Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka San Jehobah Kamar Nuhu da Daniyel da Kuma Ayuba?

Ka San Jehobah Kamar Nuhu da Daniyel da Kuma Ayuba?

“Miyagun mutane ba su fahimci hukunci ba: amma masu-biɗan Ubangiji suna fahimtar abu duka.”—MIS. 28:5.

WAƘOƘI: 126, 150

1-3. (a) Mene ne zai taimaka mana mu kasance da aminci a wannan kwanaki na ƙarshe? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

MUGAYEN mutane suna daɗa ƙaruwa kuma suna “tsiro kamar ciyawa.” (Zab. 92:7) Shi ya sa ba ma mamakin ganin cewa mutane da yawa ba sa bin dokokin Allah. Amma manzo Bulus ya shawarci Kiristoci cewa: “Ga wajen ƙeta ku zama jarirai, ga azanci kuwa ku zama cikakkun mutane.” (1 Kor. 14:20) Ta yaya za mu iya yin hakan?

2 Amsar tana nassin da aka ɗauko jigon wannan talifin. Ta ce: “Masu-biɗan Ubangiji suna fahimtar abu duka,” wato abubuwan da za su faranta wa Jehobah rai. (Mis. 28:5) Littafin Misalai 2:7, 9 ya ce Jehobah yana “ajiye ma masu-gaskiya sahihiyar hikima.” A sakamakon haka, masu gaskiya za su “fahimci adalci da shari’a, da daidaita, i, kowace hanya mai-kyau.”

3 Nuhu da Daniyel da kuma Ayuba sun kasance da wannan hikimar. (Ezek. 14:14) Bayin Allah ma a yau suna da irin wannan hikimar. Kai fa? Ka ‘fahimci abu duka,’ wato abubuwan da kake bukata don ka faranta wa Jehobah rai? Abu na musamman da kake bukata shi ne ka san Jehobah sosai. Saboda haka, bari mu tattauna (1) abin da ya taimaka wa Nuhu da Daniyel da kuma Ayuba su san Allah, (2) yadda sanin Allah ya taimaka musu, da kuma (3) yadda za mu iya kasancewa da irin bangaskiyarsu.

NUHU YA BAUTA WA ALLAH A MUGUWAR DUNIYA

4. Me ya taimaka wa Nuhu ya san Jehobah, kuma yaya ya amfana daga sanin Allah?

4 Yadda Nuhu ya san Jehobah. Tun zamanin dā, da akwai abubuwa uku da suke taimaka wa bayin Allah su san shi sosai. Na ɗaya, sun lura da halittun Allah. Na biyu, sun yin koyi da bayin Allah. Kuma na uku, sun ga yadda Allah ya albarkace su don sun bi dokokinsa. (Isha. 48:18) Babu shakka, ta wajen lura da halittun Allah, Nuhu ya ga cewa Jehobah yana wanzuwa da gaske. Ƙari ga haka, ya koyi cewa Allah yana da halaye masu kyau kamar “ikonsa madawwami da Allahntakarsa.” (Rom. 1:20) A sakamako haka, Nuhu ya gaskata da wanzuwar Allah kuma ya kasance da bangaskiya sosai.

5. Ta yaya Nuhu ya san nufin Allah game da ’yan Adam?

5 Littafi Mai Tsarki ya ce abin da muka “ji” daga wasu zai iya sa mu zama masu bangaskiya. (Rom. 10:17) Wane ne ya koya wa Nuhu game da Jehobah? Babu shakka, ya koyi abubuwa da dama daga danginsa. Ɗaya daga cikinsu shi ne babansa Lamek. Lamek mutum ne mai bangaskiya sosai da aka haifa kafin Adamu ya mutu. (Ka duba hoton da ke shafi na 8.) Ya koyi hakan ma daga wurin kakansa Methuselah da baban Methuselah, wato Jared waɗanda suka mutu shekara 366 bayan an haifi Nuhu. * (Luk. 3:36, 37) Babu shakka, mutanen nan da kuma matansu ne suka koya wa Nuhu cewa Jehobah ne ya halicci mutum kuma yana so su haifi ’ya’ya su cika duniya. Ƙari ga haka, Nuhu ya koyi cewa Adamu da Hauwa’u sun yi wa Jehobah rashin biyayya kuma ya ga yadda hakan ya jawo mugun sakamako. (Far. 1:28; 3:16-19, 24) Abin da Nuhu ya koya ya motsa shi ya bauta wa Allah.—Far. 6:9.

6, 7. Ta yaya bege ya ƙarfafa bangaskiyar Nuhu?

