Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Horo, Alama Ce Ta Kaunar Allah

Horo, Alama Ce Ta Kaunar Allah

“Wanda Ubangiji ke ƙauna shi yake horo.”​—IBRAN. 12:6.

WAƘOƘI: 123, 86

1. Ta yaya Littafi Mai Tsarki yake yawan yin amfani da kalmar nan horo?

ME KAKE tunawa sa’ad da ka ji kalmar nan “horo”? Wataƙila kana tuna da yadda ake yi ma yara dūka ko gana ma wani azaba. Amma ba shi ke nan abin da horo yake nufi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce ya dace a horar da mutum kuma a wasu lokuta ana ambata horo tare da ilimi da hikima da ƙauna da kuma rai. (Mis. 1:​2-7; 4:​11-13) Allah yana nuna cewa yana ƙaunar mu sa’ad da ya yi mana horo, don yana son mu yi rayuwa har abada. (Ibran. 12:6) Allah ba ya zalunta mu sa’ad da yake mana horo. Hakika, kalmar nan “horo” ta ƙunshi ilimantar da mutum, kamar yadda iyaye suke koyar da ɗan da suke ƙauna.

2, 3. Mene ne horo ya ƙunsa? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

2 Alal misali, akwai wani ƙaramin yaro mai suna Jamilu da ke buga ƙwallo a cikin ɗaki. Sai mahaifiyarsa ta ce: “Jamilu, ka san bai kamata ka buga ƙwallo a cikin ɗaki ba domin kana iya fasa wani abu!” Amma ya ƙi dainawa, har ya fasa tukunyar fure. Mene ne mahaifiyarsa za ta yi masa? Za ta koyar da shi ta wajen bayyana masa cewa abin da ya yi bai dace ba. Tana son ya san cewa ya dace ya riƙa yi wa iyayensa biyayya. Kuma ta bayyana masa cewa dokokinsu za su amfane shi. Ƙari ga haka, don ta taimaka wa Jamilu ya koyi darasi, tana iya horar da shi yadda ya dace. Alal misali, tana iya ƙwace ƙwallon daga hannunsa, kuma ta ƙi ba shi har sai bayan wani lokaci. Ta hakan zai koyi cewa rashin biyayya na jawo mugun sakamako.

3 Da yake mu Kiristoci ne, mun zama iyalin Allah. (1 Tim. 3:15) Shi ya sa Jehobah yake da ikon kafa dokokin da za mu bi kuma yana mana horon da ya dace sa’ad da muka yi masa rashin biyayya. Ƙari ga haka, idan ayyukanmu sun jawo mana mugun sakamako, horo zai tuna mana cewa yana da muhimmanci mu saurari Ubanmu na sama. (Gal. 6:7) Allah yana ƙaunar mu sosai kuma ba ya son mu sha wahala.​—1 Bit. 5:​6, 7.

4. (a) Me ya kamata mu yi amfani da shi wajen koyarwa? Ka bayyana. (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Yin amfani da Littafi Mai Tsarki wajen koyar da yaronmu ko ɗalibinmu zai taimaka musu su zama mabiyan Kristi. Irin wannan horon zai. Yin amfani da Kalmar Allah sa’ad da muke koyarwa zai taimaka mana mu yi ‘horo da ke cikin adalci.’ Ta yin hakan, za mu taimaka ma yaronmu ko ɗalibinmu ya fahimci ‘dukan iyakar abin da Yesu ya umurce mu’ kuma ya yi su. (2 Tim. 3:16; Mat. 28:​19, 20) Haka ne Jehobah yake son mu riƙa koyarwa, kuma hakan zai taimaka ma wasu su zama almajiran Kristi. (Karanta Titus 2:​11-14.) Bari mu tattauna amsoshin tambayoyi uku masu muhimmanci: (1) Ta yaya horon da Allah yake mana ya nuna cewa yana ƙaunar mu? (2) Mene ne za mu koya daga mutanen da Allah ya horar da su a dā? (3) Ta yaya za mu yi koyi da Jehobah da Yesu sa’ad da muke horar da mutane?

ALLAH YANA HORAR DA MU CIKIN ƘAUNA

5. A waɗanne hanyoyi ne yadda Jehobah yake horar da mu ya nuna cewa yana ƙaunar mu?

5 Jehobah yana yi mana gyara, yana koyar da mu kuma yana mana horo don yana ƙaunar mu. Ƙari ga haka, yana son mu riƙa bauta masa kuma mu sami rai na har abada. (1 Yoh. 4:16) Ba ya kunyatar da mu don mu riƙa ganin ba mu da amfani. (Mis. 12:18) Maimakon haka, Jehobah yana daraja mu kuma yana mai da hankali ga halayenmu masu kyau. Yana kuma ƙyale mu mu yi zaɓin da muke so. Idan Allah ya yi amfani da Kalmarsa ko littattafanmu ko iyayenmu ko kuma dattawa don ya yi mana horo, za mu amince da horon kuwa? Hakika, idan dattawa sun horar da mu yadda ya dace kafin ma mu san cewa mun yi wani laifi, suna yin koyi da yadda Jehobah yake ƙaunar mu.​—Gal. 6:1.

