Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Jehobah Yana Ja-gorar Mutanensa

Jehobah Yana Ja-gorar Mutanensa

Jehobah zai “bi da ku kullayaumi.”ISHA. 58:11, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 152, 22

1, 2. (a) Ta yaya Shaidun Jehobah suka bambanta da sauran addinai? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin da kuma na gaba?

MUTANE sukan tambayi Shaidun Jehobah: “Wane ne shugabanku?” Suna yin hakan domin a addinai da yawa wani ko kuma wata ce ke shugabanci. Amma muna gaya ma waɗanda suka yi mana wannan tambayar cewa ba ɗan Adam ba ne Shugabanmu. Maimakon haka, muna bin ja-gorar Kristi da aka ta da daga mutuwa, wanda ya bi ja-gorar Ubansa, Jehobah.Mat. 23:10.

2 Duk da haka, da akwai rukunin maza da ake kira “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” da suke ja-gorar mutanen Allah a yau. (Mat. 24:45) Ta yaya muka san cewa Jehobah ne yake ja-gorarmu ta wurin Ɗansa? A wannan talifi da kuma na gaba, za a tattauna yadda Jehobah yake ja-gorar wasu bayinsa don su yi shugabanci shekaru da yawa yanzu. Waɗannan talifofin za su nuna abubuwa uku da suka nuna cewa Jehobah yana tallafa ma waɗannan mazan. Hakan ya nuna cewa shi ne har ila yake ja-gorar mutanensa da gaske.Isha. 58:11.

RUHU MAI TSARKI YA ƘARFAFA SU

3. Mene ne ya taimaka wa Musa ya ja-goranci Isra’ilawa?

3 Ruhu mai tsarki yana ƙarfafa wakilan Allah. Allah ya zaɓi Musa ya zama shugaban Isra’ilawa. Mene ne ya taimaka masa ya yi wannan aiki mai muhimmanci? Jehobah ya ba Musa “ruhunsa mai-tsarki.” (Karanta Ishaya 63:11-14.) Saboda haka, Jehobah ne ainihi yake ja-gorar mutanensa domin ruhunsa ne ya taimaka wa Musa.

4. Ta yaya Isra’ilawa suka san cewa ruhu mai tsarki ne yake taimaka wa Musa? (Ka duba hoton da ke shafi na 18.)

4 Tun da yake ba a iya ganin ruhu mai tsarki, ta yaya Isra’ilawa suka san cewa ruhu mai tsarki yana taimaka wa Musa? Ruhu mai tsarki ya taimaka wa Musa ya yi mu’ujizai kuma ya gaya wa Fir’auna sunan Allah. (Fit. 7:1-3) Ƙari ga haka, ruhu mai tsarki ya sa Musa ya kasance da halaye kamar su ƙauna da tawali’u da kuma haƙuri kuma waɗannan halayen ne suka taimaka wa Musa ya ja-goranci Isra’ilawa. Hakan ya bambanta shi da shugabannin wasu al’ummai masu zalunci da kuma son kai! (Fit. 5:2, 6-9) A bayyane yake cewa Jehobah ne ya zaɓi Musa ya zama shugaban mutanensa.

5. Ka bayyana yadda Jehobah ya ba wasu mutane iko su ja-goranci mutanensa.

5 Daga baya, ruhu mai tsarki ya taimaka ma wasu mutane da Jehobah ya naɗa, su ja-goranci mutanensa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Joshua kuma ɗan Nun yana cike da ruhun hikima.” (K. Sha. 34:9) “Ruhun Ubangiji ya shiga cikin Gideon.” (Alƙa. 6:34) Ƙari ga haka, “ruhun Ubangiji kuma ya jiɗo wa Dawuda da iko ƙwarai.” (1 Sam. 16:13) Dukan waɗannan mutane sun dogara ga taimakon ruhun Allah, kuma wannan ruhun ya taimaka musu su yi ayyukan da ba za su iya yi ba da ƙarfinsu. (Josh. 11:16, 17; Alƙa. 7:7, 22; 1 Sam. 17:37, 50) Saboda haka, ya dace a yabi Jehobah don abubuwan da mutanen nan suka yi don shi ya taimaka musu.

