Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Yake Nufi a Kasance da Dangantaka Mai Kyau da Jehobah?

Me Yake Nufi a Kasance da Dangantaka Mai Kyau da Jehobah?

“Allah . . . shi yarda muku ku zama da hankali ɗaya da junanku bisa ga Kristi Yesu.”​—ROM. 15:5.

WAƘOƘI: 17, 13

1, 2. (a) Me ra’ayin mutane da yawa game da ƙulla dangantaka da Jehobah? (b) Waɗanne tambayoyi masu muhimmanci ne za mu tattauna?

WATA ’yar’uwa a Kanada ta ce: “Kasancewa da dangantakata mai kyau da Allah ya sa ni farin ciki sosai kuma ya taimaka mini in jimre da matsaloli.” Wani ɗan’uwa kuma a Brazil da ya yi shekara 23 da aure ya ce: “Muna farin ciki sosai a aurenmu don mun ƙulla dangantaka mai kyau da Allah.” Ƙari ga haka, wani ɗan’uwa da ke Filifin ya ce: “Kasancewa da dangantakata mai kyau da Jehobah ya sa ni kwanciyar hankali, kuma ya taimaka mini in riƙa abokantaka da ’yan’uwa daga ƙasashe dabam-dabam.”

2 Misalan nan sun nuna cewa za mu amfana sosai idan muka ƙulla dangantaka da Jehobah. Saboda haka, ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Me zan yi don in kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah? Kuma ta yaya hakan zai taimaka mini?’ Amma, kafin mu ba da amsar, muna bukatar mu fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da masu dangantaka mai kyau da Allah. A talifin nan, za a amsa muhimman tambayoyin nan uku. (1) Me yake nufi mutum ya kasance da dangantaka mai kyau da Allah? (2) Waɗanne misalai ne za su taimaka mana mu sami ci gaba a ibadarmu? (3) Ta yaya ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu don mu riƙa tunani kamar Kristi zai taimaka mana mu ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah?

BAMBANCIN MAI DANGANTAKA MAI KYAU DA ALLAH DA WANDA BA SHI DA SHI

3. Wane bambanci ne ke tsakanin mutum mai dangantaka mai kyau da Jehobah da wanda bai da dangantaka da shi?

3 Manzo Bulus ya taimaka mana mu san bambancin da ke tsakanin mutum da ya ƙulla dangantaka da Jehobah da wanda bai yi hakan ba. (Karanta 1 Korintiyawa 2:​14-16.) Mene ne bambancin? Mutum da ba shi da dangantaka mai kyau da Allah ba ya ‘karɓan al’amura na Ruhun Allah: gama wauta suke a gare shi; ba shi kuwa da iko shi san su.’ Amma mai dangantaka mai kyau da Jehobah yana “gwada abu duka.” Kuma yana tunani kamar Kristi. Bulus ya ƙarfafa mu mu zama masu dangantaka mai kyau da Jehobah. A waɗanne hanyoyi ne kuma mutum mai dangantaka da Allah ya bambanta da wanda ba shi da dangantaka da Jehobah?

4, 5. Ta yaya za mu san mutumin da ba shi da dangantaka mai kyau da Jehobah?

4 Wane irin hali ne mutumin da ba shi da dangantaka mai kyau da Allah yake da shi? Yana bin halin mutanen duniya da suke mai da hankali ga sha’awoyinsu kawai. Bulus ya ce hali ne “da ke aiki yanzu a cikin ’ya’yan kangara.” (Afis. 2:2) Wannan halin yana sa yawancin mutane su yi abin da wasu suke yi. Saboda haka, suna yin abin da suka ga ya dace, kuma ba sa damuwa da bin ƙa’idodin Allah. Wanda ba shi da dangantaka da Jehobah yana yawan tunani game da abin duniya. Ƙari ga haka, yakan ji cewa matsayinsa da kuɗinsa ko hakkinsa sun fi muhimmanci.

5 Ta yaya kuma ake sanin mutumin da ba shi da dangantaka mai kyau da Jehobah? Mutumin yakan yi “ayyukan jiki.” (Gal. 5:​19-21) A wasiƙa ta farko da Bulus ya rubuta wa ikilisiyar Korinti, ya ambata halayen waɗanda ba su da dangantaka mai kyau da Allah. Halayen su ne: kawo rashin jituwa da kuma jawo faɗa. Ƙari ga haka, halayen na sa mutane su yi tawaye, su kai juna kotu, su ƙi bin tsarin shugabanci kuma abu mafi muhimmanci a rayuwarsu shi ne ci da sha. Mutumin da ba shi da dangantaka da Allah ba ya guje wa abin da bai dace ba. (Mis. 7:​21, 22) Yahuda ya ce wasu za su yi sanyi a ibadarsu har ba za su kasance da ruhun Jehobah ba.​—Yahu. 18, 19.