6. Idan wani ya rasa gatarsa, ta yaya hakan ya nuna cewa Allah yana ƙaunar sa?

6 A wasu lokuta, horar da mutum ya ƙunshi wasu abubuwa ban da yi masa gargaɗi kawai. Mutumin yana iya rasa gatarsa a ikilisiya idan ya yi zunubi mai tsanani. Ko a wannan yanayin, irin wannan horon na nuna cewa Allah yana ƙaunar sa. Alal misali, rasa gata zai taimaka wa mutum ya fahimci cewa yana bukatar ya fi mai da hankali a kan nazarin Littafi Mai Tsarki da bimbini da kuma yin addu’a. Yin abubuwan nan zai taimaka masa ya ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah. (Zab. 19:7) Da shigewar lokaci, za a mayar masa da gatarsa. Ko da an yi wa mutum yankan zumunci, Jehobah yana ƙaunar sa domin horon yana kāre ikilisiya daga mugun tasiri. (1 Kor. 5:​6, 7, 11) Ƙari ga haka, don Allah yana horar da mu yadda ya dace, yankan zumunci zai sa mutum ya fahimci cewa ya yi zunubi mai tsanani kuma yana bukatar ya tuba.​—A. M. 3:19.

YA AMFANA DAGA HORON JEHOBAH

7. Wane ne Shebna, kuma wane halin banza ne yake da shi?

7 Don mu fahimci yadda horo yake da muhimmanci, za mu tattauna labarin mutane biyu da Jehobah ya yi musu horo. Ɗaya daga cikinsu Shebna ne, wanda ya yi rayuwa a zamanin Sarki Hezekiya. Ɗayan kuma wani ɗan’uwa a zamaninmu ne mai suna Graham. Shebna “shugaban gidan sarki” ne, wataƙila gidan Hezekiya. Hakan ya nuna cewa yana da iko sosai. (Isha. 22:​15, Juyi Mai Fitar da Ma’ana) Amma Shebna ya zama mai fahariya da kuma mai neman girma. Ƙari ga haka, ya haƙa wa kansa kabari mai tsada, kuma yana hawan ‘karusa mai alfarma’!​—Isha. 22:​16-18.

Allah zai albarkace mu idan mu masu tawali’u ne kuma mun canja halinmu (Ka duka sakin layi na 8-10)

8. Ta yaya Jehobah ya horar da Shebna, kuma yaya ya ji?

8 Don Shebna yana neman girma, sai Allah ya ba Eliakim matsayinsa. (Isha. 22:​19-21) Jehobah ya yi hakan sa’ad da Sarki Sennakerib na Assuriya yake so ya kai wa Urushalima hari. Akwai lokacin da Sennakerib ya tura ma’aikatansa tare da sojoji zuwa Urushalima. Ya yi hakan ne don ya tsoratar da Yahudawa kuma ya sa Hezekiya ya miƙa wuya. (2 Sar. 18:​17-25) Sarki Hezekiya ya tura Eliakim tare da wasu don su yi magana da sojojin Sennakerib. Wani da kuma Shebna wanda a lokacin sakatare ne suka bi Eliakim. Hakan ya nuna cewa Shebna bai yi fushi ba amma ya koyi hankali kuma ya karɓi matsayin da aka ba shi. Waɗanne darussa ne muka koya daga wannan labarin? Za mu tattauna guda uku daga cikinsu.

9-11. (a) Waɗanne darussa masu muhimmanci ne muka koya daga labarin Shebna? (b) Ta yaya yadda Jehobah ya horar da Shebna ya ƙarfafa ka?

9 Na ɗaya, Shebna ya rasa matsayinsa. Hakan ya nuna mana cewa “girman kai ja-gora ne zuwa ga halaka, fariya kuwa zuwa ga faɗuwa.” (Mis. 16:​18, Littafi Mai Tsarki) Wataƙila kana da gata a cikin ikilisiya, kuma wasu suna ganin kana da girma sosai. Shin hakan zai sa ka zama mai tawali’u? Za ka riƙa yaba wa Jehobah don iyawarka ko kuma abubuwan da ka cim ma a hidimarsa? (1 Kor. 4:7) Manzo Bulus ya ce: Na “faɗa wa kowane mutum wanda ke cikinku, kada shi aza kansa gaba da inda ya kamata; amma ya tuna yadda za shi aza da hankali.”​—Rom. 12:3.

