Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kana Shirye Ka Jira Jehobah da Hakuri?

Kana Shirye Ka Jira Jehobah da Hakuri?

“Ku kuma sai ku yi haƙuri.”​—YAƘ. 5:8.

WAƘOƘI: 78, 139

1, 2. (a) Me zai iya sa mu yi tambayar nan: “Har yaushe?” (b) Me ya sa misalan bayin Allah a dā za su iya ƙarfafa mu?

ANNABI Ishaya da Habakkuk sun taɓa yin wannan tambayar: “Har yaushe?” (Isha. 6:11; Hab. 1:2) Sa’ad da Sarki Dauda yake rubuta Zabura ta 13 ya yi tambayar nan: “Har yaushe” sau huɗu. (Zab. 13:​1, 2) Ban da haka ma, Yesu ya yi wannan tambayar sa’ad da yake tattaunawa da wasu mutane marasa bangaskiya. (Mat. 17:17) Saboda haka, bai kamata mu ma mu yi mamaki ba idan muka yi wannan tambayar.

2 Me zai iya sa mu yi wannan tambayar: “Har yaushe?” Wataƙila an taɓa yi mana rashin adalci. Ko kuma wataƙila muna fama da tsufa ko ciwo ko kuma matsalolin da mutane suke fama da su a waɗannan kwanaki na ƙarshe. (2 Tim. 3:1) Ko kuma halayen mutanen da muke zama da su yana ɓata mana rai. Ko da wace irin matsala muke da shi, muna samun ƙarfafa sa’ad da muka tuna cewa bayin Jehobah a dā ma sun yi tambayar nan, “har yaushe?” Kuma Jehobah bai tsauta musu don sun yi hakan ba!

3. Mene ne zai iya taimaka mana sa’ad da muka sami kanmu a cikin tsaka mai wuya?

3 Mene ne zai iya taimaka mana sa’ad da muka sami kanmu a cikin tsaka mai wuya? An hure ɗan’uwan Yesu mai suna Yaƙub ya rubuta cewa: “Ku yi haƙuri fa, ’yan’uwa har zuwan Ubangiji.” (Yaƙ. 5:7) Babu shakka, dukanmu muna bukatar mu zama masu haƙuri. Amma mene ne za mu yi don mu kasance da wannan halin?

MENE NE YIN HAƘURI YA ƘUNSA?

4, 5. (a) Mene ne yin haƙuri ya ƙunsa? (b) Yaya almajiri Yaƙub ya kwatanta wani fannin haƙuri? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)

4 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ruhu mai tsarki ne yake sa mutum ya zama mai haƙuri. Kuma idan ba tare da taimakon Allah ba, ba za mu iya kasancewa da wannan halin yadda ya kamata ba. Halin nan haƙuri baiwa ce da Allah ya ba mu. Kuma idan mu masu haƙuri ne, hakan zai taimaka mana mu yi ƙaunar Allah sosai. Ban da haka ma, idan muna haƙuri za mu riƙa ƙaunar ’yan’uwanmu sosai. Haƙuri yakan sa a kasance da zumunci amma rashin haƙuri yakan ɓata zumunci. (1 Kor. 13:4; Gal. 5:22) Haƙuri ya ƙunshi wasu halayen da ya kamata Kiristoci su koya. Alal misali, haƙuri yana da alaƙa da jimrewa don yana taimaka mana mu daure sa’ad da muke shan wahala kuma mu zama da ra’ayin da ya dace. (Kol. 1:11; Yaƙ. 1:​3, 4) Ƙari ga haka, idan muna da haƙuri za mu iya jimre sa’ad da ake tsananta mana ba tare da yin ramako ba amma mu kasance da ƙarfin hali ko da me ya faru. Kuma Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu riƙa jira. An tattauna hakan a littafin Yaƙub 5:​7, 8. (Karanta.)

5 Me ya sa za mu kasance a shirye mu riƙa jiran Jehobah? Yaƙub ya kwatanta yanayinmu da na manomi. Ko da yake manomi yana aiki tuƙuru don ya yi shuki, ba shi da iko ya tsara yadda abin da ya shuka zai girma. Ba zai iya sa abin da ya shuka ya yi girma da sauri ba. Dole ne ya yi haƙuri kuma ya jira “amfanin ƙasa mai-tamani.” Hakazalika, akwai wasu abubuwan da ba za mu iya tsara su yadda muke so ba sai dai mu jira lokacin da Jehobah zai cika alkawarin da ya yi mana. (Mar. 13:​32, 33; A. M. 1:7) Kamar manomin nan, wajibi ne mu yi haƙuri kuma mu jira.