6. Ta yaya ake sanin mutum mai ibada?

6 Mutum mai dangantaka mai kyau da Jehobah kuma fa? Yakan damu da yin abin da Allah yake so kuma yana ƙoƙari ya yi “koyi da Allah.” (Afis. 5:1) Hakan yana nufin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa ya san yadda Jehobah yake tunani da kuma ra’ayinsa a kan wasu al’amura. A gare shi, Allah ya wanzu da gaske. Ƙari ga haka, yana ƙoƙari ya bi ƙa’idodin Allah a rayuwarsa. (Zab. 119:33; 143:10) Mutumin da ke da dangantaka mai kyau da Jehobah yana ƙoƙari ya nuna “ ’ya’yan Ruhu” a rayuwarsa, maimakon ya riƙa mai da hankali ga sha’awoyinsa. (Gal. 5:​22, 23) Ga wani misalin da zai bayyana abin da yake nufi mutum ya zama mai ibada sosai. Ana kiran wanda ya iya kasuwanci, ƙwararren ɗan kasuwa. Hakazalika, ana kiran wanda yake yin abin da Allah yake so, mai ibada sosai.

7. Me Littafi Mai Tsarki ya ce game da waɗanda suka ƙulla dangantaka mai kyau da Allah?

7 Littafi Mai Tsarki ya nuna muhimmancin ƙulla dangantaka mai kyau da Allah. Littafin Matta 5:3 ya ce: “Masu farin ciki ne waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah, domin za su gāji mulkin sama.” (New World Translation) Ban da haka ma, Romawa 8:6 ya nuna amfanin yin hakan. Ya ce: “Himmantuwar jiki mutuwa ce: amma himmantuwar ruhu rai ne da lafiya.” Idan muka mai da hankali ga abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarmu da Allah, za mu sami kwanciyar hankali a yau. Kuma mu sami rai na har abada a nan gaba.

8. Me ya sa muke bukatar mu ƙoƙarta mu ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah kuma mu ci gaba da hakan?

8 Amma, muna rayuwa a muguwar duniya, kuma mutanen da ba sa bauta wa Allah ne suke ko’ina. Saboda haka, muna bukatar mu yi ƙoƙari sosai don mu kāre tunaninmu. Idan mutum ba ya tunanin abin da Jehobah yake so, zai riƙa tunanin sha’awoyinsa da kuma abin duniya kawai. Yaya za mu guji yin hakan? Ta yaya za mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah?

MISALAI MASU KYAU

9. (a) Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da zama masu ibada sosai? (b) Misalan waɗanne mutane ne za mu tattauna?

9 Yaro zai manyanta idan yana lura da abin da iyayensa suke yi kuma yana bin misalansu masu kyau. Hakazalika, za mu zama masu ibada sosai idan muna lura da abin da mutane masu dangantaka mai kyau da Jehobah suke yi, kuma muka yi koyi da su. Ban da haka, za mu san abin da bai kamata mu riƙa yi ba idan muka lura da abin da marasa ibada suke yi. (1 Kor. 3:​1-4) A Littafi Mai Tsarki, za mu ga misalan masu ibada da marasa ibada. Amma, tun da yake muna son mu zama masu ibada sosai, za mu tattauna misalai da yawa na mutane da suka ƙulla dangantaka da Allah. Za mu tattauna misalin Yakubu da Maryamu da kuma Yesu.

Mene ne muka koya daga misalin Yakubu? (Ka duba sakin layi na 10)

10. Ta yaya Yakubu ya nuna cewa yana da dangantaka mai kyau da Jehobah?

10 Bari mu soma da misalin Yakubu. Yakubu ya fuskanci matsaloli sosai a rayuwarsa kamar yawancinmu a yau. Ɗan’uwansa Isuwa ya so ya kashe shi, kuma surukinsa ya so ya cuce shi. Ko da yake Yakubu yana tare da mutane marasa ibada, ya ci gaba da ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah. Ƙari ga haka, ya yi imani da alkawarin da aka yi wa Ibrahim. Shi ya sa ya kula da iyalinsa don ya san cewa Jehobah zai yi amfani da shi wajen cika nufinsa. (Far. 28:​10-15) Furucin Yakubu da ayyukansa sun nuna cewa ya san ƙa’idodin Allah da kuma nufinsa. Alal misali, sa’ad da Yakubu ya ga cewa ɗan’uwansa Isuwa zai kawo masa hari, ya yi addu’a cewa: “Ina roƙonka, ka cece ni . . . Kai kuwa ka ce, hakika zan yi maka alheri, in mai da zuriyarka kamar yashi na teku.” (Far. 32:​6-12) Babu shakka, Yakubu yana da bangaskiya cewa Jehobah zai cika alkawuransa kuma ya bi dokokin Allah.

