Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Kana Kaunata Fiye da Wadannan?”

“Kana Kaunata Fiye da Wadannan?”

“Siman, ɗan Yohanna, kana ƙaunata fiye da waɗannan?”​—YOH. 21:15, New World Translation.

WAƘOƘI: 128, 45

1, 2. Me aka gaya wa Bitrus bayan sun kwana suna neman kifi?

ALMAJIRAN YESU guda bakwai sun kwana suna neman kifi a Tekun Galili, amma ba su kama ko ɗaya ba. Yesu da aka ta da daga mutuwa, ya hango su sai ya ce musu: “Ku jefa taru ga hannun dama na jirgi, kū samu. Suka jefa fa: yanzu kuwa suka kasa jawowa saboda yawan kifaye.”​—Yoh. 21:​1-6.

2 Bayan Yesu ya ba su abinci, sai ya juya ya kalli Siman Bitrus kuma ya ce: “Siman, ɗan Yohanna, kana ƙaunata fiye da waɗannan?” Me Yesu yake nufi sa’ad da ya yi wannan furucin? Abin da Yesu yake nufi shi ne, da yake Bitrus yana son kama kifi sosai, Yesu yana tambayar sa abin da ya fi so. Shin ya fi son kifin ko sana’ar kama kifin fiye da Yesu da koyarwarsa? Amma Bitrus ya ce: “I, Ubangiji; ka sani ina ƙaunar ka.” (Yoh. 21:​15, NW ) Babu shakka, Bitrus ya yi hakan. Ta yaya muka sani? Daga lokacin da ya yi wannan furucin, ya duƙufa a yin wa’azi kuma shi ne ya zama ginshiƙin ikilisiyar Kirista a ƙarni na farko.

3. Waɗanne abubuwan raba hankali ne ya kamata mu guje musu?

3 Wane darasi za mu koya daga tambayar da Yesu ya yi ma Bitrus? Bai kamata mu bar ƙaunar da muke yi wa Kristi ta yi sanyi kuma mu daina mai da hankali ga hidimarmu ga Jehobah ba. Yesu ya san cewa akwai abubuwan raba hankali da yawa a wannan duniyar. A kwatancinsa na mai shuki, Yesu ya ce wasu za su “ji zancen mulkin,” da farko amma daga baya, ‘ɗawainiyar duniya da ruɗin dukiya za su shaƙe maganar.’ (Mat. 13:​19-22; Mar. 4:19) Babu shakka, idan ba mu mai da hankali ba, dawainiyar duniya zai janye hankalinmu kuma ya hana mu yin ayyuka da suka shafi ibadarmu ga Jehobah. Shi ya sa Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wannan” duniyar.​—Luk. 21:34.

4. Me zai taimaka mana mu san ko muna ƙaunar Kristi sosai? (Ka duba hoton da ke shafi na 22.)

4 Kamar yadda labarin Bitrus da Yesu da muka ambata ɗazu ya nuna, za mu nuna muna ƙaunar Kristi idan muka saka aikin da ya ba mu a kan gaba. Ta yaya za mu tabbata cewa muna yin hakan babu fashi? Zai dace mu riƙa tambayar kanmu: ‘Wane abu ne na fi sakawa a kan gaba? Da ibada da shaƙatawa, wanne ne na fi mai da wa hankali?’ Don mu iya ba da amsa ga waɗannan tambayoyin, bari mu bincika wasu abubuwa uku da za su iya sa ƙaunar da muke yi wa Kristi ta yi sanyi. Me ke nan? Aiki da nishaɗi da kuma abin duniya.

KADA KA BAR AIKI YA HANA KA HIDIMAR JEHOBAH

5. Wane hakki ne Allah ya ba magidanta?

5 Kama kifi ne sana’ar da Bitrus yake yi don ya ciyar da kansa da kuma iyalinsa. Zai dace magidanta su fahimta cewa Allah ya ba su hakkin biyan bukatun iyalansu. (1 Tim. 5:8) Don haka, zai dace su yi aiki tuƙuru don su iya yin hakan. Amma a wannan zamanin, mutane da yawa sukan damu ainun game da aikinsu.

6. Wane irin fama ne ma’aikata suke yi?

6 Da yake mutane suna neman aiki sosai kuma babu aiki da yawa, wasu suna gasa don su sami aiki. Ban da haka ma, ana sa ma’aikata su riƙa yin aiki sa’o’i da yawa kuma a ba su albashi kaɗan. A yanzu, kamfanoni suna sa ma’aikatansu su riƙa aiki tuƙuru fiye da yadda ake yi a dā. Don haka, ma’aikatan sukan gaji kuma su yi ciwo. Wasu kuma suna damuwa ainun don suna ganin cewa idan ba su yi abin da shugabansu ya faɗa ba, za a kore su a aiki.