6. Wane darasi za mu iya koya daga misalin annabi Mikah?

6 Abubuwan da muke fuskanta a yau iri ɗaya ne da na mutanen zamanin annabi Mikah. Wannan annabin ya yi rayuwa ne a lokacin da wani mugun Sarki mai suna Ahaz yake sarauta kuma a lokacin ana rashin adalci sosai. Kuma mutanen da suke wurin suna yin “abin da ke mugu” ko mugunta da ƙwazo. (Karanta Mikah 7:​1-3.) Annabi Mikah ya fahimci cewa ba zai iya magance wannan matsalar ba. To, me zai yi yanzu? Ya ce: “Amma ni dai zan saurara ga Ubangiji [zan yi haƙuri sa’ad da nake jira]; zan jira Allah na cetona; Allahna za ya ji ni.” (Mi. 7:7) Kamar yadda ya faru a zamanin Mikah ya kamata mu ma mu “jira Allah.”

7. Me ya sa bai kamata mu yi zaman jiran Jehobah kawai ba?

7 Idan muna da bangaskiya kamar na Mikah za mu kasance a shirye mu ci gaba da jiran Jehobah. Kuma yanayinmu ba kamar na fursuna da aka sa shi dole ya jira hukuncin kisa ko da yake ba ya son hukuncin da za a yi masa ba. Mu muna jiran Jehobah da zuciya ɗaya don mun san cewa zai cika alkawarinsa na ba mu rai na har abada a daidai lokacin da ya dace! Don haka, muna ‘haƙuri da jimrewa tare da farin ciki.’ (Kol. 1:​11, 12) Amma Jehobah ba zai yi farin ciki ba idan sa’ad da muke jiransa muna gunaguni cewa ba ya aikatawa da sauri.​—Kol. 3:12.

MISALAN MUTANE DA SUKA YI ZAMAN JIRA

8. Me ya kamata mu tuna da shi sa’ad da muke tunani a kan misalan bayin Allah na dā?

8 Za mu kasance da ra’ayin da ya dace sa’ad da muke jira idan muka bincika labarin bayin Allah masu aminci na dā waɗanda suka jira Jehobah ya cika alkawarinsa. (Rom. 15:4) Sa’ad da kake tunani sosai a kan misalansu, bai kamata ka manta da irin dogon lokacin da suka yi suna jira da ra’ayin da suka kasance da shi sa’ad da suke jira da kuma albarka da suka samu don haƙurin da suka yi.

Ibrahim ya jira na tsawon lokaci kafin aka haifi jikokinsa Isuwa da Yakubu (Ka duba sakin layi na 9, 10)

9, 10. Har tsawo wane lokaci ne Ibrahim da Saratu suka jira Jehobah ya cika alkawarinsa?

9 Bari mu bincika labarin Ibrahim da matarsa Saratu. Su biyun suna cikin ‘waɗanda suka gāji alkawarai ta wurin bangaskiya da haƙuri.’ Littafi Mai Tsarki ya ce “bayan da [Ibrahim] ya jimre da haƙuri,” ya karɓi alkawarin da Jehobah ya yi masa cewa zai albarkace shi kuma ya sa zuriyarsa ta hayayyafa. (Ibran. 6:​12, 15) Me ya sa Ibrahim yake bukatar ya yi haƙuri? A taƙaice, zai ɗauki lokaci sosai kafin a cika alkawarin da aka yi masa. Alkawarin da Jehobah ya yi wa Ibrahim ya soma cika a 14 ga Nisan a shekara ta 1943 kafin haihuwar Yesu. A lokacin da shi da matarsa Saratu da kuma ’yan gidansa suka ketare Kogin Yufiretis kuma suka shiga Ƙasar Alkawari. Ibrahim ya jira har shekara 25 kafin ya haifi ɗansa Ishaku a shekara ta 1918 kafin haihuwar Yesu. Ban da haka ma, ya sake jira shekaru 60 kafin a haifi jikokinsa Isuwa da Yakubu a shekara ta 1858 kafin haihuwar Yesu.​—Ibran. 11:9.

