Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Yadda Na Amfana Daga Yin Tarayya da Masu Hikima

Yadda Na Amfana Daga Yin Tarayya da Masu Hikima

AKWAI wata safiyar da muka tashi da sanyi sosai a birnin Brookings, da ke jihar South Dakota, a Amirka. Hakan ya tuna min cewa nan ba daɗewa ba, za a fara ruwan ƙanƙara da zai rufe ko’ina a yankin. Kuma abin mamaki shi ne, a wannan ranar, muna cikin wani ɗaki ne da ake ajiye kayan noma kuma muna jin sanyi. Muna tsaye kusa da wani babban wuri da ke cike da ruwa mai sanyi. Bari in ba ku labarin rayuwata don ku fahimci abin da nake nufi.

TARIHIN IYALINMU

Kawuna mai suna Alfred da mahaifina

An haife ni a ranar 7 ga Maris na shekara ta 1936. Mu huɗu ne iyayenmu suka haifa, kuma ni ne auta. Muna zama a ƙaramar gona da ke gabashin jihar South Dakota. Ko da yake iyalinmu ta ɗauki yin noma da muhimmanci, amma ba shi ba ne abu mafi muhimmanci a rayuwarmu ba. Iyayena sun yi baftisma a shekara ta 1934, saboda haka, yin nufin Allah ne ya fi muhimmanci a rayuwarsu. Mahaifina Clarence, kuma daga baya kawuna Alfred, sun zama masu tsara ayyukan dattawa a ƙaramar ikilisiyarmu da ke birnin Conde, a South Dakota.

Iyalinmu ba ta wasa da halartan taro da kuma fita wa’azi, muna bin gida-gida don mu gaya wa mutane game da bege mai ban al’ajabi da ke Littafi Mai Tsarki. Misalin da iyayenmu suka kafa da kuma yadda suka horar da mu ya taimaka mana sosai. Ni da yayata Dorothy, mun zama masu shela sa’ad da kowanenmu ya kai shekara shida. A shekara ta 1943, na sa sunana a Makarantar Hidima ta Allah, don a shekarar nan ne aka soma wannan makarantar.

Sa’ad da nake hidimar majagaba a shekara 1952

Mun ɗauki halartan taron yanki da manyan taro da muhimmanci sosai. Ɗan’uwa Grant Suiter ne baƙo mai jawabi a babban taron da aka yi a shekara ta 1949 a birnin Sioux Falls da ke South Dakota. Jigon jawabin da ya bayar shi ne “Ya Kusa Ne Fiye da Yadda Kuke Zato?” Ya nanata cewa dukan Kiristoci da suka keɓe kansu suna bukatar su yi wa’azi sosai game da Mulkin Allah. Hakan ya motsa ni na keɓe kai na ga Jehobah. A taron da’ira da aka yi a birnin Brookings, ina cikin waɗanda suke jira don su yi baftisma a wannan babban wuri da ke cike da ruwan sanyi kamar yadda na ambata ɗazun. A wannan wurin ne aka yi mana baftisma a ran 12 ga Nuwamba na shekara ta 1949. Kuma a taron, mu huɗu ne muka yi baftisma.

Sai na yanke shawara cewa zan soma hidimar majagaba. Kuma na yi hakan a ran 1 ga Janairu na 1952, kuma a lokacin ina da shekara 15. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima,” kuma akwai masu hikima da yawa a iyalinmu da suka so wannan shawarar da na tsai da. (Mis. 13:20) Kawuna Julius da ke da shekara 60 ne muke yin wa’azi tare. Mun ji daɗin hidima tare ko da yake ya girme ni sosai. Na koyi abubuwa masu kyau daga wurinsa. Ba da daɗewa ba, yayata Dorothy ma ta soma hidimar majagaba.

MASU KULA DA DA’IRA SUN TAIMAKA MINI

A lokacin da nake matashi, iyayena sukan gayyato masu kula da da’ira da matansu zuwa gidanmu. Wasu ma’aurata da suka taimaka mini sosai su ne Jesse da Lynn Cantwell. Ƙarfafar da suka yi min ne ya sa na soma hidimar majagaba. Tarayyar da ni da su ya sa na kasance da maƙasudai masu kyau a rayuwa. A duk lokacin da suke ziyartar ikilisiyoyin da suke kusa da mu, sukan ce mu je mu yi wa’azi tare. Mun ji daɗin hakan kuma mun sami ƙarfafawa sosai.

Bayan haka, sai Ɗan’uwa Bud Miller da matarsa Joan suka soma ziyartar mu a matsayin masu kula da da’ira. Kuma a lokacin da suka zo ikilisiyarmu, ina da shekara 18. Da yake shekaruna sun kai na shiga soja, sai hukuma ta saka sunana cikin waɗanda za a ɗauka cikin soja. Hakan ya ɓata mini rai sosai domin Yesu ya ƙi jinin aikin soja kuma ina son in yi wa’azi game da Mulkin Allah ne. (Yoh. 15:19) Sai na tsai da shawara cewa zan kai kuka wurin hukumar da ke shigar da mutane soja don su cire sunana daga cikin waɗanda za su shiga soja kuma aka saka a cikin masu wa’azi.