Mene ne muka koya daga misalin Maryamu? (Ka duba sakin layi na 10)

11. Mene ne ya nuna cewa Maryamu mai ibada ce sosai?

11 Yanzu bari mu tattauna misalin Maryamu. Me ya sa Jehobah ya zaɓi Maryamu ta zama mahaifiyar Yesu? Babu shakka, don ita mai ibada ce sosai. Ta yaya muka san hakan? Furucin da ta yi sa’ad da ta je ziyartar danginta Zakariya da Alisabatu ya nuna cewa tana da dangantaka mai kyau da Jehobah. (Karanta Luka 1:​46-55.) Abin da Maryamu ta faɗa ya nuna cewa tana son Kalmar Allah sosai kuma ta san Nassosin Ibrananci sosai. (Far. 30:13; 1 Sam. 2:​1-10; Mal. 3:12) Ban da haka ma, sa’ad da ita da Yusufu suka yi aure, ba su yi jima’i ba sai bayan da aka haifi Yesu. Mene ne hakan ya nuna? Ya nuna cewa sun fi damuwa da nufin Jehobah, maimakon sha’awoyinsu. (Mat. 1:25) Da shigewar lokaci, Maryamu ta lura da dukan abubuwan da ke faruwa yayin da Yesu yake girma da kuma furucinsa. Ƙari ga haka, “ta riƙe dukan al’amuran . . . a cikin zuciyarta.” (Luk. 2:51) Babu shakka, tana son alkawarin Allah game da Almasihu ya cika. Ya kamata misalin Maryamu ya taimaka mana mu riƙa tunanin yadda za mu saka nufin Allah a kan gaba a rayuwarmu.

12. (a) Ta yaya Yesu ya yi abubuwa kamar Jehobah? (b) Ta yaya za mu bi misalin Yesu? (Ka duba hoton da ke shafi na 18.)

12 Duk da haka, Yesu ne ya kafa misali mafi kyau na ibada. Sa’ad da yake hidima a duniya, ya nuna cewa yana son ya yi koyi da Ubansa Jehobah. Ya yi koyi da Jehobah a tunaninsa da yadda ya ji tausayin mutane kuma ya yi abubuwa kamar Ubansa. Ƙari ga haka, ya yi rayuwa da ta jitu da nufin Allah da ƙa’idodinsa. (Yoh. 8:29; 14:9; 15:10) Alal misali, ka gwada abin da Ishaya ya ce game da yadda Jehobah yake nuna tausayi da kuma abin da Markus ya ce game da yadda Yesu yake nuna juyayi. (Karanta Ishaya 63:9; Markus 6:34.) Ya kamata mu kasance a shirye mu bi misalin Yesu ta wurin jin tausayin mutanen da ke bukatar taimako. Ƙari ga haka, Yesu ya mai da hankali ga yin wa’azi sosai. (Luk. 4:43) Yin irin waɗannan abubuwa yana nuna cewa mutum yana da dangantaka mai kyau da Jehobah.

13, 14. (a) Mene ne za mu iya koya daga mutane masu ibada sosai a yau? (b) Ka ba da misali.

13 Ban da misalan da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, da akwai ’yan’uwa da yawa a yau da suke ƙoƙari su yi koyi da Kristi. Wataƙila suna wa’azi da ƙwazo kuma suna karɓan baƙi sosai. Ƙari ga haka, suna jin tausayin mutane kuma suna da wasu halaye masu kyau. Ko da yake su ajizai ne, suna ƙoƙari su kasance da waɗannan halaye masu kyau. Wata ’yar’uwa a Brazil mai suna Rachel ta ce: “Ina son bin salon rayuwa na mutanen duniya. Saboda haka, ba na saka tufafin da suka dace. Amma sa’ad da na soma bauta wa Allah, na yi ƙoƙari in zama mai ibada sosai. Yin waɗannan canje-canje ba shi da sauƙi, amma na fi farin ciki yanzu kuma na ga cewa rayuwata ta kasance da ma’ana.”

