Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Hasumiyar da Ta Nuna Gaskiyar Annabcin Littafi Mai Tsarki

Hasumiyar da Ta Nuna Gaskiyar Annabcin Littafi Mai Tsarki

A ROMA TA TSAKIYA A ƘASAR ITALIYA, AKWAI HASUMIYA DA MUTANE A DUK DUNIYA SUKE ZUWA GANI. HASUMIYAR TANA ƊAUKAKA WANI SHUGABAN ROMA MAI SUNA TITUS.

Hasumiyar tana da manyan ginshiƙai biyu kuma tana bayyana wani sanannen labari da ya faru a dā. Amma yawancin mutane ba su san alaƙar da ke tsakanin wannan hasumiyar da kuma Littafi Mai Tsarki ba. Wannan hasumiyar da ake kira Arch of Titus tana shaida gaskiyar wani annabci mai muhimmanci da ke Littafi Mai Tsarki.

AN ANNABTA HALAKAR WANI BIRNI

A ƙarni na farko, Romawa ne suke mulkan ƙasar Birtaniya da ƙasar Gaul (yanzu ana kiransa Faransa) har zuwa Masar, kuma waɗanda ke masarautar suna jin daɗin rayuwa sosai. Amma akwai wani yanki da mutanen suke yawan tada hankalin Romawa. Wannan yankin shi ne lardin Yahudiya.

Littafin nan Encyclopedia of Ancient Rome ya ce: “Babu wani yanki da Romawan suka tsana kamar Yahudiya kuma Yahudawan ma sun tsane su. Yahudawan ba sa son shugabannin wasu ƙasashe da ba sa daraja al’adunsu, Romawan kuma suna cin zalin Yahudawan sosai don taurin kansu.” Yahudawa da yawa sun yi begen cewa wani zai zo ya cece su daga hannun Romawan kuma ya sa su koma yin rayuwarsu kamar yadda suka saba yi a dā. Amma a shekara ta 33, Yesu Kristi ya ce za a halaka Urushalima gabaki ɗaya.

Yesu ya ce: “Lokaci yana zuwa da masu gāba da ku za su gina bango kewaye da ku su yi yaƙi da ku. Sojoji za su kewaye ku ta kowane gefe. Za su yi kaca-kaca da ku, su kuma kashe mutanenku duka. Ba ko dutse ɗaya na gine-ginenku da za a bari a kan ɗan’uwansa.”​—Luka 19:​43, 44.

Kalaman da Yesu ya yi sun ba wa almajiransa mamaki sosai. Bayan kwana biyu, sa’ad da almajiran suke kallon haikalin Urushalima, ɗaya da daga cikinsu ya ce masa: “Malam, dubi manyan duwatsun nan, da gine-ginen nan masu ban mamaki!” Hakika, wani bincike ya nuna cewa wasu duwatsun da aka gina haikalin da su suna da tsayi fiye da kafa 35 da faɗin kafa 16 da kuma dogon kafa 10. Amma Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: “Game da abubuwan nan da kuke kallo ne, to, lokaci yana zuwa da ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan’uwansa, kowannensu za a rushe shi.”​—Markus 13:1; Luka 21:6.

Yesu ya ƙara da cewa: “Sa’ad da kuka ga sojoji sun kewaye Urushalima, za ku sani cewa an yi kusa a rushe ta. To, sai waɗanda suke cikin yankin Yahudiya, su gudu zuwa cikin tuddai. Waɗanda suke a birni kuma su fita, waɗanda suke a ƙauye kuma kada su shiga birnin.” (Luka 21:​20, 21) Abin da Yesu ya faɗa ya faru da gaske kuwa?

AN HALAKA URUSHALIMA

Bayan shekara talatin da uku da Yesu ya furta kalaman nan, Yahudawa sun ci gaba da ƙin jinin Romawa. Sai wani babban ma’aikacin Roma mai suna Gessius Florus ya kwace wasu kuɗaɗen da ke haikalin Urushalima a shekara ta 66 bayan haihuwar Yesu. Hakan ya sa Yahudawan fushi sosai. Ba da daɗewa ba, sai wasu Yahudawa suka zo Urushalima kuma suka kashe wasu sojojin Romawa da ke wajen kuma suka sanar da ’yancin kansu.

