Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Majagaba George Rollston da Arthur Willis sun tsaya don su cika lagireto motarsu da ruwa a yankin da ake kira Northern Territory a shekara ta 1933

DAGA TARIHINMU

“Ba Abin da Zai Iya Hana Mu Yin Wa’azi”

“Ba Abin da Zai Iya Hana Mu Yin Wa’azi”

A RANAR 26 ga Maris a shekara ta 1937, maza biyu da suka gaji tilis sun shiga birnin Sydney da ke ƙasar Ostareliya da babbar motarsu. Sun bar birnin shekara guda da ta shige kuma suka yi tafiya na kilomita 19,300 zuwa yankuna da suka fi nisa a ƙasar. Mutanen ba masu bincike ba ne. Sunansu Arthur Willis da Bill Newlands ne kuma suna cikin majagaba masu ƙwazo sosai da suka ƙudura niyya su yi wa’azin Mulkin Allah a ƙauyuka da suke ƙasar Ostareliya.

Kafin shekara ta 1929, ƙaramin rukunin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki * da ke Ostareliya sun yi wa’azi a birane da garuruwa da ke gaɓar teku na ƙasar kawai. A cikin ƙasar, akwai ƙauyuka da babu mutane sosai da kuma hamada da girmansu ya fi Nijeriya sau shida. Amma, ‘yan’uwan sun san cewa ya kamata mabiyan Yesu su yi wa’azi game da shi har zuwa “iyakan duniya” kuma hakan ya haɗa da ƙauyuka masu nisa a ƙasar Ostareliya. (A. M. 1:8) Amma ta yaya za su cim ma wannan babban aiki? Sun ƙuduri aniya za su yi iya ƙoƙarinsu don suna da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace su.

MAJAGABA NE SUKA SOMA WA’AZI

A shekara ta 1929, ‘yan’uwa da ke ikilisiyoyi a jihar Queensland da Yammacin Ostareliya sun ƙera manyan motoci don su je wa’azi a yankuna da ke ƙasar. Majagaba da suka ƙware a gyaran mota ne suke tuƙa waɗannan motocin don za su iya bi da yanayin hanyoyin kuma su gyara motocin idan suka lalace. Waɗannan majagaban sun je wurare da yawa da ba a taɓa zuwa wa’azi ba.

Majagaban da ba su da kuɗin sayan mota sun sayi kekuna. Alal misali, a shekara ta 1932, Bennett Brickell ɗan shekara 23 a lokacin ya bar birnin Rockhampton da ke jihar Queensland kuma ya yi tafiya na wata biyar yana wa’azi a dukan yankuna masu nisa da ke arewanci wannan jihar. Ya ɗauki bargo da tufafi da abinci da kuma littattafai da yawa a kan kekensa. Ya ci gaba da tafiya ko da kekensa ya yi faci, don yana da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka masa. A wuri na ƙarshe, ya tura keken har kilomita 320 ta hanyoyin da mutane suka mutu don ƙishirwa. Ɗan’uwa Brickell ya yi shekara 30 yana tafiya mil da yawa da keke da babur da kuma mota a duk ƙasar Ostareliya. Ƙari ga haka, ya yi wa asalin ‘yan ƙasar wa’azi kuma ya ƙafa sababbin ikilisiyoyi, hakan ya sa mutane suka san shi sosai a dukan ƙauyuka kuma suna daraja shi.

SUN SHAWO KAN MATSALOLI

Ƙasar Ostareliya tana cikin ƙasashe da mutane ba su da yawa sosai a duniya musamman a ƙauyukan. Saboda haka, Shaidun Jehobah sun ƙudura niyya su nemi mutane da ke ƙauyuka masu nisa na ƙasar don su yi musu wa’azi.

Majagaba Stuart Keltie da William Torrington sun nuna irin wannan ƙwazo. A shekara ta 1933 sun ƙetare babban hamadar da ake kiran Simpson don su yi wa’azi a garin Alice Springs da ke tsakiyar ƙasar. Akwai lokacin da ƙaramar motarsu ta lalace amma suka bar ta a wurin, sai suka ci gaba da wa’azi. Da yake Ɗan’uwa Keltie ƙafarsa ba lafiya, ya hau raƙumi yana zuwa wurare don ya yi wa’azi! Majagaban sun sami albarka don ƙoƙarce-ƙoƙarcensu sa’ad da suka haɗu da manajan wani otal a wani ƙauyen da ake kira William Creek, a wani tashar jirgin ƙasa. Daga baya, wannan manajan otal mai suna Charles Bernhardt ya soma bauta wa Jehobah kuma ya sayar da otal ɗinsa. Ban da haka, ya yi shekara 15 yana hidimar majagaba shi kaɗai a wasu hamada a yankunan Ostareliya masu nisa sosai.

Arthur Willis yana shirin tafiyar wa’azi a wani wurin da ake kira Perth, Western Australia a shekara ta 1936

Babu shakka, waɗannan majagaba sun bukaci ƙarfin zuciya da naciya don su shawo kan ƙalubale da suka fuskanta. Akwai lokacin da Arthur Willis da Bill Newlands da aka ambata ɗazu suke wa’azi a ƙauyukan Ostareliya kuma suka yi makonni biyu suna tafiyar kilomita 32 domin ruwan sama ya sa hamadar ta zama laka. A wasu lokatai, sun sha wahala sosai a cikin zafin rana don suna tura babbar motarsu a cikin ƙasa, don sun bi ta wurin tuddai da kuma hanyar da ke kusa da kogi mai yashi sosai. Sa’ad da motarsu ta lalace, sukan yi tafiya ko kuma su tuƙa keke na kwanaki da yawa kafin su kai wani gari kuma su jira na wasu kwanaki kafin su sami abubuwan da suka lalace a motar. Duk da irin waɗannan matsalolin, sun ci gaba da kasancewa da ra’ayi mai kyau. A lokacin da Arthur Willis yake maimaita wani furuci da aka yi a cikin mujallar The Golden Age wato Awake!, ya ce: “Ba abin da zai iya hana Shaidunsa yin wa’azi.”

Charles Harris wanda majagaba ne da daɗewa ya bayyana cewa kaɗaici da wahalar da ya sha a cikin ƙauyuka sun sa ya kusaci Jehobah. Ya daɗa cewa: “Ya fi kyau mutum ya yi rayuwa da ‘yan kaya. Idan Yesu yana shirye ya yi barci a waje idan ya zama dole, ya kamata mu ma mu yi farin cikin yin hakan.” Kuma abin da majagaba da yawa suka yi kawai. Ƙwazon da suka yi a wa’azi ya sa mutane a ko’ina a wannan nahiyar sun ji wa’azi kuma sun taimaka wa mutane da yawa su goyi bayan Mulkin Allah.

^ sakin layi na 4 An soma kiran Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da sunan nan Shaidun Jehobah a shekara ta 1931.Isha. 43:10.