Na ji daɗi sosai sa’ad da Ɗan’uwa Miller ya ce zai bi ni don mu ga hukumar. Wannan Ɗan’uwan mutumin kirki ne, mai ibada kuma yana da gaba gaɗi sosai. Gabana ya daina faɗuwa sa’ad da ya ce zai raka ni wurin. Hukumar ta saurare mu sosai shi ya sa a shekara ta 1954, aka cire sunana daga cikin waɗanda za su shiga soja kuma aka saka sunana a cikin masu wa’azi. Hakan ya sa na cim ma wani makasudina.

Na tsaya kusa da babbar mota sa’ad da na fara hidima a Bethel

A wannan lokacin, an gayyace ni zuwa Bethel kuma na yi hidima a Watchtower Farm, a Staten Island a jihar New York. Na yi shekara uku ina hidima a wurin kuma na ji daɗin hidimar sosai. Na yi aiki da masu hikima a wurin kuma na koyi abubuwa masu yawa daga wurinsu.

HIDIMA A BETHEL

A tashar WBBR tare da Ɗan’uwa Franz

Akwai tashar rediyo na WBBR a Staten Island, wurin da gonar take. Shaidun Jehobah sun yi amfani da gidan rediyon nan daga shekara ta 1924 zuwa 1957. Masu hidima a Bethel kusan ashirin ne suke aiki a wurin. Yawancinmu matasa ne da ba mu ƙware ba. Akwai wani ɗan’uwa mai suna Eldon Woodworth wanda shafaffe ne kuma yana aiki tare da mu. Shi mai hikima ne sosai. Ya taimaka mana sosai wajen ƙarfafa dangantakarmu da Allah. A lokacin da wasu suka yi wasu abubuwan ban haushi, sai Ɗan’uwa Woodworth ya ce, “Babu shakka, Ubangiji yana haƙuri da irin mutanen da yake amfani da su.”

Ɗan’uwa Harry Peterson ya kasance da ƙwazo a wa’azi

Ƙari ga haka, mun sami gatan yin aiki tare da Ɗan’uwa Frederick W. Franz. Yana da hikima sosai kuma ya san Nassosi. Ya taimaka mana sosai don yana ƙaunar mu. Ɗan’uwa Harry Peterson ne yake dafa mana abinci kuma muna kiransa da sunan mahaifinsa domin ainihin sunan shi ne Papargyropoulos, kuma sunan yana da wuya. Shi ma shafaffe ne da ba ya wasa da aikinsa a Bethel. Duk da haka, ya ɗauki yin wa’azi da muhimmanci. Yana ba mutane mujallu ɗarurruwa a kowane wata. Ban da haka, shi ma ya san Nassosi sosai kuma shi yake amsa tambayoyi da yawa da muke yi.

‘YAN’UWA MATA MASU HIKIMA SUN TAIMAKA MINI

A gonar, akwai wurin da ake ajiye amfanin gona. Ana saka wajen kwanduna 45,000 na ‘ya’yan itatuwa da kuma wasu ganyaye a gongoni don masu hidima a Bethel su riƙa amfani da shi kowace shekara. Hakan ya sa na yi aiki da wata ‘yar’uwa mai hikima da ake kira Etta Huth. ‘Yar’uwar ce take kula da yadda ake saka ‘ya’yan itatuwan da kuma ganyayen a gongoni. ‘Yan’uwa mata suna zuwa don su taimaka sa’ad da ake wannan aikin kuma ‘yar’uwa Etta ce take tsara yadda za a yi aikin. Ko da yake ‘yar’uwar ta iya aikin sosai, ba ta raina ‘yan’uwa maza da suke kula da gonar ba kuma mun koyi darasi daga abin da ta yi. Ta kafa min misali mai kyau na yin biyayya da tsarin da Allah ya kafa na shugabanci.

Ni da Angela da kuma Etta Huth

Wata ‘yar’uwa mai suna Angela Romano tana cikin ‘yan’uwa matasa da suka zo don su taimaka a aikin. Etta ta taimaka mata sa’ad da ta soma bauta wa Jehobah. Saboda haka, sa’ad da nake hidima a Bethel, na sami wata mai hikima wadda a yanzu mun yi wajen shekara 58 muna hidima tare. Na auri ‘yar’uwa Angie a watan Afrilu na shekara ta 1958, kuma mun yi hidima dabam-dabam tare. A shekarun nan, irin amincin da Angie ta kasance da shi ya ƙarfafa aurenmu sosai. Ko da wane irin yanayi ne muka sami kanmu, na tabbata za ta ƙarfafa ni.

HIDIMA A WATA ƘASA DA HIDIMAR MAI KULA DA DA’IRA

Na yi hidima a Bethel da ke Brooklyn na ɗan lokaci ne kawai bayan da aka sayar da wurin da tashar WBBR take a shekara ta 1957. Sa’ad da ni da Angie muka yi aure, sai muka bar Bethel kuma muka yi hidimar majagaba na kusan shekara uku a Staten Island. Wasu sun sayi tashar rediyonmu kuma suka canja masa suna zuwa WPOW, kuma na yi aiki da su.

