Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Karusa da Kambi Suna Kāre Ka

Karusa da Kambi Suna Kāre Ka

“Wannan za ya faru, idan kuka kiyaye muryar Ubangiji Allahnku da anniya.”​—ZAK. 6:15.

WAƘOƘI: 17, 136

1, 2. A ƙarshen wahayin Zakariya na bakwai, wane irin yanayi ne Yahudawa suke ciki?

AKWAI abubuwa da yawa da Zakariya zai yi tunani a kansu a ƙarshen wahayi na bakwai da ya gani. Jehobah ya yi alkawarin cewa zai hukunta mugaye saboda abubuwa da suke yi. Kuma babu shakka, wannan ya ƙarfafa Zakariya sosai, amma hakan bai faru ba tukun. Mutane sun ci gaba da nuna rashin gaskiya da kuma aikata mugunta. Kuma har ila ba a kammala ginin haikalin Urushalima ba. Me ya sa Yahudawa suka bar aikin da Jehobah ya ba su? Shin sun koma ƙasarsu ne don su biya bukatunsu?

2 Zakariya ya san cewa Yahudawan da suka koma Urushalima mutane masu bangaskiya ne, kuma su ne waɗanda Allah ya “taɓa” su domin su bar gidajensu da dukiyoyinsu a ƙasar Babila. (Ezra 1:​2, 3, 5, Littafi Mai Tsarki) Sun bar ƙasar da suka saba da ita kuma suka koma inda yawancinsu ba su taɓa gani ba. Da a ce ginin haikalin Jehobah ba shi da muhimmanci da ba su yi wannan tafiya mai nisan kilomita 1,600 ta hanya mai tuddai da gargada ba.

3, 4. Waɗanne matsaloli ne Yahudawan da suka zo Urushalima suka fuskanta?

3 Ka yi tunanin irin tafiyar da Yahudawan suka yi. Wataƙila sa’ad da Yahudawan suke tafiyar sun ɗau sa’o’i suna tunanin wurin da za su je. Sun ji labarin yadda Urushalima take da kyau a dā. Tsofaffi daga cikin su sun san yadda haikalin yake da kyau a dā. (Ezra 3:12) Da a ce kana tare da su sa’ad da suke yin tafiyar, yaya za ka ji idan ka hango Urushalima? Shin za ka yi fushi ne idan ka ga yadda ciyawa suka girma a gidajen da aka hallaka? Ko za ka soma kwatanta ganuwar Urushalima da aka hallaka da wanda yake Babila? Duk da yanayin Urushalima, Yahudawan ba su yi sanyin gwiwa ba. Don sun ga yadda Jehobah ya taimaka musu sa’ad da suke yin wannan tafiya mai nisa. Kuma abu na farko da suka yi a lokacin da suka iso Urushalima shi ne kafa inda za su riƙa yin hadaya ga Jehobah a wurin da haikalin yake a dā, kuma suka soma yin hakan kowace rana. (Ezra 3:​1, 2) Sun kasance da ƙwazo kuma kamar ba abin da zai sa su yin sanyin gwiwa.

4 Ban da gina haikalin, Isra’ilawa suna bukatar su gina biranensu. Kuma suna bukatar su gina gidajensu su yi gonaki kuma su riƙa ciyar da iyalinsu. (Ezra 2:70) Aikin da suke bukatar su yi kamar yana da girma sosai. Kuma nan ba da daɗewa ba, maƙiyansu suka soma tsananta musu don su hana su yin aikin. Kuma hakan ya ci gaba har shekaru 15, a sannu a hankali Yahudawan suka soma yin sanyin gwiwa. (Ezra 4:​1-4) Ban da haka ma, wata matsala ta sake tasowa, a shekara ta 522 kafin haihuwar Yesu, sarkin Fasiya ya hana su gina haikalin. Hakan ya sa kamar ba za a taɓa gina Urushalima ba.​—Ezra 4:​21-24.

5. Mene ne Jehobah ya yi game da sanyin gwiwar da mutanensa suka yi?

5 Jehobah ya san abin da mutanensa suke bukata. Allah ya nuna wa Zakariya wahayi na ƙarshe don ya nuna wa mutanen cewa yana ƙaunarsu kuma ya amince da su. Ban da haka ma, ya tabbatar wa Yahudawan cewa zai kāre su idan suka koma yin aikinsa. Jehobah ya faɗa musu game da ginin haikalin cewa: “Wannan za ya faru, idan kuka kiyaye muryar Ubangiji Allahnku da anniya.”​—Zak. 6:15.

