ne aka ba wa iyaye a Kubawar Shari’a 6:​5-7?

15 Waɗanne abubuwa ne za su sa iyaye su koma ikilisiyar da ake yaren da yaransu suka fi fahimta? Na farko, ya kamata su bincika kansu su ga ko suna da isashen lokaci da ƙarfin koya wa yaransu game da Jehobah da kuma koya musu wani yare. Na biyu, suna iya lura cewa yaransu ba sa jin daɗin ayyukan da suka shafi ibadarsu ga Jehobah ko kuma yaren da ake yi a inda suke hidima. A irin wannan yanayin, iyaye suna iya yin tunanin koma ikilisiyar da ke amfani da yaren da yaransu suka iya har sai dangantakar yaransu da Jehobah ta yi danko.​—⁠Karanta Kubawar Shari’a 6:​5-7.

16, 17. Ta yaya wasu iyaye suka taimaka wa yaransu yayin da suke hidima a inda ake wani yare?

16 A wani ɓangare kuma, wasu iyaye suna koya wa yaransu Kalmar Allah a yarensu duk da cewa suna halartan taro a wata ikilisiya ko rukunin da ake wani yare. Wani mahaifi mai suna Charles yana da yara mata uku. Ɗaya shekararta 13, ɗaya 12, ɗayar kuma 9. Suna halartan taro a yaren Lingala. Mahaifin ya ce: “Mun tsai da shawara cewa za mu riƙa yin nazari da kuma ibada ta iyali a yarenmu. Amma muna yin gwaji da wasan kwaikwayo a yaren Lingala don su ji daɗin koyon wannan yaren.”

Ku yi ƙoƙari ku koyi yaren da ake yi a yankinku kuma ku yi kalami a taro (Ka duba sakin layi na 16, 17)

17 Wani mahaifi mai suna Kevin yana da yara mata biyu. Ɗaya shekararta biyar, ɗayar kuma takwas. Ya ɗauki wasu matakai don ya koya musu abubuwan da ba sa ganewa a taron da ake yi a wani yare. Ya ce: “Ni da matata mukan yi nazari da su a yarenmu, wato Farasanci. Ƙari ga haka, mun kafa makasudin halartan taro a Farasanci sau ɗaya a wata, kuma muna amfani da lokacin hutunmu don mu halarci manyan taron da ake yi a yarenmu.”

18. (a) Wace ƙa’ida ce da ke cikin Romawa 15:​1, 2 za ta iya taimaka wa iyaye su san abin da zai amfani yaransu sosai? (b) Waɗanne shawarwari ne wasu iyaye suka ba da? (Ka duba ƙarin bayani.)

18 Hakika, kowane iyali ne za su tsai da shawara a kan abin da zai taimaka wa yaransu su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. [2] (Gal. 6:⁠5) Muriel da aka ambata ɗazu ta ce ita da mijinta sun sadaukar da abin da suke so don su taimaka wa ɗansu. (Karanta Romawa 15:​1, 2.) Serge yana ganin sun yanke shawara mai kyau. Ya ce: “Ɗanmu ya samu ci gaba sosai sa’ad da muka koma ikilisiyar da ake Faransanci kuma ya yi baftisma. Yanzu yana hidimar majagaba na kullum, kuma yana tunanin komawa rukunin da ake wani yare!”

KU BAR KALMAR ALLAH TA RATSA ZUCIYARKU

19, 20. Ta yaya za mu nuna cewa muna son Kalmar Allah?

19 Da yake Jehobah yana ƙaunar mutane, ya sa an fassara Littafi Mai Tsarki a harsuna da yawa don ‘dukan ire-iren mutane su kawo ga sanin gaskiya.’ (1 Tim. 2:⁠4) Ya san cewa ‘yan Adam za su fi ƙarfafa dangantakarsu da shi sa’ad da suka karanta Kalmarsa a yarensu.

20 Ko da a wane irin yanayi ne muka samu kanmu, ya kamata mu ƙuduri niyyar ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. Za mu iya yin hakan ta wajen yin nazarin Nassosi a kai a kai a yaren da zai taɓa zuciyarmu. Idan muka yi haka, za mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah da kuma dangantakar iyalinmu da shi, kuma za mu nuna cewa muna son Kalmar Allah sosai.​—⁠Zab. 119:⁠11.

^ [1] (sakin layi na 5) An canja sunayen.

^ [2] (sakin layi na 18) Don ku ga ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su iya taimaka wa iyalinku, ku duba talifin nan “Raising Children in a Foreign Land​—The Challenges and the Rewards” da ke cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Oktoba, 2002.