Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DAGA TARIHINMU

“Masu Shela a Britaniya, Ku Kusance da Kwazo!”

“Masu Shela a Britaniya, Ku Kusance da Kwazo!”

A CIKIN wani talifin da ke cikin ƙasidar da daga baya aka soma kiranta Hidimarmu Ta Mulki, an ba wa ‘yan’uwa a Britaniya wani umurni na gaggawa cewa: “Masu Shela a Britaniya, Ku Kusance da Ƙwazo.” Kan labarin ya daɗa cewa: “A cikin shekaru goma ba a samu ƙarin masu shela ba.” Rahoton hidima na shekara ta 1928 zuwa 1937 ya nuna cewa hakan gaskiya ne.

MAJAGABA SUN YI YAWA NE?

Me ya sa masu shela a ƙasar Britaniya suka daina yin ƙwazo a wa’azi? Mai yiwuwa ikilisiyoyin sun ci gaba da bin gurbin da aka kafa musu shekaru da yawa da suka shige. Ƙari ga haka, kwamiti da ke ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasar sun ce majagaba guda 200 ne kawai ake bukatar a ƙasar da za su yi wa’azi a yankuna masu nisa maimako su yi tare da ikilisiyoyi ba. Saboda haka, ofishin ya gaya wa majagaba a Britaniya cewa babu isashen yankuna yin wa’azi a ƙasar, don haka su je su yi hidima a wasu ƙasashen Turai. Majagaba da yawa sun bar ƙasar Britaniya kuma suka koma ƙasashe kamar Faransa don su yi hidima duk da cewa ba su iya yaren ba.

“KU KASANCE DA ƘWAZO”

Talifin da ke cikin Hidimarmu ta Mulki na shekara ta 1937 ya kafa makasudi da ake so a cim ma na yin wa’azi na sa’o’i miliyan ɗaya a shekara ta 1938! Za a iya cim ma wannan makasudin idan masu shela suka yi wa’azi na sa’o’i 15, majagaba kuma na sa’o’i 110 a kowace wata. Wasu shawarwarin da aka bayar su ne yadda za su tsara rukunin masu wa’azi don su keɓe ranakun da za su riƙa yin sa’o’i biyar suna wa’azi kuma su ɗin koma ziyara musamman ma da yamma.

Majagaba masu ƙwazo sun mai da hankali ga yin wa’azi

Yadda aka soma nanata muhimmancin kasancewa da ƙwazo a wa’azi ya sa ‘yan’uwa da yawa farin ciki. Wata ‘yar’uwa mai suna Hilda Padgett * ta ce: “Da daɗewa, yawancinmu muna ɗokin samun wannan saƙon kasancewa da ƙwazo daga hedkwatarmu kuma yin hakan ya kawo sakamako mai ban al’ajabi.” Wata ‘yan’uwa mai suna  E. F. Wallis ta ce: “Shawarar da aka ba da cewa a keɓe ranakun da za a riƙa yin sa’o’i biyar ana wa’azi yana da kyau sosai! Ba abin da ya fi yin amfani da dukan rana don yin aikin Ubangiji . . .  Wataƙila mukan dawo a gajiye amma muna farin ciki sosai!” Wani matashi mai suna Stephen Miller ya ga cewa ana bukatar a yi wannan aikin da gaggawa don hakan shi ma ya saka hannu a yin wa’azi. Yana so ya yi amfani da damar da yake da shi! Ya tuna da wasu rukunin masu shela da suke tuƙa keke suna wa’azi daga safe zuwa yamma kuma a lokacin rani suna saka wa mutane jawabai da aka ɗauka a faifai don su saurara. Ƙari ga haka, suna zagayawa suna ɗauke da fosta don yin wa’azi da kuma rarraba wa mutane mujallu a kan titi.

