Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

‘Ka Biya Abin da Ka Yi Wa’adi’ ko Alkawarinsa

‘Ka Biya Abin da Ka Yi Wa’adi’ ko Alkawarinsa

“Sai ka cika wa’adodinka ga Ubangiji.”MAT. 5:33.

WAƘOƘI: 63, 59

1. (a) Mene ne Jephthah da Hannatu suka yi? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika a wannan talifin?

AN TAƁA yin wani jarumi wanda shugaba ne da kuma wata mace mai hankali. Dukansu suna bauta wa Jehobah kuma akwai wani abu mai kyau da su biyun suka yi. Sun cika alkawarin da suka yi wa Allah. Su waye ne waɗannan mutanen? Jephthah ne da Hannatu matar Elkanah. Waɗannan mutanen sun kafa wa maza da mata misali mai kyau game da cika alkawari. Amma akwai wasu tambayoyi masu muhimmanci da ya kamata mu sami amsarsu: Mene ne wa’adi ko alkawari? Me ya sa cika alkawarin da muka yi wa Allah yake da muhimmanci? Wane darasi ne za mu iya koya daga Jephthah da kuma Hannatu?

2, 3. (a) Mene ne alkawari ko wa’adi? (b) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da yin wa’adi?

2 Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa wa’adi, alkawari ne da muke yi wa Allah. Mutum zai iya yin alkawarin yin wani aiki, ba da wata kyauta, ko yin wata hidima ko kuma daina yin wasu abubuwa. Mutum yakan yi alkawari da zuciya ɗaya, ba sai an matsa masa ba. Duk da haka, Allah yana ɗaukan wa’adi ko alkawarin da mutane suke yi da muhimmanci domin yana kamar rantsuwa ce suka yi cewa za su yi wani abu ko kuma za su daina yin wasu abubuwa. (Far. 14:22, 23; Ibran. 6:16, 17) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa da ya nuna cewa yin wa’adi ko kuma alkawari yana da muhimmanci?

3 Dokar da aka bayar ta hannun Musa ta ce: “Sa’anda mutum ya yi wa’adi ga Ubangiji, ko kuwa ya yi rantsuwa . . . , ba za ya warware maganarsa ba; sai shi aika dukan abin da bakinsa ya furta.” (Lit. Lis. 30:2) Bayan haka, Sulemanu ya ce: “Sa’anda kake yin wa’adi a gaban Allah, ka biya ba tare da jinkiri ba; gama ba shi jin daɗin wawaye: sai ka biya abin da ka yi wa’adinsa.” (M. Wa. 5:4) Yesu ya faɗi muhimmancin wa’adi sa’ad da ya ce: “Kun ji aka faɗa ma mutanen dā, Ba za ka yi rantsuwa da ƙarya ba, amma sai ka cika wa’adodinka ga Ubangiji.”Mat. 5:33.

4. (a) Me ya sa alkawari ko wa’adi da muka yi wa Allah yake da muhimmanci? (b) Wane darasi za mu koya daga Jephthah da kuma Hannatu?

4 Hakan ya nuna cewa yi wa Allah alkawari batu ne mai muhimmanci sosai. Yadda muka ɗauki alkawari ko wa’adi da muka yi yana shafan dangantakarmu da Jehobah. Dauda ya ce: ‘Wane ne za ya hau zuwa tudun Ubangiji? Wane ne za ya tsaya a cikin wurinsa mai-tsarki? Shi wanda . . . bai ɗauki ransa ya sa ga abin banza ba, ba ya kuwa rantse da munafunci ba.’ (Zab. 24:3, 4) Wane alkawari ne Jephthah da Hannatu suka yi, kuma me ya sa cika alkawarin yake da wuya?

SUN CIKA ALKAWARIN DA SUKA YI MA ALLAH

5. Wane alkawari ne Jephthah ya yi kuma da wane sakamako?

5 Jephthah ya cika alkawarin da ya yi wa Jehobah game da Ammonawa da suke ta yi wa mutanen Allah barazana. (Alƙa. 10:7-9) Da yake Jephthah yana son ya yi nasara a yaƙin, sai ya yi alkawari cewa: “Idan dai hakika za ka ba da ‘ya’yan Ammon a cikin hannuna: sa’an nan za ya zama, ko mene ne da za ya fito ta ƙofofin gidana garin ya tarbe ni, sa’anda na dawo lafiya daga bin sawun Ammon, za ya zama na Ubangiji.” Ya yi nasara kuwa? Hakika ya yi nasara a kan Ammonawa kuma ‘yarsa tilo da yake ƙauna ce ta fito don ta marabce shi sa’ad da ya dawo. Ita ce za ta “zama na Ubangiji.” (Alƙa. 11:30-34) Mene ne hakan ya ƙunsa?