7, 8. (a) Wane ne kaɗai ya kamata mu bauta masa? (b) Wane darasi ne wani ɗan’uwa a Thailand ya koya game da aiki?

7 Da yake mu Kiristoci ne, ya kamata mu kasance da aminci ga Jehobah kaɗai ba wanda ya ɗauke mu aiki ba. (Luk. 10:27) Muna aiki ne kawai don mu sami abin biyan bukata da kuma abin da za mu tallafa wa kanmu da shi a hidimar da muke yi. Amma idan ba mu mai da hankali ba, aikinmu zai iya zama a kan gaba kuma mu yi banza da ibadarmu. Alal misali, wani ɗan’uwa a ƙasar Thailand ya ce: “Ina jin daɗin aikin gyara kwamfuta amma aikin na ɗaukan lokaci sosai, don haka ba na samun lokacin ibada. Na fahimci cewa idan ina son in saka Mulkin Allah a kan gaba, dole ne in nemi wani aiki.” Mene ne wannan ɗan’uwan ya yi?

8 Ya ce: “Na yi shekara ɗaya ina shiri, bayan haka, sai na soma sayar da ayis kirin. Da farko ba na samun ciniki a sana’ar, sai na soma yin sanyin gwiwa. Kuma idan na haɗu da waɗanda muka yi aikin gyarar kwamfuta tare, sai su riƙa dariya suna tambaya na dalilin da ya sa na bar aikin gyarar kwamfuta da ake zama a wurin da akwai iyakwandishan kuma na soma sayar da ayis kirin. Na yi addu’a ga Jehobah ya taimaka min in jimre don in riƙa mai da hankali ga ayyukan ibada. Ba da daɗewa ba, sai abubuwa suka canja kuma na sami kwastomomi da yawa kuma na ƙware a sana’ata. Ban da haka ma, a duk lokacin da na fito sayar da ayis kirin, sai na sayar gabaki ɗaya. A gaskiya, ina farin ciki da kuma jin daɗin sana’ata fiye da gyarar kwamfuta. Abu mafi muhimmanci kuma, na kusaci Jehobah.”​—Karanta Matta 5:6; Luka 11:28.

9. Ta yaya za mu ci gaba da kasancewa da ra’ayi mai kyau game da aiki?

9 Kalmar Allah ta ƙarfafa mu mu riƙa aiki sosai don hakan yana da amfani. (Mis. 12:14) Duk da haka, ɗan’uwan da aka ambata ɗazu ya fahimta cewa bai kamata mu bar aiki ya hana mu yin ibada ba. Yesu ya ce: “Ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abubuwa duka [abin biyan bukata] fa za a ƙara maku su.” (Mat. 6:33) Don mu tabbata cewa ba ma mai da hankali ga aikinmu ko sana’armu fiye da ibada, zai dace mu tambayi kanmu: ‘Ina jin daɗin aikin da nake yi kuma in yi banza da ayyukan ibada?’ Yin tunani ko bimbini a kan aikin albashi da ibada zai taimaka mana mu san abin da muka fi mai da wa hankali.

10. Wane darasi mai muhimmanci ne Yesu ya koya mana game da saka abubuwa masu muhimmanci a kan gaba?

10 Yesu ya kafa mana misalin abin da ya kamata mu saka a kan gaba. Akwai lokacin da Yesu ya ziyarci Maryamu da ’yar’uwarta Martha. Maryamu ta zauna tana sauraron Yesu amma Martha ta duƙufa wajen dafa abinci. Sai Martha ta gaya wa Yesu ya gaya wa Maryamu ta taimaka mata, amma Yesu ya ce: “Maryamu ta zaɓi abu mai kyau, ba kuwa za a karɓe mata ba.” (Luk. 10:​38-42, Littafi Mai Tsarki) Yesu ya koya wa Martha darasi mai muhimmanci. Wane darasi ke nan? Idan muna son mu nuna cewa muna ƙaunar Yesu da gaske, wajibi ne mu yi banza da abubuwan da za su janye hankalinmu daga ibada amma mu “zaɓi abu mai kyau,” wato mu mai da hankali ga abubuwan da suka fi muhimmanci.