Bayan aƙalla wata uku, sai wani gwamnan Roma mai suna Cestius Gallus ya ja-goranci sojojin Roma guda 30,000 don su yaƙi Yahudawan. Romawan ba su ɓata lokaci wajen kewaye birnin ba. Farat ɗaya, sai Romawan suka bar wurin. Yahudawan da suka yi tawaye sun yi murna sosai kuma suka bi su don su kashe su. Da Kiristocin suka ga hakan, sai suka bi umurnin Yesu, suka gudu zuwa duwatsun da ke hayin Kogin Urdun.​—Matiyu 24:​15, 16.

Bayan shekara ɗaya, sai Janar na sojojin Romawa mai suna Vespasian tare da ɗansa Titus suka sake koma Yahuda don su yi yaƙi da Yahudawa. Amma sai sarkin Romawa mai suna Nero ya mutu a shekara ta 68 bayan haihuwar Yesu. Hakan ya sa Janar Vespasian ya koma Roma don ya zama sarki. Vespasian ya bar ɗansa Titus ya ja-goranci sojoji 60,000 a yaƙi.

A watan Yuni na shekara ta 70 bayan haihuwar Yesu, Titus ya gaya wa sojojin su sare bishiyoyin da suke yankunan Yahudiya. Sun yi amfani da bishiyoyin sun yi katangar da tsayinsa ya kai kilomita 7 kuma suka kewaye bangon Urushalima da shi. A watan Satumba, Romawa sun ci Yahudawa da yaƙi kuma suka ƙone Urushalima da kuma haikalin gabaki ɗaya kamar yadda Yesu ya faɗa. (Luka 19:​43, 44) Wani bincike ya nuna cewa “mutanen da suka rasa rayukansu a Urushalima da wasu wurare a yankunan Yahudiya sun kai aƙalla 250,000 zuwa 500,000.”

ROMAWA SUN YI NASARA

A shekara ta 71 bayan haihuwar Yesu ne Titus ya koma birnin Roma a ƙasar Italiya kuma mutanen birnin suka marabce shi sosai. Mutanen birnin gabaki ɗaya sun yi gagarumin biki don wannan nasarar da suka yi.

Mutane sun yi mamakin ganin dukiyoyin da ake shigo da su birnin. Sun ji daɗin kallon abubuwan da sojojin suka kawo daga Urushalima. Kuma abubuwan nan su ne ƙananan jiragen ruwa da wasu hotunan da suke nuna abin da ya faru a yaƙin da kuma kayayyakin da aka kwaso daga haikalin da ke Urushalima.

Bayan mutuwar mahaifin Titus, wato Vespasian, Titus ya zama sarkin Roma a shekara ta 79 bayan haihuwar Yesu. Amma bayan shekaru biyu, sai ya yi mutuwar gaggawa. Ɗan’uwansa mai suna Domitian ne ya zama sarki bayan mutuwarsa kuma nan da nan ya gina wata Hasumiya don a riƙa ɗaukaka Titus.

HASUMIYAR A ZAMANINMU

Yadda Arch of Titus take a yau a Roma

A yau, dubban mutanen da suke zuwa Roma suna son hasumiyar da ake kira Arch of Titus sosai. Wasu suna ɗaukaka hasumiyar don yadda aka ƙera ta, wasu kuma hasumiyar tana sa su tuna da ikon da Daular Roma take da shi. Ƙari ga haka, hasumiyar tana sa wasu su tuna da yadda aka halaka Urushalima da kuma haikalinta.

Amma masu bincika Littafi Mai Tsarki suna ganin wannan hasumiyar da muhimmanci sosai. Hasumiyar tana tabbatar da gaskiyar annabce-annabcen da ke Littafi Mai Tsarki kuma tana nuna cewa Allah ne ya hure waɗanda suka rubuta su.​—2 Bitrus 1:​19-21.