6 Bege yana ƙarfafa bangaskiyarmu. Shi ya sa Nuhu ya kasance da bangaskiya sosai. Ya san cewa sunansa wanda yake nufin “Hutu ko Ta’aziyya” zai sa mutane su kasance da bege! (Far. 5:29) Jehobah ya hure Lamek ya yi wani annabci game da ɗansa cewa: “Wannan [Nuhu] za ya ta’azantar da mu domin . . . wahalar hannuwanmu, da ya fito daga ƙasa wadda Ubangiji ya la’anta.” Nuhu yana da bangaskiya sosai kamar Habila da Anuhu, kuma ya gaskata cewa ‘zuriya’ da aka yi annabcinsa zai murƙushe kan macijin.—Far. 3:15.

7 Ko da yake Nuhu bai fahimci abin da aka ambata a littafin Farawa 3:15 sosai ba, amma ya fahimci cewa wannan annabci zai sa mutane su sami ceto a nan gaba. Ban da haka, Anuhu ya yi wa’azi cewa Jehobah zai halaka mugaye. (Yahu. 14, 15) Abin da Anuhu ya annabta zai sake faruwa a Armageddon. Babu shakka, hakan ya ƙarfafa bangaskiyar Nuhu da kuma begensa!

8. Ta yaya sanin Allah ya kāre Nuhu?

8 Yadda sanin Allah ya taimaka wa Nuhu. Sanin Jehobah sosai ya sa Nuhu ya kasance da bangaskiya da kuma hikima. Hakan ya kāre shi, musamman daga yin abin da zai ɓata wa Jehobah rai. Alal misali, domin Nuhu ya yi “tafiya tare da Allah” bai yi tarayya da mugayen mutane ba. Abubuwan da aljanu da suka sauko duniya a lokacin suke yi suna burge mutanen, har ma suka soma bauta wa aljanun. Amma Nuhu bai yi hakan ba. (Far. 6:1-4, 9) Ƙari ga haka, Nuhu ya san cewa an gaya wa mutane ne su haifi ’ya’ya su cika duniya. (Far. 1:27, 28) Saboda haka, ya san cewa bai dace aljanu su auri mata kuma su haifi yara ba. Amma ya fi tabbata da hakan sa’ad da ya ga yadda yaran da suka haifa suka fi yaran ʼyan Adam girma da kuma ƙarfi. Da shigewar lokaci, Allah ya gaya wa Nuhu cewa zai halaka mugayen mutanen da ambaliya. Nuhu ya gina jirgin ruwa kuma shi da iyalinsa sun tsira domin yana da bangaskiya cewa Jehobah zai cika alkawarinsa.—Ibran. 11:7.

9, 10. Ta yaya za mu kasance da bangaskiya kamar Nuhu?

9 Yadda za mu kasance da bangaskiya kamar Nuhu. Yana da muhimmanci mu riƙa nazarin Kalmar Allah sosai kuma mu so abin da muka koya. Ƙari ga haka, ya kamata mu yi amfani da darasin wajen gyara rayuwarmu da kuma tsai da shawarwari masu kyau. (1 Bit. 1:13-15) Idan muka yi hakan, bangaskiya da hikima za su kāre mu daga dabarun Shaiɗan kuma su sa mu guji halayen mutanen duniya. (2 Kor. 2:11) Mutane da yawa a duniya suna son yin mugunta da lalata, kuma abin da suka fi mai da wa hankali ke nan. (1 Yoh. 2:15, 16) Idan ba mu da bangaskiya sosai, za mu ƙi gaskatawa cewa ƙarshen mugunta ya kusa. Ka tuna cewa sa’ad da Yesu yake gwada zamaninmu da na Nuhu, ya mai da hankali a kan abubuwan da za su iya raba hankalinmu daga bauta wa Allah, ba a kan mugunta da lalata ba.—Karanta Matta 24:36-39.

10 Ka tambayi kanka: ‘Yadda nake rayuwa yana nuna cewa na san Jehobah sosai? Bangaskiya tana sa in yi abin da Jehobah yake so, da kuma koya wa mutane su yi hakan?’ Amsoshinka ne za su nuna ko kana ‘tafiya da Allah.’

DANIYEL YA NUNA HIKIMA A BABILA

11. (a) Mene ne ya taimaka wa Daniyel ya riƙa ƙaunar Allah? (b) Waɗanne halayen Daniyel ne za ka so ka koya?

11 Yadda Daniel ya koya game da Jehobah. Iyayen Daniyel sun koya masa ya riƙa ƙaunar Jehobah da Kalmarsa kuma Daniyel ya yi hakan dukan rayuwarsa. Ya yi nazarin Nassosi sosai har sa’ad da ya tsufa. (Dan. 9:1, 2) Daniyel ya san Jehobah sosai, kuma ya san dukan abin da ya yi wa Isra’ilawa. Mun san hakan ta addu’ar da Daniyel ya yi da ke Daniyel 9:3-19. Zai dace ka karanta addu’ar nan kuma ka yi tunani sosai a kanta. Ƙari ga haka, ka mai da hankali ga abin da addu’ar take koya maka game da shi.