Ni da matata Angie mun tsai da shawarar sauƙaƙa rayuwarmu don mu sami damar yin hidima a wurare dabam-dabam. Don haka, a shekara ta 1961, an tura mu birnin Falls City, a jihar Nebraska. Bayan haka, sai aka gayyace mu zuwa Makarantar Hidima ta Mulki, a lokacin ana yin koyarwa na wata ɗaya ne kawai kuma wurin da ake makarantar shi ne South Lansing, a jihar New York. Mun ji daɗin makarantar don abubuwan da muka koya za su taimaka mana a hidimar da muke yi a jihar Nebraska. Amma sai aka tura mu zuwa ƙasar Kambodiya a matsayin masu wa’azi a ƙasar waje. Zuwa wannan ƙasa mai kyau da ke kudu maso gabashin Asiya ya sa mun ga wurare da abubuwa da suka bambanta da abubuwan da muka saba da su. Mun so mu yi wa’azi a wurin.

Amma da yanayin ƙasar ya canja saboda siyasa, sai muka ƙaura zuwa jihar South Vietnam. Amma ban yi dace a wurin ba domin a cikin shekara biyu da muka yi hidima a wurin, na yi rashin lafiya mai tsanani kuma aka shawarce mu mu koma ƙasarmu. Na koma gida don in yi jinya, amma da na sami sauƙi, sai muka soma hidima ta cikakken lokaci kuma.

Sa’ad da ni da Angela muka je ganawa a tashar talabijin a shekara ta 1975

A watan Maris na shekara ta 1965, mun sami gatan yin hidima a matsayin masu kula masu ziyara. Ni da matata Angie mun yi shekaru 33 muna hidimar masu kula da da’ira da kuma hidimar masu kula da gunduma. Ban da haka ma, mun ji daɗin shirya manyan taro. Ina jin daɗi a duk lokacin da ake yin manyan taro kuma ina taimakawa wajen tsara su. Mun yi shekaru muna hidima a Birnin New York kuma an yi manyan taro da yawa a filin wasa da ake kira Yankee Stadium.

HIDIMA A BETHEL DA KUMA KOYARWA A MAKARANTU

Mun fuskanci ƙalubale da kuma abubuwa masu faranta rai a hidima ta cikakken lokaci ta musamman da muka yi shekaru muna yi. Alal misali, a shekara ta 1995, na sami gatan koyar da ‘yan’uwa a Makarantar Koyar da Masu Hidima. Bayan shekaru uku, an ƙara gayyatar mu zuwa Bethel. Na yi farin cikin komawa wurin da na soma hidima ta cikakken lokaci na musamman fiye da shekaru 40 da suka shige. Na yi hidima a Sashen Kula da Hidima kuma na koyar da ‘yan’uwa a makarantu da yawa. A shekara ta 2007, Hukumar da ke Kula da Ayyukanmu ta kafa Sashen Makarantun Hidima ta Allah kuma ta ce na riƙa kula da shi kuma na yi shekaru da yawa ina yin wannan aikin.

An yi ta kyautata tsarin makarantu a kwana-kwanan nan. An soma Makaranta Don Dattawan Ikilisiya a shekara ta 2008. Kuma cikin shekara biyu, an koyar da dattawa 12,000 a Bethel da ke Patterson a Brooklyn. Ƙwararrun dattawa suna koyar da ‘yan’uwa har wa yau a wurare dabam-dabam. A shekara ta 2010 ne aka canja sunan Makarantar Koyar da Masu Hidima zuwa Makarantar Littafi Mai Tsarki don ‘Yan’uwa Maza Marasa Aure. Bayan haka, sai aka kafa makarantar da ake kira Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata.

Amma a shekara ta 2015 ne aka haɗa waɗannan makarantun kuma aka kira shi Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Ma’aurata da waɗanda ba su yi aure ba, maza da mata, za su iya halartar makarantar. ‘Yan’uwa a faɗin duniya sun yi farin ciki sa’ad da suka ji cewa za a yi waɗannan makarantu a ofisoshinmu dabam-dabam a duniya. Mun yi farin cikin ganin yadda aka kyautata makarantun Allah kuma na yi farin cikin haɗuwa da ‘yan’uwa da yawa da suka ba da kansu don su halarci waɗannan makarantun.

Idan na soma tunanin abubuwan da suka faru kafin in yi baftisma da kuma bayan da na yi baftisma, ina godiya ga Jehobah don yadda ya tanadar da masu hikima da suka taimaka mini a ibadar da nake yi masa. Ko da yake wasu cikinsu shekarunmu ba ɗaya ba kuma mun fito ne daga ƙasashe dabam-dabam, muna da haɗin kai kuma su masu ibada ne sosai. Halinsu da yadda suke yin abubuwa ya nuna cewa suna ƙaunar Jehobah sosai. A ƙungiyar Jehobah, muna da masu hikima sosai da za mu iya yin koyi da su. Na yi koyi da su kuma na amfana sosai.

Ina jin daɗin hira da ɗaliban da suka zo daga ƙasashe dabam-dabam