6. Me ya sa Allah yake so mutanensa su yi wa shugabannin Isra’ila ladabi?

6 Mene ne ya kamata Isra’ilawa su yi sa’ad da suka ga cewa ruhun Allah ne yake taimakon waɗannan mutanen? A lokacin da mutanen suka yi gunaguni game da shugabancin Musa, Jehobah ya ce: ‘Har yaushe mutanen nan za su rena ni?’ (Lit. Lis. 14:2, 11) Hakika, Jehobah ne ya zaɓi Musa da Joshua da Gideon da kuma Dauda su ja-goranci mutanensa. Idan Isra’ilawa suka bi ja-gorancin waɗannan mutane, hakan ya nuna cewa suna bin Jehobah a matsayin Shugabansu.

MALA’IKU SUN TAIMAKA MUSU

7. Ta yaya mala’iku suka taimaka wa Musa?

7 Mala’iku sun taimaka ma wakilan Allah. (Karanta Ibraniyawa 1:7, 14.) Jehobah ya yi amfani da mala’iku don su taimaka wa Musa kuma su yi masa ja-gora. Allah ya sa Musa ya “zama hakimi da mai-fansa ta hannun mala’ika wanda ya bayyana gare shi cikin sarƙaƙiya.” (A. M. 7:35) Ta hannun “mala’iku,” Jehobah ya ba mutane Doka da Musa ya yi amfani da ita don ya koyar da Isra’ilawa. (Gal. 3:19) Ƙari ga haka, Jehobah ya gaya masa: “Ka bi da mutane zuwa wurin da na ambata maka: ga mala’ikana za shi tafi gabanka.” (Fit. 32:34) Littafi Mai Tsarki bai faɗa ko Isra’ilawa sun ga wani mala’ika yana yin waɗannan ayyukan ba. Amma yadda Musa ya koyar da mutanen da kuma yi musu ja-gora ya nuna cewa mala’iku sun taimaka masa.

8. Ta yaya mala’iku suka taimaka wa Joshua da Hezekiya?

8 “Sarkin rundunar Ubangiji” ya taimaka wa Joshua wanda ya ɗauki matsayin Musa ya ja-goranci mutanen Allah sa’ad da suke yaƙi da Kan’aniyawa kuma Isra’ilawa sun ci yaƙin. (Josh. 5:13-15; 6:2, 21) Bayan haka, sa’ad da Sarki Hezekiya yake ja-gorar mutanen Allah, rundunar Assuriyawa sun yi ƙoƙari su kai wa Urushalima hari. Amma a cikin dare ɗaya “mala’ikan Ubangiji ya fita, ya buga mutum zambar ɗari da tamanin da biyar.”2 Sar. 19:35.

9. Ko da yake wakilan Allah ajizai ne, mene ne ya kamata Isra’ilawa su yi?

9 Hakika, ko da yake mala’iku kamiltattu ne, mutanen da suka taimaka, ajizai ne. Akwai lokacin da Musa bai ɗaukaka Jehobah ba. (Lit. Lis. 20:12) Joshua kuma bai nemi ja-gorar Allah kafin ya yi wa Gibeyonawa alkawari ba. (Josh. 9:14, 15) Akwai wani lokaci da Hezekiya ya yi girman kai. (2 Laba. 32:25, 26) Amma ko da yake waɗannan mutanen ajizai ne, an bukaci Isra’ilawa su yi musu biyayya. Jehobah yana amfani da mala’iku don ya tallafa wa mutanensa. Hakika, Jehobah ne yake ja-gorar mutanensa.

