Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Darussan da Za Ka Koya Daga Wahayin Zakariya

Darussan da Za Ka Koya Daga Wahayin Zakariya

“Ku komo wurina, . . . ni ma in koma wurinku.”​—ZAK. 1:3.

WAƘOƘI: 120, 117

1-3. (a) Mene ne yanayin mutanen Jehobah sa’ad da Zakariya ya soma annabci? (b) Me ya sa Jehobah ya gaya wa mutanensa su ‘komo wurinsa’?

ZAKARIYA ya ga wani naɗaɗɗen littafi yana yawo a sama da wata mata da aka saka a cikin kwando da kuma mata biyu masu fukafukai suna yawo a sama kamar tsuntsu da ake kira shamuwa. Dukan wahayin nan suna cikin littafin Zakariya. (Zak. 5:​1, 7-9) Me ya sa Jehobah ya nuna wa annabinsa wannan wahayi mai ban mamaki? Mene ne yanayin Isra’ilawa a wannan lokacin? Ta yaya za mu amfana daga wannan wahayin a yau?

2 A shekara ta 537 kafin haihuwar Kristi, mutanen Jehobah suna farin ciki. Sun yi shekara 70 suna zaman bauta a Babila amma yanzu sun sami ’yanci. Sun yi farin ciki sosai don sun koma Urushalima kuma hakan ya sa suka saka ƙwazo don su sake gina haikalin kuma su bauta wa Jehobah a wurin. A shekara ta 536, sai suka kafa harsashi a haikalin. A wannan lokacin, mutanen suna ‘ihu mai-ƙarfi, aka ji amon kuma har daga nesa.’ (Ezra 3:​10-13) Amma, ba da daɗewa ba aka soma tsananta musu don aikin gini da suke yi. Sai Isra’ilawa suka yi sanyin gwiwa kuma suka daina gina haikalin amma suka mai da hankali ga gina nasu gidaje da kuma yin noma. Bayan shekara 16 ba a gama gina haikalin Jehobah ba. Don haka, ya kamata a tuna wa mutanen Allah cewa suna bukatar su koma ga Jehobah kuma su daina biɗan abubuwan kansu. Jehobah yana so su soma bauta masa da dukan zuciyarsu.

3 A shekara ta 520 kafin haihuwar Yesu, Jehobah ya tura annabinsa Zakariya ya taimaka wa mutanen su tuna dalilin da ya sa suka samu ’yanci daga Babila. Sunan Zakariya yana nufin “Jehobah Ya Tuna.” Ko da yake Isra’ilawan sun manta da abin da Jehobah ya yi musu, har ila Allah ya tuna da su. (Karanta Zakariya 1:​3, 4.) Jehobah ya yi alkawari zai taimaka musu su soma bauta masa kuma, amma ya kuma yi musu gargaɗi cewa wajibi ne su bauta masa da dukan zuciyarsu. Bari mu bincika wahayin Zakariya na shida da na bakwai. Za mu koya yadda Jehobah ya sa Isra’ilawa su kasance da ƙwazo. Ƙari ga haka, za mu ga darussan da za mu koya daga wannan wahayin.

HUKUNCIN DA ALLAH ZAI YI WA MASU SATA

4. Mene ne Zakariya ya gani a wahayi na shida, kuma me ya sa yadda aka yi rubutu a ko’ina a cikin littafin har da gefe-gefensa yake da muhimmanci? (Ka duba hoto na farko da ke shafi na 21.)

4 Sura ta biyar na littafin Zakariya ya soma da wahayi mai ban mamaki. (Karanta Zakariya 5:​1, 2.) Zakariya ya ga wani littafi da tsawonsa ya kai kusan ƙafa 30, faɗinsa kuma ƙafa 15 yana yawo a sama. Littafin yana buɗe kuma an rubuta wani saƙo a ciki har gefe-gefensa. (Zak. 5:3) A zamanin dā, mutane suna rubutu a gefe ɗaya kawai na naɗaɗɗen littafin. Amma wannan saƙon yana da muhimmanci sosai shi ya sa aka yi rubutu ko’ina har da gefe-gefen littafin.