YADDA YA KAMATA MU ƊAUKI NISHAƊI DA SHAƘATAWA

11. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya koyar game da hutu?

11 Saboda aiki da muke yi, a wasu lokuta muna bukatar hutu. Kalmar Allah ta ce: “Babu abin da ya fi ga mutum ya ci ya sha, ya ji wa ransa daɗi cikin aikinsa.” (M. Wa. 2:24) Yesu ma ya san muhimmancin hutu. Bayan mabiyansa sun yi wa’azi sosai, ya gaya musu cewa: “Ku zo da kanku waje ɗaya inda ba kowa, ku huta kaɗan.”​—Mar. 6:31, 32.

12. Me ya sa ya kamata mu yi hankali sa’ad da muke nishaɗi da kuma shaƙatawa? Ka ba da misali.

12 Babu shakka, nishaɗi da shaƙatawa suna da kyau. Amma, za su iya zama matsala idan hakan ne ya fi muhimmanci a rayuwarmu. A ƙarni na farko, mutane da yawa suna da halin “Bari mu ci mu sha, gama gobe za mu mutu.” (1 Kor. 15:32) A yau ma, mutane da yawa suna da irin wannan halin. Alal misali, shekarun baya, wani matashi a Turai ya soma halartan taro. Amma yana son nishaɗi sosai don haka ya daina yin tarayya da Shaidun Jehobah. Daga baya ya zo ya fahimci cewa nishaɗin da ya saka a kan gaba ya jawo masa matsaloli da yawa. Don haka, ya sake soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ya cancanci ya zama mai-shela. Bayan ya yi baftisma ya ce: “Da-na-sanin da nake yi shi ne cewa na ɓata lokaci da yawa don na shagala a yin nishaɗi kafin in san cewa bauta wa Jehobah ne ya fi nishaɗi sa mutum farin ciki.”

13. (a) Ka ba da misalin matsalolin da ke tattare da nishaɗi da kuma shaƙatawa. (b) Mene ne zai taimaka mana mu ɗauki nishaɗi da shaƙatawa yadda ya dace?

13 Muna jin daɗin nishaɗi da shaƙatawa don yana sa mu mu wartsake kuma mu huta. Amma don mu yi hakan, shin muna bukatar mu yi amfani da lokaci sosai ne? Ka yi la’akari da wannan kwatancin: Mutane da yawa suna son cin kek da alewa, amma mun san cewa idan muna cin waɗannan abubuwan koyaushe zai iya yi mana illa. Saboda haka, idan muna so mu kasance da lafiya muna bukatar mu riƙa cin abinci da yake da kyau, ko ba haka ba? Haka ma yake da irin nishaɗi da kuma shaƙatawar da muke so, za su iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Don mu kāre kanmu daga hakan, muna bukatar mu duƙufa da yin hidimar Jehobah. Ta yaya za mu san ko muna saka nishaɗi da shaƙatawa kan gaba da ibada? A cikin mako muna iya rubuta sa’o’in da muke yi muna yin abubuwan da suka shafi ibada, kamar su halartan taro da fita wa’azi da nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma ibada ta iyali. Bayan haka, za mu iya rubuta sa’o’in da muke yi wajen yin nishaɗi da shaƙatawa kamar su wasanni da kallon telibijin ko kuma yin wasan bidiyo. Shin wanne ne muka fi ɓata lokaci muna yi? Muna bukatar mu yi gyara ne?​—Karanta Afisawa 5:15, 16.

14. Mene ne zai taimaka mana mu zaɓi nishaɗin da ya dace?

14 Jehobah ya ba mu ’yancin zaɓa wa kanmu nishaɗi da muke so, ban da haka ma, magidanta suna iya zaɓa wa iyalinsu nishaɗi da ya jitu da ƙa’idodin Jehobah kuma ya ƙunshi ayyukan da suka dace. * Saboda nishaɗin da ya dace ‘kyauta ce [daga] Allah.’ (M. Wa. 3:​12, 13) Hakika, mun san cewa ra’ayin kowa game da nishaɗi ya bambanta sosai. (Gal. 6:​4, 5) Amma ko da wane irin nishaɗi ne muka zaɓa, bai kamata ya fi ibada muhimmanci ba. Yesu ya ce: “Wurin da dukiyarka ta ke, can zuciyarka za ta kasance kuma.” (Mat. 6:21) Don haka, ƙaunar da muke yi wa Yesu zai sa furucinmu da tunaninmu da kuma yadda muke yin abubuwa su nuna cewa muna sa Mulkin Allah a kan gaba fiye da kome.​—Filib. 1:9, 10.