10 Yaya faɗin ƙasar da Ibrahim ya gāda yake? Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘[Jehobah] ba ya kuwa ba shi gādo cikinta ba, ko misalin takin sawu: amma ya yi masa alkawari za ya ba shi ita abin mulki, har ga zuriyarsa daga bayansa, ko da yake ba shi da ɗa tukuna.’ (A. M. 7:5) Sai bayan shekaru 430 da Ibrahim ya ketare Kogin Yufiretis ne aka tsara zuriyarsa suka zama al’umma da za ta gāji ƙasar.​—Fit. 12:​40-42; Gal. 3:17.

11. Me ya sa Ibrahim ya jira Jehobah kuma wace albarka zai samu don haƙurin da ya yi?

11 Ibrahim yana da bangaskiya sosai shi ya sa ya jira Jehobah da zuciya ɗaya. (Karanta Ibraniyawa 11:​8-12.) Ibrahim ya kasance da ra’ayi mai kyau ko da yake Jehobah bai cika alkawarin da ya yi a zamaninsa ba. Babu shakka, Ibrahim zai yi farin ciki sosai idan aka ta da shi zuwa aljanna a duniya kuma ya ga yadda aka rubuta labarinsa da na zuriyarsa a cikin Littafi Mai Tsarki. * Ban da haka ma, zai yi farin ciki ya ga yadda alkawarin da aka masa cewa zuriyarsa za ta taimaka wa dukan mutane zai sa a cika nufin Jehobah! Kuma zai fahimci cewa yadda ya jira na dogon lokaci ne ya sa aka sami albarka.

12, 13. Me ya sa Yusufu yake bukatar ya zama mai haƙuri, kuma wane irin ra’ayi ne ya kasance da shi?

12 Yusufu tattaba kunnen Ibrahim ya jira Jehobah da zuciya ɗaya. Me ya faru da shi? An yi masa rashin adalci. Ta yaya? ’Yan’uwansa sun sayar da shi kuma ya zama bawa a lokacin da yake shekara 17. Bayan haka, sai aka masa sharri cewa ya so ya yi wa matar shugabansa fyaɗe kuma aka saka shi a fursuna. (Far. 39:​11-20; Zab. 105:​17, 18) Ko da yake shi mai adalci ne, ya sha wahala maimakon ya sami albarka. Amma bayan shekara 13 sai yanayinsa ya canja nan da nan. An sāke shi daga fursuna kuma ya zama mutum mafi girma na biyu a ƙasar Masar.​—Far. 41:​14, 37-43; A. M. 7:​9, 10.

13 Wannan rashin adalci da aka yi ma Yusufu ya sa shi fushi ne? Hakan ya sa shi ya daina amincewa da Jehobah ne? A’a. Me ya taimaka wa Yusufu ya jira da zuciya ɗaya? Bangaskiyarsa ce ga Jehobah. Don ya ga yadda Jehobah ya albarkace shi shi ya sa ya gaya wa ’yan’uwansa cewa: “Kada ku ji tsoro: ni maimakon Allah ne? Ku dai, kuka nufe ni da mugunta; amma Allah ya nufi alheri, domin shi sanya a yi ceton mutane da yawa, kamar yadda yake yau.” (Far. 50:​19, 20) Babu shakka, Yusufu ya fahimci cewa yadda ya jira na dogon lokaci ya sa ya sami albarka.

14, 15. (a) Wane darasi muka koya daga Dauda? (b) Me ya taimaka wa Dauda ya yi haƙuri sa’ad da yake jira?

14 Sarki Dauda ma ya sha wulaƙanci sosai. Ko da yake Jehobah ya zaɓe Dauda ya zama sarkin Isra’ila tun yana ƙarami, sai da ya yi shekaru 15 yana jira kafin ya zama sarki. (2 Sam. 2:​3, 4) Kuma a lokacin da yake jira, Sarki Saul yana nema ya kashe shi. * A sakamakon haka, Dauda ya yi gudun hijira zuwa wasu ƙasashe, kuma a wasu lokuta a kogwanni yake ɓuya. Ko da yake daga baya an kashe Saul a yaƙi, sai da Dauda ya jira na tsawon shekaru bakwai kafin aka ba shi ikon yin sarauta bisa al’ummar Isra’ila.​—2 Sam. 5:​4, 5.