6. (a) Shin ya yi ma Jephthah da ‘yarsa sauƙi ne su cika alkawarin da ya yi? (b) Mene ne littafin Kubawar Shari’a 23:21, 23 da kuma Zabura 15:4 suka faɗa game da yi ma Allah alkawari?

6 Don ta cika alkawarin da mahaifinta ya yi, ‘yar Jephthah tana bukatar yin hidima a mazauni har ƙarshen ranta. Shin Jephthah bai yi tunani ba ne kafin ya yi wannan alkawarin? A’a. Wataƙila ya san cewa ‘yarsa ce za ta fito don ta marabce shi. Duk da haka, bai kasance masa da sauƙi ya cika alkawarin ba don yana son ‘yarsa sosai. Ita ma ‘yar Jephthah abin bai zo mata da sauƙi ba. Da ya ga cewa ita ce ta fito, sai ya yage “tufafinsa,” ya ce an kashe masa gwiwa. ‘Yar kuma ‘ta yi kukan budurcinta.’ Me ya sa? Jephthah bai da ɗa kuma ‘yarsa ba za ta iya yin aure ba don ta haifa masa jikoki. Ban da haka ma, ba wanda zai gāji sunansa. Amma wannan ma ba shi ne matsalar ba. Jephthah ya ce: “Na rigaya na buɗe bakina wurin Ubangiji, ba shi kuwa yiwuwa” in karya alkawarin. Sai ‘yarsa ta ce: “Ka yi mani bisa ga abin da ya fito daga cikin bakinka.” (Alƙa. 11:35-39) Mutanen nan suna da aminci, shi ya sa suka ƙi karya alkawarin da suka yi ma Allah Maɗaukaki duk da cewa hakan yana da wuya.Karanta Kubawar Shari’a 23:21, 23; Zabura 15:4.

7. (a) Wane alkawari ne Hannatu ta yi, me ya sa ta yi alkawarin, kuma mene ne sakamakon? (b) Me Sama’ila zai yi don ya cika alkawarin da mahaifiyarsa Hannatu ta yi? (Ka dubi ƙarin bayani.)

7 Hannatu ma ta cika alkawarin da ta yi wa Jehobah. Ta yi masa alkawari sa’ad da take baƙin ciki sosai don ba ta haihu ba, kuma ana mata baƙar magana. (1 Sam. 1:4-7, 10, 16) Hannatu ta yi addu’a ga Allah ta ce: “Ya Ubangiji mai-runduna, idan dai ka yarda ka dubi ƙuncin baiwarka, ka tuna da ni, ba ka kuwa manta da baiwarka ba, amma ka ba baiwarka ɗa namiji, ni ma sai in ba da shi ga Ubangiji muddar ransa, kuma aska ba za ta bi ta kansa ba.” * (1 Sam. 1:11) Allah ya ji addu’ar Hannatu kuma ya ba ta ɗa. Babu shakka, ta yi farin ciki sosai. Har ila, ba ta manta da alkawarin da ta yi ma Allah ba. Sa’ad da ta haifi ɗan, sai ta ce: “Na roƙo shi ga Ubangiji” ne.1 Sam. 1:20.

8. (a) Alkawarin da Hannatu ta yi wa Allah yana da sauƙin cikawa kuwa? (b) Ta yaya furucin da Dauda ya yi a Zabura 61 ya tuna mana da misali mai kyau da Hannatu ta kafa?