KALMAR ALLAH TA YI MUSU JA-GORA

10. Ta yaya Allah ya yi amfani da Dokarsa don ya yi wa Musa ja-gora?

10 Allah ya yi amfani da Kalmarsa don ya yi ma wakilansa ja-gora. Littafi Mai Tsarki ya kira Dokar da aka ba wa Isra’ilawa “shari’ar Musa.” (1 Sar. 2:3) Duk da haka, Nassosi sun ce Jehobah ne ainihi ya ba da Dokar, kuma Musa ya yi biyayya da dokar. (2 Laba. 34:14) Bayan Jehobah ya gaya wa Musa yadda zai gina mazaunin, “hakanan Musa ya yi: bisa ga dukan abin da Ubangiji ya umurce shi, haka ya yi.”Fit. 40:1-16.

11, 12. (a) Mene ne aka ce Joshua da sarakuna su yi? (b) Ta yaya Kalmar Allah ta taimaka ma waɗanda suke yi wa mutanen Allah ja-gora?

11 Joshua yana karanta Kalmar Allah lokacin da ya soma ja-gorar mutanen Allah, kuma Jehobah ya gaya masa: “Za ka riƙa bincikensa dare da rana, domin ka kiyaye ka aika bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki.” (Josh. 1:8) Daga baya, sarakunan da suka yi sarautar mutanen Allah sun bi misalin Joshua. An ba su umurni su riƙa karanta Dokar kowace rana, kuma su rubuta shi. Ƙari ga haka, za su ‘kiyaye dukan zantattukan wannan shari’a da farillan nan, domin su aikata.’—Karanta Kubawar Shari’a 17:18-20.

12 Ta yaya Kalmar Allah ta taimaka wa mutanen da suke ja-gora? Ka yi la’akari da misalin Sarki Josiah, bayan da aka gano wani littafin da ke ɗauke da abin da aka rubuta a Dokar da aka ba da ta hannun Musa, sakataren Josiah ya soma karanta masa dokar. * Mene ne sarkin ya yi? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’anda sarki ya ji zantattukan litafin shari’a, sai ya yage tufafinsa.” Ya yi wani abu kuma. Da yake yana so ya bi abin da aka rubuta a cikin Kalmar Allah sai Josiah ya soma halaka dukan gumaka da ke ƙasar kuma ya shirya a yi babban bikin Idin Ketarewa. (2 Sar. 22:11; 23:1-23) Domin Josiah da wasu shugabannai masu aminci sun bi ja-gorar da ke cikin Kalmar Allah, sun daidaita ra’ayinsu kuma sun bayyana wa mutanen abin da kalmar Allah ta ce. Waɗannan abubuwan da suka yi sun sa mutanen Allah a dā sun yi wa Jehobah biyayya.

13. Ta yaya shugabannin mutanen Allah suka bambanta da shugabannin al’ummai da ke kusa da su?

13 Shugabannin wasu al’ummai suna amfani da hikimar ɗan Adam ne sa’ad da suke sarauta. Alal misali, shugabannin mutanen Kan’ana da mutanensu sun yi munanan abubuwa kamar su jima’i tsakanin dangi da luwaɗi da kuma jima’i da dabbobi da yin hadaya da yara da kuma bautar gumaka. (Lev. 18:6, 21-25) Ƙari ga haka, shugabannin mutanen Babila da Masar ba su kafa irin dokokin kasancewa da tsabta da mutanen Allah suke da shi ba. (Lit. Lis. 19:13) Ban da haka, mutanen Allah na dā sun ga yadda shugabanninsu masu aminci suka ƙarfafa su su tsarkake bautarsu, su kasance da tsabta kuma su guji lalata. A bayane yake cewa Jehobah ne yake ma waɗannan shugabannin ja-gora.

14. Me ya sa Jehobah ya yi ma wasu shugabannin mutanensa horo?

14 Ba dukan shugabannin mutanen Allah ba ne suka kasance da aminci kuma suka bi umurninsa. Wasu shugabannin ba su yi wa Allah biyayya ba kuma sun ƙi su bi ja-gorar ruhu mai tsarki da mala’ikunsa da kuma Kalmarsa. A wasu lokatai Jehobah yana yi musu horo ko kuma ya sa wasu su ɗauki matsayinsu. (1 Sam. 13:13, 14) Daga baya Jehobah zai naɗa wanda zai zama shugaba kamiltacce.

