Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Salama ta Allah ta Fi Ganewar Dan Adam”

“Salama ta Allah ta Fi Ganewar Dan Adam”

“Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku.”​—FILIB. 4:7.

WAƘOƘI: 76, 141

1, 2. Waɗanne abubuwa ne suka faru a Filibi da ya sa aka saka Bulus da Sila a kurkuku? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

KA YI la’akari da wannan labarin. An kama Bulus da Sila kuma aka saka su a fursuna a Filibi. An ɗaure ƙafafunsu kuma jikinsu yana musu ciwo don irin dūkan tsiya da aka musu. (A. M. 16:​23, 24) Kafin hakan ya faru, an kai Bulus da Sila kasuwa don a yi musu tambayoyi a gaban jama’a. A wurin aka yayyage tufafinsu kuma aka musu dukan tsiya. (A. M. 16:​16-22) Hakan rashin adalci ne sosai don Bulus ɗan ƙasar Roma ne kuma bai kamata su masa irin wannan wulaƙancin ba. *

2 Wataƙila Bulus ya yi ta tunanin abin da ya faru da shi a wannan ranar sa’ad da yake kurkuku. Ban da haka ma, ya yi ta tunanin mutanen Filibi. Me ya sa? Don ba su da majami’ar Yahudawa a birnin kamar wasu biranen da ya je. Yahudawan suna fita ne waje su riƙa taro a bakin wani kogi. (A. M. 16:​13, 14) Me ya sa? Ko don wataƙila babu Yahudawa maza goma da ake bukata kafin a sami majami’a ne? Mutanen da suke zama a Filibi suna alfahari cewa su ’yan ƙasar Roma ne. (A. M. 16:21) Wataƙila shi ya sa suka ɗauka cewa tun da Bulus da Sila Yahudawa ne, babu yadda za a yi a ce su ’yan ƙasar Roma ne. Ko da ba mu tabbata da hakan ba, abin da muka sani shi ne saka su a fursuna da aka yi rashin adalci ne.

3. Me ya sa wataƙila Bulus ya kasa fahimtar dalilin da ya sa aka saka shi a fursuna, duk da haka wane irin ra’ayi ne ya kasance da shi?

3 Mai yiwuwa Bulus yana tunani a kan abubuwan da suka faru da shi watanni da suka shige. Yana wancan gefen Tekun Aegean a Asiya Ƙarama kuma ruhu mai tsarki ya hana shi yin wa’azi a wasu wurare a wurin. Kamar dai ruhu mai tsarki yana gaya masa ya je wa’azi a wani wuri dabam. (A. M. 16:​6, 7) A ina ke nan? Ya sami amsar wannan tambayar sa’ad da aka saukar masa da wahayi a lokacin da yake Taruwasa. A wahayin an gaya masa: “Ka ƙetaro zuwa Makidoniya.” Da ya fahimci abin da Jehobah yake so ya yi, sai nan da nan ya tafi Makidoniya. (Karanta Ayyukan Manzanni 16:​8-10.) Amma me ya faru? Da Bulus ya shigo Makidoniya, sai aka kama shi kuma aka saka shi a fursuna. Me ya sa Jehobah ya bar shi ya sha irin wannan wahalar? Yaushe za a sāke shi daga fursuna? Ko da yake Bulus ya yi waɗannan tambayoyin, amma hakan bai sa shi baƙin ciki ko ya daina kasancewa da bangaskiya ba. Shi da Sila suna ta “addu’a suna rera waƙa ga Allah.” (A. M. 16:25) Me ya taimaka musu? Salama ta Allah ce ta sa suka sami kwanciyar hankali.

4, 5. (a) Ta yaya yanayinmu zai iya zama ɗaya da na Bulus? (b) Yaya yanayin Bulus ya canja ba zato ba tsammani?

4 Kamar yadda ya faru da Bulus, wataƙila akwai wasu lokutan da ka ga cewa kana bin ja-gorancin ruhu mai tsarki amma sai ka ga cewa abubuwa ba sa faruwa yadda kake zato. Kuma ka tsinci kanka a cikin matsala sosai da ta sa yanayinka ya canja gabaki ɗaya. (M. Wa. 9:11) Wataƙila ka yi tunani a kan batun kuma ka yi mamakin dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale ka kake shan irin wannan wahalar. Me za ka yi don ka ci gaba da jimrewa da kuma dogara ga Jehobah? Bari mu bincika labarin Bulus da Sila kafin mu sami amsar wannan tambayar.