8 Da Hannatu ta yaye Sama’ila, sai nan da nan ta kai shi wurin da zai riƙa yi wa Allah hidima. Kuma a lokacin, shekarunsa uku ne ko sama da hakan. Da ta kai Sama’ila wurin Babban Firist mai suna Eli a mazauni, sai ta ce: “Domin wannan yaro na yi addu’a: Ubangiji kuma ya ba ni roƙona da na biɗa a gareshi: domin wannan ni kuma na ba da shi ga Ubangiji: an bayar da shi ga Ubangiji muddar ransa.” (1 Sam. 1:24-28) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sama’ila ya yi girma a gaban Ubangiji.” (1 Sam. 2:21) Abin da Hannatu ta yi yana da sauƙi ne? A’a. Tana son ɗanta sosai kuma yanzu ba za ta riƙa ganinsa kullum ba. Babu shakka, ta so su zauna tare don ta riƙe shi ta kula da shi kuma su yi wasa tare kamar yadda iyaye suke yi ma yaransu sa’ad da suke girma. Duk da haka, Hannatu ta cika alkawarin da ta yi wa Allah kuma ba ta yi da-na-sani ba.1 Sam. 2:1, 2; karanta Zabura 61:1, 5, 8.

Kana cika alkawarin da ka yi wa Jehobah kuwa?

9. Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?

9 Yanzu da muka fahimci yadda yin wa’adi ko alkawari yake da muhimmanci, bari mu bincika waɗannan tambayoyin: Waɗanne irin wa’adi ko alkawari ne Kiristoci suke yi? Kuma ta yaya za mu kuɗiri aniyar cika alkawuran da muka yi?

ALKAWARIN DA KA YI SA’AD DA KA KEƁE KANKA

Alkawarin keɓe kai (Ka duba sakin layi na 10)

10. Wane alkawari ko wa’adi mai muhimmanci ne Kiristoci suke yi, kuma mene ne hakan ya ƙunsa?

10 Wa’adi ko alkawari mai muhimmanci da Kiristoci suke yi shi ne keɓe kansu wa Jehobah. Ta yaya? Mutum zai yi addu’a ga Allah kuma ya yi alkawari cewa zai bauta masa har ƙarshen ransa ko da me ya faru. Kamar yadda Yesu ya ce, mutum zai “yi musun kansa” kuma ya yi alkawarin saka bautar Allah a gaba. (Mat. 16:24) Tun daga lokacin, ya zama “na Ubangiji.” (Rom. 14:8) Duk wanda ya keɓe kai ga Allah bai kamata ya yi wasa da wannan alkawarin da ya yi ba. Wani marubucin zabura ma ya yi wani furuci game da alkawarin da ya yi wa Allah. Ya ce: “Me zan bayar ga Ubangiji sabili da dukan alherinsa a gareni? In cika alkawarina ga Ubangiji. I, a gaban dukan jama’arsa.”Zab. 116:12, 14.

11. Wane alkawari ne ka yi a ranar da ka yi baftisma?

11 Shin ka yi alkawarin bauta ma Jehobah kuma ka yi baftisma? Idan ka yi hakan, muna yaba maka! Ka tuna cewa a lokacin da ka yi baftisma, an yi muku tambayar nan a gaban jama’a: Ko kun “fahimci cewa keɓe kai da kuma yin baftisma za su nuna cewa kun zama Shaidun Jehobah, waɗanda suke tarayya da ƙungiyar da Allah yake yi wa ja-gora ta hanyar ruhunsa?” Amsar da kuka bayar ya nuna cewa kun cancanci a yi muku baftisma a matsayin masu hidima da Jehobah ya naɗa. Hakan ya sa Jehobah farin ciki sosai!

12. (a) Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi ma kanmu? (b) Waɗanne halaye ne Bitrus ya ƙarfafa mu mu kasance da su?

12 Baftisma ita ce mataki na farko da mutum yake ɗauka wa don ya zama aminin Jehobah. Saboda haka, muna bukatar mu ci gaba da riƙe alkawarin da muka yi wa Allah. Shi ya sa ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Ina samun ci gaba ne tun daga lokacin da na yi baftisma? Ina bauta wa Jehobah da dukan zuciyata? (Kol. 3:23) Ina addu’a da karanta Kalmar Allah da halartan taron ikilisiya da kuma yin wa’azi a kai a kai? Na rage yin ayyukan ibada da na saba yi a dā?’ Manzo Bitrus ya nuna cewa idan muna yin nazari, kuma muka zama masu haƙuri, za mu guji yin sanyin gwiwa kuma za mu ƙarfafa bangaskiyarmu.Karanta 2 Bitrus 1:5-8.