JEHOBAH YA NAƊA SHUGABA KAMILTACCE

15. (a) Ta yaya annabawa suka nuna cewa shugaba kamiltacce yana zuwa? (b) Wane ne shugaba da aka yi annabcinsa?

15 Ƙarnuka da yawa, Jehobah ya yi annabci cewa zai naɗa wa mutanensa shugaba kamiltacce. Musa ya gaya wa Isra’ilawa cewa: “Ubangiji Allahnka za ya tayar maka da wani annabi daga tsakiyarka, a cikin ‘yan’uwanka, kamar ni; a gare shi za ku saurara.” (K. Sha. 18:15) Ishaya ya annabta cewa wannan zai zama “shugaba da mai-mulki ga al’ummai.” (Isha. 55:4) Kuma an hure annabi Daniyel ya rubuta game da wanda zai zama Almasihu “sarki.” (Dan. 9:25) A ƙarshe, Yesu Kristi ya nuna cewa shi ne ‘Shugaban’ mutanen Allah. (Karanta Matta 23:10, LMT.) Almajiran Yesu sun bi shi da zuciya ɗaya, kuma sun gaskata cewa shi ne Jehobah ya zaɓa. (Yoh. 6:68, 69) Mene ne ya tabbatar musu cewa ta wurin Yesu Kristi ne Jehobah yake ja-gorar mutanensa?

16. Mene ne ya nuna cewa ruhu mai tsarki ya taimaka wa Yesu?

16 Ruhu mai tsarki ya taimaka wa Yesu. Sa’ad da aka yi wa Yesu baftisma, Yohanna mai baftisma ya ga “sammai suka bude, ruhu kuwa da kamar kurciya yake saukowa a bisansa.” Bayan haka, “ruhu ya koro shi zuwa jeji.” (Mar. 1:10-12) A lokacin da Yesu yake hidima a duniya, ruhun Allah ya ba shi ikon koyar da mutane da gaba gaɗi da kuma yin mu’ujizai. (A. M. 10:38) Ƙari ga haka, ruhu mai tsarki ya taimaka wa Yesu ya nuna halaye kamar su ƙauna da farin ciki kuma ya kasance da bangaskiya sosai. (Yoh. 15:9; Ibran. 12:2) Babu wani shugaban da ya nuna yana da ruhun Allah kamar Yesu. Babu shakka, hakan ya nuna cewa Jehobah ne ya zaɓi Yesu ya zama shugaba.

Ta yaya mala’iku suka taimaka wa Yesu bayan da ya yi baftisma? (Ka duba sakin layi na 17)

17. Mene ne mala’iku suka yi don su taimaka wa Yesu?

17 Mala’iku sun taimaka wa Yesu. Ba da daɗewa ba bayan da Yesu ya yi baftisma, ‘mala’iku suka zo, suka yi masa hidima.’ (Mat. 4:11) Kafin Yesu ya rasu, wani “mala’ika daga sama ya bayana gare shi yana ƙarfafa shi.” (Luk. 22:43) Yesu yana da tabbaci cewa Jehobah zai aika mala’iku su taimaka masa don ya cim ma nufin Allah.Mat. 26:53.

18, 19. Ta yaya Yesu ya yi amfani da Kalmar Allah a koyarwarsa?