5 A lokacin da Bulus da Sila suke waƙa, sai abubuwa dabam-dabam da ba su yi zato ba suka faru. Me ke nan? An yi girgizar ƙasa kuma kofofin fursunan suka buɗe. Sarkokin da aka ɗaure fursunonin da su suka kwance. Da shugaban fursunonin yake son ya kashe kansa, sai Bulus ya hana shi. Wannan shugaban da iyalinsa duka suka yi baftisma. Da gari ya waye, sai alƙalan suka aiki mutane su sāki Bulus da Sila kuma suka gaya musu su bar birnin nan da nan. Da ’yan majalisa suka gane cewa sun yi kuskure wajen saka Bulus da Sila a kurkuku don su ’yan ƙasar Roma ne, sai suka raka su har ƙofar birnin. Amma Bulus da Sila sun je sun yi ban kwana da Lydia wadda ta yi baftisma ba da daɗewa ba. Ban da haka ma, sun yi amfani da wannan zarafin don su ƙarfafa ’yan’uwansu. (A. M. 16:​26-40) Nan da nan yanayinsu ya canja ba zato ba tsammani!

TA FI GABAN GANEWAR ƊAN ADAM

6. Mene ne za mu bincika yanzu?

6 Waɗanne darussa ne muka koya daga abubuwan da suka faru? Mun koya cewa Jehobah zai iya yin abubuwan da ba mu yi zato ba. Saboda haka, sa’ad da muke shan wahala, bai kamata mu damu ainun ba. Kuma manzo Bulus bai manta da wannan darasin ba shi ya sa ya rubuta wa mutanen Filibi wasiƙa game da damuwa ainun da kuma salama ta Allah. Bari mu bincika furucin Bulus da ke Filibiyawa 4:​6, 7. (Karanta.) Bayan haka, za mu tattauna wasu labaran Littafi Mai Tsarki na yadda Jehobah ya yi wasu abubuwan da mutane ba su yi zatonsa ba. Sai kuma mu kammala da bincika yadda ‘salama ta Allah’ take taimaka mana mu jimre da kuma dogara ga Jehobah.

7. Wane darasi ne Bulus ya koyar a wasiƙar da ya rubuta wa ’yan’uwa a Filibi, kuma wane darasi muka koya daga wasiƙarsa?

7 Babu shakka, sa’ad da ’yan’uwa da ke Filibi suka karanta wasiƙar da Bulus ya rubuta musu, sun tuna da irin wulaƙancin da aka yi masa da kuma yadda Jehobah ya ɗauki mataki a hanyar da ba su yi zatonsa ba. Wane darasi ne Bulus yake so ya koya musu? Darasin shi ne: Bai kamata su riƙa damuwa ainun ba. Idan ka yi addu’a, za ka sami salama kuwa ta Allah. Amma ka lura cewa salama ta Allah ta fi ganewar ɗan Adam. Me hakan yake nufi? Wasu mafassara sun fassara wannan furucin cewa “ta fi dukan abin da muke mafarkinsa” ko kuma “ta fi dukan shawarwarin mutum.” Abin da Manzo Bulus yake nufi shi ne ‘salama ta Allah’ ta fi duk wani abin da muke tunaninsa daraja. Ko da yake a wasu lokuta sa’ad da muke shan wahala, za mu ga kamar ba mu da mafita. Amma Jehobah zai taimaka mana kuma zai iya yin abubuwan da ba mu yi zatonsu ba.​—Karanta 2 Bitrus 2:9.

8, 9. (a) Wace albarka aka samu duk da rashin adalcin da aka yi wa manzo Bulus a Filibi? (b) Me ya sa ya dace ’yan’uwa da ke Filibi su ɗauki furucin Bulus da muhimmanci?

8 ’Yan’uwa da ke Filibi sun sami ƙarfafa sosai sa’ad da suka yi tunani a kan abubuwan da suka faru shekaru goma da suka shige. Abin da manzo Bulus ya rubuta gaskiya ne. Saboda rashin adalci da Jehobah ya bar mutanen su yi ne ya sa aka ‘yi kariyar bishara da tabbatar da ita.’ (Filib. 1:​7, Littafi Mai Tsarki) Don haka, waɗannan alƙalan ba za su riƙa tsananta wa ’yan’uwa a sabuwar ikilisiyar Kirista da aka kafa a birnin ba gaira ba dalili ba. Wataƙila don Bulus ya faɗa cewa shi ɗan Roma ne ya sa abokin aikinsa Luka ya ci gaba da hidima a Filibi bayan da Bulus da Sila suka bar wurin. Kuma Luka ya taimaka wa ’yan’uwa a wannan sabuwar ikilisiya da aka kafa.