RUNDUNAN MALA’IKU

6. (a) Ta yaya wahayin Zakariya na takwas ya soma? (Ka duba hoton da ke shafi na 26.) (b) Me ya sa dawakan suke da kala dabam-dabam?

6 Wahayin Zakariya na takwas yana iya zama wanda ya fi kasancewa da ban ƙarfafa. (Karanta Zakariya 6:​1-3.) Ka yi tunanin abin da Zakariya ya gani: A ‘tsakanin duwatsu biyu . . . na jan ƙarfe’ karusai guda huɗu suka fito kuma kamar suna shirye su je yaƙi. Kalar dawakan da suke jan karusan ya bambanta, kuma hakan zai taimaka don a san mahayan. Zakariya ya yi tambaya cewa: ‘Mene ne waɗannan?’ (Zak. 6:4) Mu ma za mu so mu sani don wahayin ya shafe mu.

[Bayanin da ke shafi na 28]

7, 8. (a) Mene ne duwatsu guda biyun suke wakilta? (b) Kuma me ya sa aka yi duwatsun da jan ƙarfe?

7 A Littafi Mai Tsarki duwatsu yana iya wakiltar mulki ko kuma gwamnati. A littafin Zakariya an ambaci duwatsu guda biyu kamar wanda Daniyel ya yi annabci a kai. Dutse guda yana wakiltar mulkin Jehobah da zai kasance har abada. Dutse na biyun kuma yana wakiltar gwamnatin da Yesu zai yi sarautar ta. (Dan. 2:​35, 45) Tun daga shekara ta 1914 da aka naɗa Yesu sarki, duwatsu biyun suna nan kuma suna da muhimmanci wajen cika nufin Allah game da duniya.

8 Me ya sa aka yi duwatsun da jan ƙarfe? Kamar zinariya, jan ƙarfe yana da muhimmanci sosai. Jehobah ya ba da umurni cewa a yi amfani da wannan ƙarfe mai walƙiya don a gina mazauni a haikalin da ke Urushalima. (Fit. 27:​1-3; 1 Sar. 7:​13-16) Hakan ya dace don waɗannan duwatsun jan ƙarfe na alama za su riƙa tuna mana yadda mulkin Jehobah da kuma na Yesu suke da muhimmanci don za su kāre ’yan Adam kuma su kawo albarka sosai.

9. Su wane ne mahayan karusan, kuma wane aiki aka ba su?

9 Yanzu bari mu tattauna game da karusan. Mene ne karusan da kuma mahayan su suke wakilta? Mahayan mala’iku ne wataƙila runduna dabam-dabam na mala’iku. (Karanta Zakariya 6:​5-8.) Kuma sun fito ne daga “gaban Ubangijin dukan duniya” don su yi wani aiki mai muhimmanci da ya ba su. Wane aiki ke nan? An tura karusan da kuma mahayansu zuwa yankuna dabam-dabam don su kula da su. Kuma aikin su shi ne su kāre mutanen Allah, musamman ma waɗanda suke zama a “ƙasar arewa” wato Babila. Jehobah zai tabbata cewa Babila ba za ta ƙara mayar da Isra’ilawa bayi ba. Babu shakka, hakan ya ƙarfafa masu gina haikalin a zamanin Zakariya. Kuma ba su damu da abin da maƙiyansu za su yi ba.

10. Ta yaya annabcin Zakariya game da karusa da kuma mahayan zai taimaka wa mutanen Allah a yau?

10 Kamar yadda Jehobah ya yi a zamanin Zakariya, har yanzu yana amfani da mala’ikunsa don ya kāre da kuma ƙarfafa mutanensa. (Mal. 3:6; Ibran. 1:​7, 14) Tun a shekara ta 1919 da bayin Allah suka daina zaman bauta a Babila Babba, maƙiyansu sun yi iya ƙoƙarinsu don a daina bauta ta gaskiya, amma hakan bai yiwu ba, bauta ta gaskiya sai yaɗuwa take yi. (R. Yoh. 18:4) Ba ma bukatar mu riƙa yin fargaba cewa ƙungiyar Jehobah za ta koma yin abubuwan da addinan ƙarya suke yi, don mala’iku suna kāre mu. (Zab. 34:7) Maimakon haka, muna bukatar mu kasance da tabbacin cewa bayin Jehobah a dukan faɗin duniya za su ci gaba da ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. Wahayin Zakariya zai taimaka mana mu fahimci cewa duwatsu guda biyun za su kāre mu.