YADDA ZA MU GUJI NEMAN KAYAN DUNIYA

15, 16. (a) Ta yaya son abin duniya zai iya zama wa Kirista tarko? (b) Wane umurni ne Yesu ya bayar game da abin duniya?

15 A yau, mutane suna ganin kamar dole ne sai sun sayi kayan da ake yayi da waya ko kwamfutar zamani, da dai sauran su. Don haka, kowane Kirista yana bukatar ya bincika kansa ta wajen yi ma kansa waɗannan tambayoyin: ‘Shin ina yin tunanin samun sabuwar motar da ake yayi ko kuma kayan yayi da har ba na samun lokacin da zan yi bincike don taro? Shin abubuwan yau da kullum da nake yi suna hana ni samun lokacin yin addu’a da kuma karanta Littafi Mai Tsarki?’ Idan muka gano cewa mun fi son abin duniya da Kristi, muna bukatar mu yi tunani a kan abin da Yesu ya ce, mu ‘tsare kanmu daga dukan ƙyashi.’ (Luk. 12:15) Me ya sa Yesu ya yi wannan gargaɗin?

16 Yesu ya ce, “ba wanda ke da iko shi bauta wa ubangiji biyu.” Bayan haka, ya ce: “Ba ku da iko ku bauta wa Allah da dukiya ba.” Me ya sa? Don “ubangiji biyu” ɗin kowannensu zai bukaci a bauta masa shi kaɗai. Shi ya sa Yesu ya ce, ‘ko ku ƙi ɗayan, ku ƙaunaci ɗayan’ ko kuma ‘ku lizimci ɗayan, ku rena ɗayan.’ (Mat. 6:24) Da yake dukanmu ajizai ne, muna bukatar mu ci gaba da gujewa “sha’awoyin jikinmu” wanda ya ƙunshi son abin duniya.​—Afis. 2:3.

17. (a) Me ya sa mutanen da suke son nishaɗi da abin duniya ba sa sanin yadda ya kamata su bi da su a rayuwarsu? (b) Mene ne zai taimaka mana mu guji son abin duniya?

17 Mutane da yawa suna son nishaɗi da kuma abin duniya, don haka ba sa sanin yadda ya kamata su bi da waɗannan abubuwan a rayuwarsu. Me ya sa? Saboda ba sa mai da hankali ga abubuwan da suka shafi ibadarsu ga Jehobah. (Karanta 1 Korintiyawa 2:14.) Don haka, ba su san abin da ya dace da wanda bai dace ba. (Ibran. 5:​11-14) Ƙari ga haka, son da suke yi wa abin duniya yana daɗa ƙaruwa shi ya sa kayan duniya ba ya isansu. (M. Wa. 5:10) Amma akwai wani abin da zai taimaka mana mu guje wa irin wannan tunanin. Me ke nan? Karanta Kalmar Allah koyaushe. (1 Bit. 2:2) Kamar yadda yin tunanin a kan Kalmar Allah ya taimaka wa Yesu ya yi tsayyaya da gwaji, haka ma bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu gujewa son abin duniya. (Mat. 4:​8-10) Idan muna yin hakan, za mu nuna wa Yesu cewa muna ƙaunarsa fiye da kayan duniya.

Mene ne ka saka a kan gaba a rayuwarka? (Ka duba sakin layi na 18)

18. Mene ne ka ƙuduri aniyar yi?

18 A lokacin da Yesu ya tambayi Bitrus: “Kana ƙaunata fiye da waɗannan?” Yesu yana son ya nuna wa Bitrus abin da ya kamata ya saka a kan gaba a rayuwarsa, wato hidimar Allah. Bitrus wanda sunansa yake nufin “Dutse,” ya yi rayuwar da ta jitu da sunansa, don ya nuna ƙarfin hali kamar dutse. (A. M. 4:​5-20) A yau, mu ma mun ƙuduri niyyar ci gaba da ƙaunar Kristi, don haka, muna ɗaukan nishaɗi da aiki da kuma kayan duniya yadda ya kamata. Bari zaɓin da muke yi a rayuwa ya nuna cewa mun amince da abin da Bitrus ya faɗa wa Yesu cewa: “Ubangiji; ka sani ina ƙaunarka.”

^ sakin layi na 14 Ka duba talifin nan “Nishaɗin Da Kake Yi Yana Amfane Ka Kuwa?” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2011, shafuffuka na 9-12, sakin layi na 6-15.