13. Me ya kamata wanda ya keɓe kansa kuma ya yi baftisma ya tuna?

13 Ba zai yiwu mu canja alkawarin da muka riga muka yi wa Allah na bauta masa har ƙarshen ranmu ba. Idan mutum ya gaji da bauta ma Jehobah, ba zai iya ce zai soke alkawarin da ya yi kuma ya ce baftismar da ya yi ta zama banza ba. * Domin da ya yi baftisma ya nuna wa kowa cewa ya ba da kansa gabaki ɗaya ne ga Jehobah. Kuma zai ba da lissafin zunubin da ya yi a gaban Jehobah da kuma ikilisiya. (Rom. 14:12) Bai kamata a ce mun “bar ƙaunarmu ta fari” ba. A maimakon haka, muna son Yesu ya gaya mana cewa: “Na san ayyukanka, ƙaunarka, bangaskiyarka, hidimarka da haƙurinka, na sani kuma ayyukanka na ƙarshe sun ɗara na fari.” (R. Yoh. 2:4, 19) Bari mu ci gaba da riƙe alkawarin da muka yi na bauta wa Jehobah har ƙarshen ranmu.

ALKAWARIN AURE

Alkawarin aure (Ka duba sakin layi na 14)

14. Wane alkawari na biyu mai muhimmanci ne mutum yake yi kuma me ya sa?

14 Wa’adi ko alkawari na biyu mai muhimmanci da mutum yake yi shi ne na aure. Me ya sa? Domin aure abu ne da Allah ya kafa. Amarya da ango suna alkawari a gaban Allah da kuma mutane. Suna yin alkawari cewa za su so juna kuma su mutunta juna, kuma za su yi hakan ‘har iyakar rayuwarsu tare cikin duniya bisa ga tsarin aure na Allah.’ Ko da yake wasu ba su yi amfani da waɗannan kalaman ba sa’ad da suka yi aure, duk da haka, sun yi alkawari a gaban Allah. Bayan haka, suka zama mata da miji kuma za su zauna tare har ƙarshen ransu. (Far. 2:24; 1 Kor. 7:39) Yesu ya ce: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum ya raba.” Saboda haka, bai kamata mata da miji su soma tunani cewa za su iya kashe aure idan ba sa jin daɗinsa ba.—Mar. 10:9.

15. Me ya sa bai kamata Kiristoci su kasance da ra’ayin duniya game da aure ba?

15 Hakika, babu ma’auratan da ba sa samun matsaloli a aurensu don dukansu ajizai ne. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce ma’aurata za su “sha wahala a cikin jiki” a wasu lokuta. (1 Kor. 7:28) Abin baƙin ciki shi ne, yawancin mutane suna da ra’ayin da bai dace ba game da aure. Idan suka sami matsala a aurensu, sai su kashe auren kawai. Bai dace Kirista ya riƙa yin hakan ba. Karya alkawarin aure yana kama da yi wa Allah ƙarya kuma mun san cewa Allah ya tsani maƙaryata! (Lev. 19:12; Mis. 6:16-19) Manzo Bulus ya ce: “Kana ɗaure ne ga mace? Kada ka nemi kwancewa.” (1 Kor. 7:27) Abin da ya sa Bulus ya faɗi hakan shi ne domin ya san cewa Jehobah ya tsani kashe aure ba tare da wata ƙwaƙƙwarar dalili ba.Mal. 2:13-16.

16. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da kashe aure da kuma rabuwa?

16 Yesu ya koyar da cewa wata ƙwaƙƙwarar dalili ɗaya da za ta iya sa a kashe aure shi ne idan wani cikin ma’auratan ya ƙi ya gafarta wa abokin aurensa ko abokiyar aurensa da ta yi zina. (Mat. 19:9; Ibran. 13:4) Mene ne Kalmar Allah ta ce game da rabuwa? Littafi Mai Tsarki bai ɓoye kome game da hakan ba. (Karanta 1 Korintiyawa 7:10, 11.) Babu wani nassi da ya goyi bayan rabuwa. Duk da haka, wasu ma’aurata Kiristoci sun rabu domin abokin aurensu da ba ya bauta wa Jehobah ko kuma ya yi ridda, yana yawan cin zalinsu ko kuma yana hana su bauta wa Jehobah. *