18 Kalmar Allah ta yi wa Yesu ja-gora. Yesu ya bar Littafi Mai Tsarki ya yi masa ja-gora a lokacin da ya soma hidimarsa a duniya. (Mat. 4:4) Ƙari ga haka, ya yi biyayya da Kalmar Allah sa’ad da yake kan gungumen azaba. Kuma kafin ya mutu, ya ambata wasu annabce-annabce da aka yi game da shi. (Mat. 27:46; Luk. 23:46) Amma, shugabannin addinai na zamaninsa ba su yi abin da Yesu ya yi ba. Sun ƙi bin Kalmar Allah a duk lokacin da suka ga wani abu a ciki da bai jitu da ra’ayinsu ba. Yesu ya yi amfani da Kalmar Allah sa’ad da yake magana game da su, ya ce: “Wannan al’umma tana girmama ni da leɓunansu; amma zuciyarsu tana nesa da ni. Amma banza suke yi mani sujada, koyarwa da suke yi dokokin mutane ne.” (Mat. 15:7-9) Jehobah ba zai taɓa zaɓan irin waɗannan mutanen su ja-goranci mutanensa ba.

19 Yesu ya kuma yi amfani da Kalmar Allah sa’ad da yake koyarwa. A lokacin da malaman addinai suka yi masa tambaya, bai yi amfani da hikimarsa ko abin da ya sani don ya ba su amsa ba. Maimakon haka, ya koya wa mutane abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (Mat. 22:33-40) Ƙari ga haka, da Yesu ya burge mutane da labaran rayuwa da ya yi a sama ko kuma game da halittar sama da ƙasa, ko ba haka? Amma bai yi hakan ba, maimakon haka, ya “buɗe hankalinsu, domin su fahimci littattafai.” (Luk. 24:32, 45) Yesu yana son Kalmar Allah kuma ya ji daɗin koya wa mutane abin da ke ciki.

20. (a) Ta yaya Yesu ya ɗaukaka Jehobah? (b) Ta yaya Yesu da Hirudus Agaribas suka bambanta?

20 Ko da yake masu sauraron Yesu sun yi mamakin yadda yake amfani da “zantattukan alheri” sa’ad da yake koyarwa, amma Yesu a koyaushe ya nuna cewa Jehobah ne ya koyar da shi. (Luk. 4:22) A lokacin da wani mutum mai arziki ya kira Yesu “Malam managarci,” Yesu ya amsa cewa: “Don me kake ce da ni managarci? Babu wani managarci sai ɗaya, Allah.” (Mar. 10:17, 18) Amma, Hirudus Agaribas wanda halinsa ya bambanta da na Yesu ya zama sarkin Yahudiya kusan shekaru takwas bayan da Yesu ya rasu. A wani taro na musamman da aka yi, Hirudus ya saka “tufafi na sarauta,” sai mutanen da suka ji jawabinsa suka soma yaba masa suna ihu suna cewa “muryar wani allah ke nan, ba ta mutum ba ce.” Me ya faru bayan haka? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Nan da nan kuwa mala’ikan Ubangiji ya buge shi, domin ba ya ba da girma ga Allah ba: tsutsotsi suka cinye shi, ya mutu.” (A. M. 12:21-23) Babu shakka, ba Jehobah ne ya zaɓi Hirudus ya zama shugaba ba. Amma Yesu ya nuna cewa Allah ya zaɓe shi, kuma yana ɗaukaka Jehobah a kai a kai a matsayin Babban Shugaban mutanensa.

21. Mene ne za a bincika a talifi na gaba?

21 Jehobah ya so Yesu ya zama shugaba na dogon lokaci, shi ya sa bayan da aka ta da Yesu daga mutuwa sai ya ce: “Dukan hukunci a cikin sama da ƙasa an bayar gare ni.” Sai ya daɗa cewa “ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.” (Mat. 28:18-20) Amma ta yaya Yesu zai yi wa mutanen Allah a duniya ja-gora tun da yake shi ruhu ne da ba a gani? Su waye ne Jehobah zai yi amfani da su don su yi ja-gorar mutanensa? Kuma ta yaya Kiristoci za su iya gane wakilansa? Za a amsa waɗannan tambayoyin a talifi na gaba.

^ sakin layi na 12 Wataƙila wannan ne littafi na asali da Musa ya rubuta.