14 Wata ’yar Filifin mai suna Reylene ta fuskanci wata matsala dabam. Ta mai da hankali ga zuwa makarantar jami’a da kuma samun aiki mai kyau. Ta ce: “Da shigewar lokaci, na daina ɗaukan maƙasudai da na kafa a ibadata ga Jehobah da muhimmanci. Amma na soma lura cewa akwai abin da ba na yi a rayuwata, wato abin da ya fi aikina muhimmanci. Sai na canja ra’ayina kuma na sa hidimata ga Jehobah a kan gaba.” A yanzu, salon rayuwar Reylene ya nuna cewa ta yi imani da alkawarin da Jehobah ya yi a Matta 6:​33, 34. Kuma ta ce: “Na tabbata cewa Jehobah zai biya bukatuna!” Wataƙila da akwai ’yan’uwa a ikilisiyarku da suke yin hakan. Bari mu yi koyi da misalinsu yayin da suke bin misalin Kristi.​—1 Kor. 11:1; 2 Tas. 3:7.

KU RIƘA “TUNANI” KAMAR KRISTI

15, 16. (a) Me muke bukatar mu yi idan muna so mu zama kamar Kristi? (b) Ta yaya za mu bar tunanin Kristi ya shafi ayyukanmu?

15 Ta yaya za mu yi koyi da Kristi? Littafin 1 Korintiyawa 2:16 ya ce muna bukatar mu kasance da [‘tunanin Kristi,’ Littafi Mai Tsarki] Romawa 15:5 kuma ta ce mu “zama da hankali ɗaya . . . bisa ga Kristi Yesu.” Saboda haka, don mu zama kamar Kristi, muna bukatar mu san yadda yake tunani da kuma halinsa kuma mu yi koyi da shi. Yesu ya fi mai da hankali ga dangantakarsa da Allah. Idan muka bi misalinsa, za mu zama kamar Jehobah. Shi ya sa yake da muhimmanci sosai mu riƙa tunani kamar Yesu.

16 Ta yaya za mu iya yin hakan? Almajiran Yesu sun ga mu’ujizai da ya yi, sun ji jawabansa kuma sun ga yadda ya yi sha’ani da mutane dabam-dabam. Ƙari ga haka, sun lura da yadda ya bi ƙa’idodin Allah. Sun ce: “Mu kuwa shaidu ne ga dukan abin da ya aika.” (A. M. 10:39) Amma ba mu ga abubuwan da Yesu ya yi ba. Shi ya sa Jehobah ya yi mana tanadin Linjila don mu san Yesu sosai. Za mu koya yadda Yesu yake tunani idan mun karanta da kuma yi bimbini a kan littattafan Matta da Markus da Luka da kuma Yohanna. Yin hakan zai taimaka mana mu “bi sawun” Yesu sosai kuma mu riƙa tunani kamar sa.​—1 Bit. 2:21; 4:1.

17. Ta yaya yin tunani kamar Kristi zai taimaka mana?

17 Ta yaya yin tunani kamar Kristi zai taimaka mana? Za mu sami ƙoshin lafiya idan muna cin abinci mai kyau. Hakazalika, yin tunani kamar Kristi zai sa mu ƙarfafa dangantakarmu da Allah. A hankali, za mu san abin da Kristi zai yi a kowane yanayi. Hakan zai taimaka mana mu riƙa tsai da shawarwari da za su faranta wa Allah rai kuma zuciyarmu ba za ta riƙa damun mu ba. Hakika, waɗannan dalilai ne masu kyau da za su sa mu “ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu.”​—Rom. 13:​14, LMT.

18. Mene ne ka koya daga wannan talifin da zai taimaka maka ka zama mai ibada sosai?

18 Mun tattauna abin da yake nufi mutum ya zama mai ibada sosai. Kuma mun ga cewa za mu koyi darussa masu kyau daga mutanen da suka ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. Ban da haka ma, mun koyi yadda yin tunani kamar Kristi zai taimaka mana mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Allah. Amma, da akwai fannoni dabam-dabam na yadda za mu zama masu ibada sosai da ya kamata mu bincika. Alal misali, ta yaya za mu san ko dangantakarmu da Jehobah tana da ƙarfi sosai? Me za mu yi don mu ƙarfafa dangantakarmu da Allah? Kuma ta yaya hakan yake taimaka mana a rayuwa? Za a amsa tambayoyin nan a talifi na gaba.