A cikin Hidimarmu Ta Mulki ɗin, an ambata cewa: “Muna bukatar majagaba guda 1,000.” An kuma ce majagaba ba za su riƙa yin wa’azi a wani yanki dabam su kaɗai ba amma tare da ‘yan’uwan da ke cikin ikilisiya don su taimaka musu da kuma ƙarfafa su. Wata ‘yar’uwa mai suna Joyce Ellis ta ce: “ ’Yan’uwa da yawa sun ga cewa ya kamata su soma hidimar majagaba. Ko da yake shekaruna 13 ne a lokacin, amma abin da nake so shi ne in zama majagaba.” Ta cim ma burinta sa’ad da ta kai shekara 15 a watan Yuli a shekara ta 1940. Peter, wanda daga baya ya zama mijin Joyce ya ce ya ji sa’ad da aka gaya wa masu shela su “Kasance da Ƙwazo,” kuma hakan ya sa ya “soma tunanin yin hidimar majagaba.” Sa’ad da yake ɗan shekara 17, ya tuƙa keke na kilomita 105 zuwa garin Scarborough a watan Yuni na shekara ta 1940 don ya yi hidimar majagaba a wajen.

Wasu ma’aurata da suka yi sadaukarwa don su soma hidimar majagaba sune Cyril da Kitty. Sun sayar da gidansu da kuma kayansu don su sami kuɗin da za su kula da kansu sa’ad da suka soma hidimar majagaba. Cyril ya bar aikinsa kuma a cikin wata ɗaya suka yi shirin soma yin hidimar majagaba. Ya ce: “Muna da tabbaci cewa abin da muka yi daidai ne kuma mun yi hakan da yardar rai kuma muna farin ciki.”

AN BUDE GIDAJEN MAJAGABA

Yayin da majagaba suka soma ƙaruwa sosai, sai wasu ‘yan’uwa masu hakki suka soma yin tunanin hanyoyin da za su iya taimaka musu. A shekara ta 1938, wanda yake hidima a matsayin zone servant (yanzu ana kiransa mai kula da da’ira) mai suna Jim Carr ya bi shawarar da aka bayar cewa a buɗe gidajen da majagaban za su riƙa zama a birane. An ƙarfafa rukunin majagaba su zauna da kuma wa’azi tare, ta hakan za a rage yawan kuɗin da ake kashewa. ‘Yan’uwa sun yi hayar wani babban gida a birnin Sheffield kuma wani ɗan’uwa ne zai riƙa kula da wajen. Ikilisiyoyin da ke wajen su ba da gudummawar kuɗi da kuma kayan ɗaki. Jim ya ce: “Dukanmu mu yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka wa majagaban.” Majagaba masu ƙwazo sosai guda goma ne suka zauna a gidan kuma suna yin ayyukan da suka ƙunshi ibadarsu ga Jehobah a kai a kai. Jim ya ƙara cewa: “Kowace safiya kafin su ci abinci sukan tattauna nassin yini. Bayan hakan, sai majagaban su tafi yankunansu a cikin birnin don su yi wa’azi.”

’Yan’uwa sun soma hidimar majagaba a Britaniya

Masu shela da kuma majagaba sun bi wannan gargaɗin da aka yi musu na kasancewa da ƙwazo kuma sun cim ma makasudin da aka kafa na yin sa’o’in miliyan ɗaya a shekara ta 1938. Ban da haka ma, rahoton ya nuna cewa sun samu ƙaruwa a kowane fanni na wa’azi. A cikin shekara biyar, adadin masu shela a ƙasar Britaniya ya ƙaru sosai. Yadda aka nanata kasancewa da ƙwazo a hidima ya ƙarfafa mutanen Allah don su jimre da yanayin yaƙe-yaƙe da za su fuskanci a nan gaba.

Yayin da yaƙin Armageddon yake gabatowa, adadin majagaba a Britaniya ya ci gaba da ƙaruwa. Sun sami ƙaruwa sosai cikin shekaru 10 da suka shige, kuma a watan Oktoba ta shekara ta 2015, adadin majagaba ya kai 13,224. Waɗannan majagaban sun san cewa ba abin da ya fi yin amfani da rayuwarsu wajen yin hidima ta cikakken lokaci.

^ sakin layi na 8 Da akwai tarihin ‘yar’uwa Padgett a cikin Hasumiyar Tsaro na 1 ga watan Oktoba, shekara ta 1995, shafuffuka na 19-24.