Wajibi ne Kiristoci su guji yin kowace irin sata (Ka duba sakin layi na 5-7)

5, 6. Ta yaya Jehobah yake ɗaukan kowace irin sata?

5 Karanta Zakariya 5:​3, 4Dukan ’yan Adam za su ba da lissafi ga Jehobah don ayyukansu, musamman ma mutanensa da yake suna ɗauke da sunansa. Waɗanda suke ƙaunar Allah sun san cewa yin sata yana ɓata ‘sunan Allah.’ (Mis. 30:​8, 9) Wasu mutane suna iya gani cewa ba laifi ba ne mutum ya yi sata idan yana da dalili mai kyau na yin hakan. Amma ko da wane dalili ne ya sa mutum ya yi sata, wannan halin yana nuna cewa ba ya ɗaukaka Jehobah da sunansa da kuma dokarsa.

6 Shin ka lura cewa littafin Zakariya 5:​3, 4 ya ce “la’ana . . . ta shiga cikin gidan ɓarawo . . . za ta kuwa zauna a cikin tsakiyar gidansa, ta kuwa cinye shi”? Hakan ya nuna cewa Jehobah zai iya fallasa ko kuma ya shari’anta duk wani laifi da mutanensa suka yi. Ko da a ce mutumin da ya yi sata zai iya ɓoye wa ’yan sanda da shugaban wurin aikinsa da dattawa ko kuma iyayensa, ba zai iya ɓoye wa Jehobah ba. Allah zai tabbata cewa an fallasa duk wata sata da mutum ya yi. (Ibran. 4:13) Saboda haka, yana da kyau mu yi cuɗanya da mutanen da suke iya ƙoƙarinsu don su riƙa faɗin gaskiya a “dukan abu.”​—Ibran. 13:18.

7. Ta yaya za mu guji la’anar naɗaɗɗen littafi da ke yawo a sama?

7 Yin sata yana ɓata wa Jehobah rai. Abin daraja ne a gare mu mu yi rayuwa da ta jitu da ƙa’idodin Jehobah, kuma mu kasance da hali mai kyau da ba zai ɓata sunansa ba. Ta yin hakan, za mu guji hukuncin Jehobah a kan mutanen da ba sa yi masa biyayya da ganga.

KA RIƘA CIKA ALKAWARINKA “KOWACE RANA”

8-10. (a) Mece ce rantsuwa? (b) Wane alkawari ne Sarki Zedekiya ya kasa cikawa?

8 Naɗaɗɗen littafin ya kuma idar da saƙo ga waɗanda suke ‘rantsuwa da sunan Allah.’ (Zak. 5:4) Rantsuwa tana nufin cewa abin da mutum ya faɗa gaskiya ne ko kuma yin alkawari ne cewa mutum zai yi wani abu ko kuma ba zai yi ba.

9 Ba abin wasa ba ne mutum ya yi rantsuwa da sunan Jehobah. Mun san hakan daga abin da ya faru da Zedekiya, sarki na ƙarshe a Urushalima. Zedekiya ya yi rantsuwa da sunan Jehobah cewa zai riƙa yin biyayya ga sarkin Babila. Amma, Zedekiya bai cika alkawarinsa ba. Saboda haka, Jehobah ya ce: “Na rantse da raina, . . . Hakika a wurin nan da sarki yake zaune wanda ya sarautar da shi, shi wanda rantsuwarsa ya rena, ya warware alkawarinsa kuma, tare da shi a tsakiyar Babila [Zedekiya] za ya mutu.”​—Ezek. 17:16.

10 Sarki Zedekiya ya yi rantsuwa da sunan Jehobah, kuma Jehobah yana so Zedekiya ya cika alkawarinsa. (2 Laba. 36:13) Maimakon ya yi hakan, sai ya nemi taimakon Masar don ya sami ’yanci daga Babila. Duk da haka, Masar ba ta iya taimaka masa ba.​—Ezek. 17:​11-15, 17, 18.

11, 12. (a) Wane alkawari mafi muhimmanci muka yi? (b) Ta yaya keɓe kai zai shafi ayyukanmu na yau da kullum?