12-14. (a) Ta yaya Daniyel ya nuna hikima? (b) Ta yaya Jehobah albarkaci Daniyel don amincinsa?

12 Yadda sanin Allah ya taimaka wa Daniyel. Ba shi da sauƙi Bayahude mai aminci ya bauta wa Allah a Babila. Alal misali, Jehobah ya ce wa Yahudawa: “Ku biɗi lafiyar birni inda na sa a kai ku bauta.” (Irm. 29:7) Duk da haka, ya ce su bauta masa shi kaɗai. (Fit. 34:14) Mene ne ya taimaka wa Daniyel ya bi waɗannan umurnin? Kasancewa da hikima ya sa ya san cewa Allah ne ya kamata ya fara yi wa biyayya, ba sarakunan ’yan Adam ba. Sa’ad da Yesu ya zo duniya bayan shekaru da yawa, shi ma ya koyar da hakan.—Luk. 20:25.

13 Ka yi tunanin abin da Daniyel ya yi sa’ad da aka kafa dokar da ta hana yin addu’a na kwana 30 ga wani allah ko mutum, sai dai sarki. (Karanta Daniyel 6:7-10.) Daniyel yana iya ba da hujja cewa, ‘A’i dokar na kwana 30 ne kawai!’ Amma bai ƙyale dokar ta hana shi bauta wa Allah ba. Hakika, Daniyel yana iya yin addu’a a ɓoye, amma ya san cewa mutane sun saba ganin yana addu’a kowace rana. Saboda haka, ko da yin addu’a yana da haɗari, Daniyel ya ci gaba don kada mutane su ɗauka cewa ya daina bauta wa Jehobah.

14 Jehobah ya albarkaci Daniyel don amincinsa kuma ya yi mu’ujiza da ta hana zakuna kashe shi. A sakamako, mutane da ke Midiya da Fasiya sun ji game da Jehobah.—Dan. 6:25-27.

15. Ta yaya za mu kasance da bangaskiya kamar Daniyel?

15 Yadda za mu kasance da bangaskiya kamar Daniyel. Abin da zai taimaka mana shi ne ‘fahimtar’ Kalmar Allah ba karanta ta kawai ba. (Mat. 13:23) Muna bukatar mu san ra’ayin Jehobah a kan wasu batutuwa, kuma hakan ya ƙunshi fahimtar ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, ya kamata mu riƙa bimbini a kan abin da muka karanta. Kuma mu riƙa addu’a a kai a kai, musamman sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Ƙari ga haka, ya kamata mu yi imani cewa Jehobah zai ba mu hikima kuma ya ƙarfafa mu.—Yaƙ. 1:5.

AYUBA YA BI ƘA’IDODIN ALLAH A KOWANE LOKACI

16, 17. Ta yaya Ayuba ya koya game da Jehobah?

16 Yadda Ayuba ya koya game da Jehobah. Ayuba ba Ba’isra’ile ba ne. Amma Ibrahim da Ishaku da Yahuda danginsa ne kuma Jehobah ya bayyana musu kansa da nufinsa game da ’yan Adam. Littafi Mai Tsarki bai faɗi yadda Ayuba ya san waɗannan abubuwan ba. (Ayu. 23:12) Ayuba ya ce: “Dā na ji labarinka da kunne kawai.” (Ayu. 42:5, Juyi Mai Fitar da Ma’ana) Ban da haka ma, Jehobah da kansa ya ce Ayuba ya gaya ma wasu gaskiya game da shi.—Ayu. 42:7, 8.

Za mu kasance da bangaskiya sosai idan muka koyi halayen Jehobah daga halittunsa (Ka duba sakin layi na 17)

17 Ayuba ya koya game da Jehobah ta wurin lura da halittu. (Ayu. 12:7-9, 13) Daga baya, Elihu da Jehobah sun yi amfani da fannoni dabam-dabam na halittu don su tuna wa Ayuba cewa ’yan Adam ba kome ba ne idan aka gwada su da Allah. (Ayu. 37:14; 38:1-4) Abin da Jehobah ya ce ya ratsa zuciyar Ayuba sosai, har ya ce: “Na sani ka iya kome, ba kuwa wani nufinka da za shi hanuwa. . . . Na tuba cikin ƙura da toka.”—Ayu. 42:2, 6.

18, 19. Ta yaya Ayuba ya nuna cewa ya san Jehobah sosai?