11. Me ya sa ba ma bukatar mu ji tsoron harin da za a kawo wa mutanen Allah?

11 Nan ba da daɗewa ba, Shaiɗan zai yi amfani da masu sarauta don ya yi ƙoƙari ya hallaka mutanen Allah. (Ezek. 38:​2, 10-12; Dan. 11:​40, 44, 45; R. Yoh. 19:19) A annabcin Ezekiyel an bayyana cewa rundunar mayaƙa za su rufe duniya kamar hadari. Kuma za su kawo mana hari da zafin rai a kan dawakansu. (Ezek. 38:​15, 16) * Shin muna bukatar mu tsorata ne? A’a! Muna da rundunar Jehobah da suke goya mana baya. A lokacin ƙunci mai girma, mala’iku za su taimaka wa mutanen Allah kuma su hallaka mutanen da ba sa son mulkinsa. (2 Tas. 1:​7, 8) Babu shakka, wannan babban rana ce! Amma wane ne zai yi wa sojojin Jehobah shugabanci?

JEHOBAH YA NAƊA FIRIST YA ZAMA SARKI

12, 13. (a) Mene ne aka umurci Zakariya ya yi? (b) Ka bayyana yadda mutumin da sunansa Reshe yake wakiltar Yesu Kristi.

12 Zakariya ne kaɗai ya ga wahayi takwas ɗin. Bayan haka ya yi abin da wasu za su gani da zai ƙarfafa waɗanda suke gina haikalin. (Karanta Zakariya 6:​9-12.) An umurci Zakariya ya karɓi azurfa da kuma zinariya daga wurin Heldai da Tobijah da kuma Jedaiah, mutane uku da ba su daɗe da zuwa daga Babila ba. Jehobah ya umurci Zakariya ya yi “kambi” da abubuwan da ya karɓa daga wurin su. (Zak. 6:11) Shin Jehobah ya umurci Zakariya ya saka kambin a kan gwamna Zerubbabel wanda ya fito daga zuriyar Dauda ne? A’a! Babu shakka, mutanen da suke wurin sun yi mamaki da Zakariya ya saka wa Babban Firist Joshua kambin.

13 Amma saka wa Babban firist Joshua kambin, yana nufin cewa ya zama sarki ne? A’a. Joshua bai fito daga zuriyar Dauda ba, don haka bai cancanci zama sarki ba. Saboda haka, saka masa kambin annabci ne da ya nuna cewa a nan gaba za a naɗa sarkin da zai zama firist. Sunan wannan babban firist da za a naɗa sarki shi ne Reshe. Kuma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu Kristi ne wannan Reshe.​—Isha. 11:1; Mat. 2:23. *

14. Wane aiki ne Yesu zai yi a matsayin Sarki da kuma Babban Firist?

14 Yesu ne Sarki da kuma Babban Firist don shi ne shugaban rundunar Jehobah. Don haka, yana yin aiki da ƙwazo don mutane gabaki ɗaya su yi rayuwa a cikin kwanciyar hankali a duniya da ake ƙiyayya. (Irm. 23:​5, 6) Nan ba da daɗewa ba, Yesu zai hallaka al’ummai don yana goyon bayan mulkin Allah kuma yana kāre mutanen Jehobah. (R. Yoh. 17:​12-14; 19:​11, 14, 15) Amma kafin haka ya faru, Reshe yana da babban aikin da zai yi.

ZAI GINA HAIKALI

15, 16. (a) Yaya aka tsabtace bayin Allah a yau, kuma waye ne ya yi hakan? (b) Mene ne za a cim ma a ƙarshen Sarautar Shekara Dubu da Kristi zai yi?

15 Ban da zama Sarki da kuma Babban Firist, an ba wa Yesu aikin “gina haikalin Ubangiji.” (Karanta Zakariya 6:13.) A zamaninmu, aikin gina haikali da Yesu ya yi ta ƙunshi sa bayin Allah su sami ’yanci daga hannu Babila Babba, wato addinin ƙarya a shekara ta 1919. Ban da haka ma, ya naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” don ya yi shugabanci a ƙungiyar Jehobah ta duniya. (Mat. 24:45) Kuma Yesu ya ci gaba da tsabtace bayin Allah da kuma taimaka musu don su bauta wa Allah yadda ya dace.​—Mal. 3:​1-3.