15 Me ya sa Dauda ya jira Jehobah? Mun sami amsar a zaburar da muka ambata ɗazu da ya tambayi Jehobah sau huɗu: “Har yaushe?” Sai ya ce: “Na dogara ga jinƙanka; zuciyata za ta yi murna cikin cetonka: Zan raira waƙa ga Ubangiji, gama ya kyauta mini.” (Zab. 13:​5, 6) Dauda ya dogara ga Jehobah kuma ya san zai yi masa jin ƙai. Ƙari ga haka, ya jira lokacin da Jehobah zai cece shi, ban da haka, ya tuna yadda Jehobah ya taimaka masa a dā. Babu shakka, Dauda ya san cewa idan ya jira, zai sami albarka.

Idan ya zo ga yin haƙuri, Jehobah ba ya bukatarmu mu yi wani abu da shi da kansa ba zai iya yi ba

16, 17. Ta yaya Jehobah da Yesu suka kafa mana misali mai kyau na kasancewa da haƙuri sa’ad da muke jira?

16 Idan ya zo ga yin haƙuri, Jehobah ba ya bukatarmu mu yi wani abu da shi da kansa ba ya so ya yi. Ya kafa mana misali mai kyau na kasancewa da haƙuri sa’ad da muke jira. (Karanta 2 Bitrus 3:9.) Jehobah ya yi dubban shekaru yana jira don a warware matsalar da Shaiɗan ya jawo a lambun Adnin. Yana haƙuri sa’ad da yake “sauraro” ko jiran lokacin da za a tsarkake sunansa. Kuma waɗanda suka yi haƙuri suna jiransa ma za su sami albarka sosai​—Isha. 30:18.

17 Yesu ma ya kasance da haƙuri sa’ad da yake jira. Ko da yake ya jimre sa’ad da yake duniya kuma ya ba da hadayar fansa a shekara ta 33 a zamaninmu, sai da ya jira har shekara ta 1914 kafin ya soma sarauta. (A. M. 2:​33-35; Ibran. 10:​12, 13) Ban da haka ma, sai bayan sarautar Yesu na shekaru dubu kafin a hallaka maƙiyansa gaba ɗaya. (1 Kor. 15:25) Ko da yake zai jira na dogon lokaci, amma muna da tabbaci cewa zai sami albarka.

ME ZAI TAIMAKA MANA?

18, 19. Me zai taimaka mana mu yi haƙuri sa’ad da muke jira?

18 Babu shakka, dukanmu muna bukatar mu kasance da ra’ayi mai kyau sa’ad da muke jira kuma mu yi haƙuri sa’ad da muke yin hakan. Amma me zai taimaka mana mu yi hakan? Ka yi addu’a Allah ya ba ka ruhu mai tsarki. Kuma ka riƙa tunawa cewa haƙuri yana cikin ’yar ruhu. (Afis. 3:16; 6:18; 1 Tas. 5:​17-19) Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka kasance da haƙuri sa’ad da yake jira.

19 Ban da haka ma, ya kamata mu tuna da abin da ya taimaka wa Ibrahim da Yusufu da kuma Dauda su yi haƙuri sa’ad da suke jiran alkawarin da Jehobah ya yi musu. Me ke nan? Bangaskiyarsu ce ga Jehobah da kuma ganin yadda ya taimaka musu. Ba su mai da hankali ga kansu da abubuwan da za su sa su farin ciki ba. Kuma idan muka yi tunani sosai a kan yadda yanayinsu ya canja daga baya, hakan zai taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace kuma mu yi haƙuri sa’ad da muke jira.

20. Me ya kamata mu ƙudiri aniyar yi?

20 Mun kuɗiri aniya cewa za mu jimre sa’ad da muke jira ko da muna fuskantar gwaji da kuma matsaloli. Kuma a wasu lokuta, za mu iya yin baƙin ciki kuma mu ce: “Har yaushe, ya Ubangiji?” (Isha. 6:11) Amma da taimakon ruhu mai tsarki dukanmu za mu iya mu yi magana kamar Irmiya cewa: ‘Ubangiji rabona ne, . . . Zan sa bege’ wato, in jira shi.​—Mak. 3:​21, 24.

^ sakin layi na 11 An rubuta labarin Ibrahim a surori guda 15 na littafin Farawa. Ban da haka ma, waɗanda suka rubuta Nassosin Hellenanci na Kirista sun ambaci Ibrahim fiye da sau 70.

^ sakin layi na 14 Ko da yake Jehobah ya ƙi Sarki Saul bayan da ya yi sarauta na shekaru biyu, Jehobah ya bar shi ya yi sarauta har na tsawon shekaru 38.​—1 Sam. 13:1; A. M. 13:21.