17. Ta yaya ma’aurata za su sa aurensu ya dawwama?

17 Idan ma’aurata suka nemi shawarar dattawa don matsalolin da suke fuskanta a aurensu, zai dace dattawa su tambayi ma’auratan ko sun kalli bidiyon nan Mece Ce Ƙauna Ta Gaskiya? Ko kuwa sun yi nazarin ƙasidar nan Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya. Me ya sa? Don waɗannan abubuwa sun nuna ƙa’idodin da suka taimaka wa mutane da yawa su ƙarfafa aurensu. Wani mutum da matarsa sun ce: “Mun fi jin daɗin aurenmu tun daga lokacin da muka soma nazarin wannan ƙasidar.” Wata mata da ta yi shekaru 22 da aure da sauran kaɗan su kashe aurensu ta ce: “Mun yi baftisma, amma ni da mijina ba mu shaƙu da juna ba. An fito da wannan bidiyon a lokacin da ya dace! A yanzu, muna ƙoƙarin mu ƙarfafa aurenmu.” Shin kana da aure? Ka yi iya ƙoƙarinka don ka bi ƙa’idodin Jehobah a aurenka. Yin hakan zai taimaka muku ku cika alkawarin da kuka yi sa’ad da kuka yi aure!

ALKAWARIN DA MASU HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI TA MUSAMMAN SUKA YI

18, 19. (a) Mene ne iyaye da yawa suka yi? (b) Wane alkawari ne waɗanda suke hidima ta cikakken lokaci ta musamman suka yi?

18 Shin akwai wata alaƙa kuma tsakanin alkawarin Jephthah da na Hannatu? Alkawarin da suka yi ya sa yaransu sun yi tsarkakkiyar hidima a mazauni kuma hakan rayuwa ce mai ma’ana. A yau, iyaye da yawa sun ƙarfafa yaransu su soma hidima ta cikakken lokaci don su mai da hankali ga yin nufin Allah. Muna yaba ma waɗanda suka yi hakan.Alƙa. 11:40; Zab. 110:3.

Alkawarin hidima ta cikakken lokaci ta musamman (Ka duba sakin layi na 19)

19 A yanzu haka, akwai masu hidima ta Cikakken Lokaci ta Musamman wajen 67,000 a faɗin duniya. Wasu suna hidima a Bethel da wuraren da ake gine-gine da masu kula da da’ira da masu koyarwa a makarantu, da majagaba na musamman da masu-wa’azi a ƙasashen waje da masu kula da Majami’ar Taro ko kuma wuraren da ake koyar da masu hidima. Dukansu sun cika takardar da ake kira “Vow of Obedience and Poverty.” A cikin takardar, sun amince za su yi duk wata hidima da aka ce su yi a ƙungiyar Jehobah don yin wa’azin Mulkin Allah da yin rayuwa mai sauƙi da kuma ƙin neman kuɗi ko yin aikin albashi ba tare da izini ba. Hidimar da suke yi ita ce ta musamman ba mutanen da ke hidimar ba. Masu hidimar sun san muhimmancin riƙe wannan alkawarin muddin suna hidima ta cikakken lokaci ta musamman.

20. Me ya kamata mu riƙa yi “kowace rana,” kuma me ya sa?

20 Shin guda nawa ne cikin alkawura ko wa’adodi da muka tattauna ka yi? Ɗaya ko biyu ko kuma duka ukun? Babu shakka, kamar yadda muka tattauna, bai kamata ka yi wasa da wa’adin da ka yi ba. (Mis. 20:25) Idan muka ƙasa cika alkawarin da muka yi wa Jehobah, za mu iya samun mummunar sakamako. (M. Wa. 5:6) Don haka, bari dukanmu da farin ciki mu ‘raira yabo ga sunan Jehobah, domin mu cika wa’adodinmu kowace rana.’Zab. 61:8.

^ sakin layi na 7 Hannatu ta yi alkawari cewa ɗan da za ta haifa zai zama Ba-nazari har ƙarshen ransa, wato zai yi wa Jehobah tsarkakkiyar hidima.Lit. Lis. 6:2, 5, 8.

^ sakin layi na 13 Matakan da dattawa suka ɗauka kafin mutum ya cancanci yin baftisma yana nuna cewa ba yadda zai yiwu baftismar da muka yi ta zama banza.

^ sakin layi na 16 Ka duba shafuffuka na 219 zuwa 221 na littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah.”