16 A lokacin da Kristi zai yi Sarauta na Shekara Dubu, shi da waɗanda za su yi sarauta guda 144,000 a matsayinsu na sarakuna da firistoci ne za su sa mutane masu aminci su zama kamiltattu. Kuma bayan sun gama yin wannan aikin, masu bauta wa Jehobah ne kaɗai za su rage a duniyar nan. Kuma hakan zai sa a riƙa bauta ta gaskiya a dukan duniya!

KA SA HANNU A AIKIN GININ

17. Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa Yahudawa, kuma ta yaya wannan saƙon ya shafe su?

17 Amma ta yaya saƙon Zakariya ya shafi Yahudawa a zamaninsa? Jehobah ya yi musu alkawarin cewa zai taimaka da kuma kāre su don su kammala gina haikalin. Wannan alkawarin wataƙila ya ƙarfafa su sosai. Amma ta yaya mutane kalilan za su iya yin wannan aikin? Abin da Zakariya ya faɗa musu daga baya ya sa sun daina shakka. Ban da irin taimakon da mutane masu aminci kamar Heldai da Tobijah da kuma Jedaiah suka bayar, Allah ya gaya musu cewa mutane da yawa “za su zo su yi gini a cikin haikalin Ubangiji.” (Karanta Zakariya 6:15.) Saboda suna da tabbacin cewa Jehobah zai taimaka musu, Yahudawan suka soma aikin ginin duk da cewa an hana su yin hakan. Kuma nan ba da daɗewa ba Jehobah ya sa sarkin Fasiya ya kawar da takunkumi da ya saka kuma suka kammala haikalin a shekara ta 515. (Ezra 6:22; Zak. 4:​6, 7) Ƙari ga haka, abin da Jehobah ya faɗa ya nuna wani babban abun da zai faru a zamaninmu.

Jehobah ba zai taɓa mantawa da ƙaunar da muka nuna masa ba! (Ka duba sakin layi na 18, 19)

18. Ta yaya Zakariya 6:15 yake cika a zamaninmu?

18 A yau, miliyoyin mutane suna bauta wa Jehobah kuma suna ba da ‘wadatarsu’ wanda ya ƙunshi lokacinsu da ƙarfinsu da kuma dukiyarsu don su tallafa wa ƙungiyar Jehobah. (Mis. 3:9) Ta yaya za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana farin ciki don abubuwan da muke yi? Ka tuna cewa Heldai da Tobijah da kuma Jedaiah ne suka kawo abubuwan da Zakariya ya yi kambi da su. Kuma kambin ya zama abin da za a gani don “tunawa” da gudummawar da suka bayar. (Zak. 6:​14, Littafi Mai Tsarki) Saboda haka, Jehobah ba zai taɓa mantawa da aiki da kuma ƙaunar da muke yi masa ba. (Ibran. 6:10) Jehobah zai riƙa tunawa da abubuwan da muka yi.

 

19 Dukan abubuwan da aka cim ma a bauta ta gaskiya a wannan kwanaki na ƙarshe suna nuna albarkar Jehobah da kuma yadda Yesu yake yi mana ja-goranci. Muna farin cikin kasancewa a cikin ƙungiyar da ake ’yan’uwa suke da kwanciyar hankali kuma za su ci gaba da hakan har abada. Kuma nufin Jehobah game da bauta ta gaskiya zai “faru.” Don haka, kana bukatar ka riƙa farin ciki da abin da kake yi a ƙungiyar Jehobah kuma ka ci gaba da jin ‘muryar Ubangiji Allahnka da anniya.’ Idan kana yin hakan, Sarkinmu da kuma Babba Firist tare da mahayan dawakan za su kāre ka. Ka yi iya ƙoƙarinka don tallafa wa bauta ta gaskiya. Idan ka yi hakan, za ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai kāre ka har ƙarshen zamanin nan da kuma har abada!

^ sakin layi na 11 Don ƙarin bayani, ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Mayu, 2015, shafuffuka na 29-30.

^ sakin layi na 13 An samo kalmar nan Nazarat daga kalmar Ibrananci da take nufin “reshe.”

Har ila Jehobah yana amfani da mala’iku don ya kāre da kuma ƙarfafa mutanensa