18 Yadda sanin Allah ya taimaka wa Ayuba. Ayuba ya fahimci ƙa’idodin Allah sosai. Ya san Jehobah da kyau kuma hakan ya sa ya yi abin da ya dace. Alal misali, Ayuba ya san ba zai iya ce yana ƙaunar Allah ba idan ba ya nuna wa maƙwabcinsa alheri. (Ayu. 6:14) Ayuba bai ɗauka ya fi wasu ba. Maimakon hakan, ya kula da masu arziki da talakawa. Kuma ya ce: “Shi wanda ya sifanta ni cikin ciki, ba shi ya yi wancan” ba? (Ayu. 31:13-22) Hakan ya nuna cewa ko a lokacin da Ayuba mai arziki ne, bai ɗauki kansa ya fi wasu ba. Amma, masu arziki da iko a yau ba sa yin hakan!

19 Ayuba bai ɗau abin duniya da muhimmanci fiye da Jehobah ba. Ya san cewa idan ya yi hakan, zai musunci “Allah da ke” sama. (Karanta Ayuba 31:24-28.) Ƙari ga haka, Ayuba ya san cewa aure wa’adi ne tsakanin namiji da ta mace. Ya ma yi alkawari da idanunsa cewa ba zai yi sha’awar budurwa ba. (Ayu. 31:1) Hakan abin mamaki ne don a zamaninsa, maza suna iya auren mata da yawa. Saboda haka, zai iya ƙara aure idan ya so yin hakan. * Amma wataƙila ya san game da aure na farko da Allah ya ɗaura a Adnin, kuma ya bi wannan misalin. (Far. 2:18, 24) Bayan shekara 1,600, Yesu Kristi ya koya ma masu sauraronsa su bi wannan ƙa’ida game da aure da kuma jima’i.—Mat. 5:28; 19:4, 5.

20. Ta yaya sanin Jehobah da ƙa’idodinsa sosai za su taimaka mana mu zaɓi abokan kirki da kuma nishaɗin da ya dace?

20 Yadda za mu kasance da bangaskiya kamar Ayuba. Ya kamata mu san Jehobah sosai kuma mu bar ƙa’idodinsa su riƙa mana ja-goranci a rayuwa. Alal misali, Dauda ya ce Jehobah ya tsani “mai-mugunta da mai-son zalunci,” ya kuma ce kada mu yi tarayya da “mutanen banza.” (Karanta Zabura 11:5; 26:4.) Me ayoyin nan suka koya mana game da Allah? Ta yaya ya kamata hakan ya shafi abubuwan da suka fi muhimmanci a gare mu? Yaya hakan zai taimaka mana mu guji kallon abubuwan da ba su dace ba a intane da kuma bin abokan banza? Ta yaya zai taimaka mana mu zaɓi nishaɗin da ya dace? Amsoshinka za su taimaka maka ka san ko ka san Jehobah sosai. Don kada mugaye su rinjaye mu, wajibi ne mu horar da kanmu don mu san bambanci tsananin nagarta da mugunta da kuma abin da zai nuna cewa muna da hikima.—Ibran. 5:14; Afis. 5:15.

21. Me zai taimaka mana mu ‘fahimci’ dukan abin da zai faranta wa Jehobah rai?

21 Jehobah ya taimaka wa Nuhu da Daniyel da Ayuba su ‘fahimci’ dukan abin da zai faranta masa rai domin sun biɗe shi da zuciya ɗaya. Misalinsu ya nuna cewa yin abubuwan da Jehobah yake so zai sa mu yi nasara. (Zab. 1:1-3) Saboda haka, ka tambayi kanka, ‘Na san Jehobah sosai kamar Nuhu da Daniyel da kuma Ayuba?’ Hakika, a yau za mu iya sanin Jehobah fiye da su don mun sami ƙarin haske game da shi! (Mis. 4:18) Saboda haka, ka yi nazarin Kalmar Allah sosai, ka yi bimbini a kanta kuma ka roƙi Allah ya ba ka ruhu mai tsarki. Idan ka yi haka, mugaye a duniyar nan ba za su rinjaye ka ba. Maimakon haka, za ka riƙa aikatawa da hikima kuma za ka kusaci Jehobah sosai.—Mis. 2:4-7.

^ sakin layi na 5 Anuhu, kakan-kakan Nuhu ma ya ci gaba da “tafiya tare da Allah.” Amma, “Allah ya ɗauke shi” wajen shekara 70 kafin a haifi Nuhu.—Far. 5:23, 24.

^ sakin layi na 19 Nuhu ma ya auri mace guda, ko da yake maza sun soma auren mata da yawa bayan Adamu da Hauwa’u sun yi tawaye a Adnin.—Far. 4:19.