9 Babu shakka, sa’ad da ’yan’uwa a Filibi suka karanta wasiƙar Bulus, sun san cewa ba ra’ayinsa ya rubuta a wasiƙar ba. Ko da yake Bulus ya sha wahala sosai, ya nuna cewa yana da ‘salama ta Allah.’ Bulus yana tsare a Roma a wani gida a lokacin da ya rubuta wannan wasiƙar. Duk da haka, ya nuna cewa har ila yana da ‘salama ta Allah.’​—Filib. 1:​12-14; 4:​7, 11, 22.

“KADA KU YI ALHINI CIKIN KOWANE ABU”

10, 11. Me ya kamata mu yi sa’ad da muke fuskantar matsala, kuma me ya kamata mu yi zatonsa?

10 Me zai taimaka mana kada mu riƙa yin alhini amma mu kasance da ‘salama ta Allah’? Wasiƙar da Bulus ya rubuta wa ’yan’uwa a Filibi ya nuna cewa addu’a ita ce za ta taimaka mana mu daina damuwa ainun. Saboda haka, sa’ad da muke shan wahala, ya kamata mu yi addu’a. (Karanta 1 Bitrus 5:​6, 7.) Kuma idan muna yin addu’ar ya kamata mu kasance da bangaskiya cewa Jehobah yana kulawa da mu. Ban da haka ma, ya kamata mu yi addu’a “tare da godiya” muna tuna da yadda Jehobah yake yi mana albarka. A ƙarshe, bai kamata mu manta cewa Jehobah zai iya “aikata ƙwarai da gaske gaba da dukan abin da muke roƙo ko tsammani” ba.​—Afis. 3:20.

11 Kamar yadda ya faru da Bulus da Sila, mu ma za mu iya shan mamaki a kan yadda Jehobah yake yin abubuwa. Ba zai iya zama wani abu da ya taka kara ya ƙarya ba, amma kuma shi ne abin da muke bukata. (1 Kor. 10:13) Hakan ba ya nufin cewa za mu naɗe hannu mu zauna kawai muna jira Jehobah ya gyara yanayin ko kuma ya magance matsalar da muke fuskanta. A maimakon haka, muna bukatar mu riƙa yin abubuwan da suka jitu da addu’o’inmu. (Rom. 12:11) Don Jehobah ya albarkace mu, ya kamata yadda muke yin abubuwa ya nuna cewa mu masu gaskiya ne. Amma bai kamata mu manta cewa Jehobah zai iya yin fiye da abin da muka roƙa ko kuma zata zai yi ba. A wasu lokuta zai yi abin da mutane ba su taɓa tsammani ba. Bari mu bincika wasu labaran Littafi Mai Tsarki da za su sa mu riƙa dogara ga Jehobah cewa zai iya yin abubuwan da ba mu taɓa tsammani ba.

WASU ABUBUWAN DA JEHOBAH YA YI DA BA A ZATA BA

12. (a) Mene ne Sarki Hezekiya ya yi sa’ad da Sennakerib Sarkin Assuriya yake masa barazana? (b) Wane darasi muka koya daga yadda Jehobah ya magance matsalar?

12 Muna da labarai da yawa a Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda Jehobah ya yi abubuwan da ba a yi tsammaninsu ba. A lokacin da Sarki Hezekiya yake sarauta a Yahuda, Sarkin Assuriya mai suna Sennakerib ya kai hari kuma ya kwace dukan biranen amma ban da Urushalima. (2 Sar. 18:​1-3, 13) Bayan haka, sai Sennakerib ya shirya zai kai wa Urushalima hari. Wane mataki ne Sarki Hezekiya zai ɗauka? Ya yi addu’a kuma ya nemi shawara daga Ishaya wani annabin Jehobah. (2 Sar. 19:​5, 15-20) Ban da haka ma, Hezekiya ya yi basira ta wurin biyan taran da Sennakerib ya ce ya biya. (2 Sar. 18:​14, 15) A ƙarshe, sai Hezekiya ya soma shiri don ya kai hari. (2 Laba. 32:​2-4) Amma ta yaya aka magance matsalar? Jehobah ya aiko da mala’ika ɗaya wanda ya hallaka sojojin Sennakerib guda dubu 185,000 a dare ɗaya. A gaskiya, Hezekiya bai taɓa yin zato cewa Jehobah zai ɗauki wannan matakin ba.​—2 Sar. 19:35.

Wane darasi ne za mu koya daga labarin Yusufu?​—Far. 41:42 (Ka duba sakin layi na 13)

13. (a) Wane darasi muka koya daga labarin Yusufu? (b) Wane abu ne Saratu ba ta yi tsammanin zai faru da ita ba?