11 Jehobah yana jin alkawarin da muka yi. Yana ɗaukan alkawarin da muka yi da muhimmanci, kuma wajibi ne mu cika alkawarin idan muna so mu faranta masa rai. (Zab. 76:11) Alkawari mafi muhimmanci da muka yi shi ne sa’ad da muka keɓe kanmu ga Jehobah. Sa’ad da muka yi hakan, mun yi alkawari cewa za mu bauta masa a kowane yanayin da muka sami kanmu.

12 Ta yaya za mu cika alkawarin da muka yi sa’ad da muka keɓe kanmu ga Jehobah? Idan muna jimre kowace jaraba da muke fuskanta, hakan zai nuna cewa muna ɗaukan alkawarin da muka yi na yabon Jehobah a “kowace rana” da muhimmanci. (Zab. 61:8) Alal misali, mene ne za ka yi idan wani a wurin aikinka ko kuma a makaranta ya soma kwarkwasa da kai? Shin za ka ƙi yin hakan kuma ka nuna cewa kana ‘ji daɗin tafarkun’ Jehobah? (Mis. 23:26) Idan kana zama a iyalin da wasu ba sa bauta wa Jehobah, shin kana neman taimakon Jehobah don ka kasance da aminci ko a lokacin da babu wanda yake ƙoƙarin yin hakan a wurin da kake? Shin kana addu’a kullum ga Jehobah, kana gode masa don yadda yake ƙaunarmu da kuma yi mana ja-goranci? Shin kana keɓe lokaci don karanta Littafi Mai Tsarki kullum? Ballantana ma, mun yi alkawari cewa za mu riƙa yin waɗannan abubuwa sa’ad da muka keɓe kanmu. Idan muka yi wa Jehobah biyayya muna nuna masa cewa muna ƙaunarsa kuma mun ba da ranmu a gare shi. Bauta wa Jehobah ya zama salon rayuwarmu ba wai muna yin hakan kawai ba. Ƙari ga haka, domin muna da aminci ga Jehobah, ya yi mana alkawari cewa za mu more rayuwa a nan gaba.​—K. Sha. 10:​12, 13.

13. Wane darasi za mu koya daga wahayi na shida da Zakariya ya yi?

13 Wahayi na shida da Zakariya ya gani ya taimaka mana mu fahimci cewa bai kamata duk wani bawan Jehobah ya yi sata ko ya yi alkawari kuma ya yi rantsuwa a kan abin da ba zai yi ba. Mun sake fahimta cewa duk da ajizancin Isra’ilawa, Jehobah ya cika alkawarinsa kuma bai ƙyale su ba. Ya fahimci abin da suka fuskanta sa’ad da magabtansu suka kewaye su. Ƙari ga haka, ya kafa mana misali mai kyau ta wurin cika alkawarin da ya yi mana kuma zai taimaka mana mu riƙa cika namu alkawarin. Hanya ɗaya da ya yi mana hakan ita ce ta wurin tabbatar mana da cewa wata rana, zai kawar da mugunta a ko’ina a duniya. Annabcin Zakariya na gaba ya tabbatar da hakan.

JEHOBAH YA KAWAR DA MUGUNTA

14, 15. (a) Mene ne Zakariya ya gani a wahayi na bakwai? (Ka duba hoto na 2 da ke shafi na 21.) (b) Mene ne matar da ke cikin kwando take wakilta, kuma me ya sa aka saka ta a wurin?

14 Bayan da Zakariya ya ga wani littafi na yawo a sama, sai mala’ika ya gaya masa ya “duba” sama. Me zai gani a wannan wahayi na bakwai? Zakariya ya ga wani kwando da ake kira epha yana fitowa. (Karanta Zakariya 5:​5-8.) Wannan kwandon yana da murfin “darma.” Sa’ad da aka buɗe kwandon, sai Zakariya ya ga wata mata tana ‘zaune a ciki.’ Mala’ikan ya bayyana cewa mata da ke cikin kwandon “Mugunta” ce. Ka yi tunanin irin tsoron da Zakariya ya ji sa’ad da ya ga matar tana ƙoƙari ta fito daga cikin kwandon! Sai mala’ikan ya yi sauri ya tura matar ciki kuma ya rufe kwandon da murfi mai nauyi. Mene ne wannan yake nufi?

15 Wannan wahayin yana nuna cewa Jehobah zai kawar da masu mugunta tsakanin mutanensa. Idan Jehobah ya ga abin da bai dace ba, zai aikata nan da nan don ya kawar da shi. (1 Kor. 5:13) Mala’ikan ya tabbatar mana da hakan ta wajen rufe kwandon da murfi mai nauyi.

Jehobah ya yi alkawari cewa zai sa bautarsa ta kasance da tsabta (Ka duba sakin layi na 16-18)

16. (a) Mene ne Zakariya ya gani ya faru da kwandon da ake kira epha? (Ka duba hoto na 3 da ke shafi na 21.) (b) Ina ne mata masu fukafukai suka kai kwandon da ake kira epha?

16 Bayan haka, sai Zakariya ya ga mata biyu masu fukafukai masu ƙarfi kamar na shamuwa. (Karanta Zakariya 5:​9-11.) Waɗannan matan sun yi dabam da macen da ke cikin kwandon! Waɗannan matan sun yi amfani da fukafukansu masu ƙarfi suka ɗaga kwandon da “Mugunta” take ciki. A ina ne za su kai ta? Sun kai ta “ƙasar shinar,” ko Babila. Amma me ya sa suka kai kwandon Babila?

17, 18. (a) Me ya sa ya dace “Mugunta” ta kasance a ƙasar Shinar? (b) Ya kamata mu ƙuduri aniyar yin me game da mugunta?

17 Isra’ilawa na zamanin Zakariya sun fahimci dalilin da ya sa ya dace da aka kai Mugunta zuwa Shinar. Sun san cewa Babila birni ne cike da lalata da addinan ƙarya. Zakariya da Yahudawa da suka yi girma a wurin suna iya ƙoƙarinsu don kada su saka hannu a bautar arna. Saboda haka, wannan wahayin ya tabbatar musu cewa Jehobah zai sa bauta ta gaskiya ta kasance da tsabta!

18 Ban da haka ma, wahayin ya tuna wa Yahudawa cewa su ma suna bukatar su ci gaba da bauta wa Jehobah. Ba za a ƙyale masu mugunta su kasance a tsakanin mutanen Allah ba. A yau, Jehobah ya kawo mu cikin ƙungiyarsa mai tsabta, inda muke ganin yadda yake ƙaunarmu da kuma kāre mu. Kowannenmu yana da hakkin sa ƙungiyar Jehobah ta ci gaba da kasancewa da tsabta. Shin hakan yana motsa ka ka sa ‘gidanmu’ wato ƙungiyar Jehobah ya kasance da tsabta? Ba za a bar mugunta ta kasance ko kaɗan a tsakanin mutanen Jehobah ba.

MUTANE MASU TSABTA SUNA GIRMAMA JEHOBAH

19. Mene ne wahayin Zakariya mai ban mamaki yake nufi a yau?

19 Wahayi na shida da na bakwai da Zakariya ya gani gargaɗi ne sosai ga waɗanda suke mugunta a yau, don hakan ya nuna cewa Jehobah ba zai ƙyale mutane suna mugunta ba. Tun da yake mu bayinsa ne, wajibi ne mu tsani mugunta. Wannan wahayin ya sake tabbatar mana cewa idan mun faranta wa Ubanmu rai, ba zai yi mana la’ana ba amma zai kāre mu kuma ya albarkace mu. Dukan fama da muke yi don mu kasance da tsaba a wannan duniya da ke cike da mugunta ba zai zama a banza ba. Muna da tabbaci cewa za mu yi nasara da taimakon Jehobah! Amma ta yaya za mu kasance da tabbaci cewa za a ci gaba da bauta ta gaskiya a wannan duniya cike da mugunta? Wane tabbaci muke da shi cewa Jehobah zai kāre ƙungiyarsa yayin da ƙunci mai girma ya kusa? Za a tattauna waɗannan tambayoyi a talifi na gaba.