13 Bari mu bincika labarin matashin nan Yusufu ɗan Yakubu. A lokacin da yake fursuna a Masar, ya san cewa zai zama shugaba na biyu a ƙasar Masar ne? Ban da haka ma, ya san cewa Jehobah zai yi amfani da shi don ya ceci iyalinsa daga yunwa ne? (Far. 40:15; 41:​39-43; 50:20) Babu shakka, Jehobah ya yi abin da Yusufu bai yi zato cewa zai faru ba. Ban da haka ma, ka yi la’akari da labarin Saratu, kakar Yusufu. Shin tsohuwar nan ta san cewa Jehobah zai iya sa ta haifi ɗa ne baicin wanda ya baiwarta ta haifa mata? Saratu ba ta taɓa yin mafarki cewa za ta haifi Ishaku ba, amma ta haife shi.​—Far. 21:​1-3, 6, 7.

14. Wane tabbaci ne muke da shi game da Jehobah?

14 Bai kamata mu yi tsammanin cewa Jehobah zai kawar da dukan matsalolin da muke fuskanta kafin sabuwar duniya ta zo. Ban da haka ma, ba ma zato cewa Jehobah zai riƙa yi mana wasu mu’ujizai. Amma mun sani cewa Allah wanda ya taimaka wa bayinsa a dā shi ne Allahn da muke bauta masa. (Karanta Ishaya 43:​10-13.) Sanin hakan yana sa mu kasance da bangaskiya a gare shi. Kuma mun san cewa zai iya taimaka mana mu yi nufinsa da kyau. (2 Kor. 4:​7-9) Waɗanne darussa muka koya daga waɗannan labaran? Kamar yadda labarin Hezekiya da Yusufu da kuma Saratu suka nuna, Jehobah zai taimaka mana mu magance wata matsalar da muke ganin ba mu da mafita idan muka kasance da aminci a gare shi.

Jehobah zai taimaka mana mu magance wata matsalar da muke ganin ba mu da mafita idan muka kasance da aminci a gare shi

15. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da ‘salama ta Allah,’ kuma ta yaya hakan zai yiwu?

15 Mene ne zai taimaka mana mu kasance da ‘salama ta Allah’ ko da yake muna fuskantar matsaloli? Abin da zai taimaka mana shi ne kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah. Yesu Kristi wanda ya ba da ransa hadaya ne zai iya taimaka mana mu kasance da dangantaka mai kyau da Allah. Tanadin fansa da Jehobah ya yi yana ɗaya daga cikin abubuwan da ba mu yi tsammaninsu ba da Jehobah ya yi mana. Jehobah ya yi amfani da wannan fansar ya gafarta mana zunubanmu don mu bauta masa da kyau kuma mu kusace shi.​—Yoh. 14:6; Yaƙ. 4:8; 1 Bit. 3:21.

ZA TA TSARE ZUCIYARKU DA TUNANINKU

16. Wace albarka za mu samu idan muna da ‘salama ta Allah’? Ka ba da misali.

16 Wace albarka za mu samu idan muna da ‘salama ta Allah wadda ta fi gaban ganewa duka’? Littafi Mai Tsarki ya ce ‘za ta tsare zukatanmu da tunaninmu cikin Kristi Yesu.’ (Filib. 4:7) Ana amfani da kalmar nan “tsare” sa’ad ake nuna yadda sojoji suke tsaron birni a zamanin dā. Filibi yana ɗaya daga cikin irin waɗannan biranen. Mutanen wannan birnin suna barci da dare hankali kwance don sun san cewa sojoji suna gaɗinsu. Hakazalika, idan muna da ‘salama ta Allah’ hankalinmu zai zama a kwance don mun san cewa Jehobah yana kula da mu kuma yana son mu yi nasara. (1 Bit. 5:10) Hakan zai taimaka mana mu daina yin alhini kuma kada mu yi sanyin gwiwa.

17. Me zai taimaka mana kada mu firgita game da abin da zai faru a nan gaba?

17 Nan ba da daɗewa ba, za a yi ƙunci mai girma a duniya gabaki ɗaya. (Mat. 24:​21, 22) Ba mu san ainihin abin da zai faru da mu ba. Duk da haka, bai kamata mu riƙa damuwa ainun ba. Mun tabbata da Allahn da muke bauta masa ko da yake ba mu san takamaiman abin da zai yi ba. Labaran da muka bincika a baya sun nuna cewa ko da me ya faru, Jehobah yana yin nufinsa a kullum. Kuma a wasu lokuta yakan yi hakan a hanyoyin da ba mu taɓa yin tsammaninsu ba. A duk lokacin da Jehobah ya yi mana hakan, muna kasancewa da ‘salamarsa wadda ta fi gaban ganewa duka.’

^ sakin layi na 1 Kamar dai Sila ma ɗan ƙasar Roma ne.​—A. M. 16:37.