10 Na biyu, yadda Jehobah ya horar da Shebna ya nuna cewa Jehobah ya gaskata cewa zai canja halinsa. (Mis. 3:​11, 12) Wannan darasi ne mai kyau ga duk waɗanda suka rasa gatansu! Maimakon su riƙa fushi ko baƙin ciki, ya kamata su ci gaba da bauta wa Allah da zuciya ɗaya. Ƙari ga haka, su san cewa Jehobah ya yi musu horo don yana ƙaunar su. Ku tuna cewa Ubanmu zai albarkaci dukan masu tawali’u. (Karanta 1 Bitrus 5:​6, 7.) Horon Jehobah zai amfane mu idan muka zama masu tawali’u, kuma muka yi taushi kamar laka a hannunsa.

11 Na uku, waɗanda suke da ikon horar da mutane, kamar dattawa da iyaye za su iya koyan darasi sosai daga yadda Jehobah ya horar da Shebna. Wane darasi ke nan? Jehobah yana ƙaunar wanda ya yi zunubi duk da cewa ba ya son zunubi. Idan iyaye da dattawa suna son su yi wa yaronsu ko ’yan’uwa a ikilisiya horo, zai dace su yi koyi da Jehobah.​—Yahu. 22, 23.

12-14. (a) Yaya wasu suke ji idan an yi musu horo? (b) Ta yaya Kalmar Allah ta taimaka ma wani ɗan’uwa ya canja ra’ayinsa, kuma yaya hakan ya amfane shi?

12 Amma wasu suna baƙin ciki sa’ad da aka yi musu horo. A sakamako, sai su daina bauta wa Allah da yin cuɗanya da mutanensa. (Ibran. 3:​12, 13) Hakan yana nufin cewa ba za a iya taimaka musu ba? A’a. Alal misali, an yi wa Graham yankan zumunci kuma daga baya aka dawo da shi. Bayan hakan, sai ya daina wa’azi da halartan taro. Bayan wasu shekaru, sai ya gaya wa wani dattijo da ya zama abokinsa cewa ya yi nazari da shi.

13 Dattijon ya ce: “Graham mai fahariya ne sosai. Yana ganin cewa dattawan da suka yi masa yankan zumunci suna da laifi. Saboda haka, mun yi nazari a kan ayoyin da suka yi magana game da fahariya da yadda take shafan mutane. Da taimakon Kalmar Allah, Graham ya ga cewa yana da matsala sosai, kuma hakan ya sa shi baƙin ciki! Ƙari ga haka, ya amince cewa ‘gungume,’ wato fahariya da kuma kushe mutane da yake yi sun sa bai ga cewa yana da laifi ba. Sai ya ɗauki mataki nan da nan don ya canja halinsa. Ban da haka, ya soma halartan taro a kai a kai da kuma yin nazarin Kalmar Allah sosai. Kuma yana addu’a kullum ga Jehobah. Ya kuma soma kula da iyalinsa sosai. Hakan ya sa matarsa da yaransa farin ciki.”​—Luk. 6:​41, 42; Yaƙ. 1:​23-25.

14 Dattijon ya ci gaba da cewa: “Wata rana, Graham ya gaya mini abin da ya sosa zuciyata. Ya ce, ‘Na yi shekaru ina bauta wa Jehobah, har na yi hidimar majagaba. Amma, yanzu ne zan ce da dukan zuciyata cewa ina ƙaunar Jehobah sosai.’ Ba da daɗewa ba, aka gaya wa Graham ya riƙa kula da makarufo a taro, kuma yana farin cikin yin wannan hidimar. Labarinsa ya koya min cewa idan mutum mai tawali’u ne kuma ya amince da horon da aka yi masa, Jehobah zai albarkace shi!”

KU YI KOYI DA ALLAH DA KRISTI SA’AD DA KUKE HORAR DA WASU

15. Me za mu yi idan muna son mutane su amince da horon da muka yi musu?

15 Wajibi ne mu riƙa nazari sosai idan muna son mu zama ƙwararrun malamai. (1 Tim. 4:​15, 16) Hakazalika, idan kana horar da mutane, wajibi ne ka zama mai tawali’u kuma ka riƙa bin ja-gorancin Jehobah. Yin hakan zai sa mutane su riƙa daraja ka kuma su bi shawarar da ka ba su. Za mu iya koyan darasi daga misalin Yesu.

16. Mene ne za mu iya koya daga Yesu game da horo da kuma koyarwa?

16 Yesu yana yi wa Ubansa biyayya har a lokacin da yin hakan ya yi masa wuya sosai. (Mat. 26:39) Kuma ya ce Ubansa ne ya sa ya iya koyarwa, shi ne kuma ya sa ya zama mai hikima. (Yoh. 5:​19, 30) Mutane sun kusaci Yesu domin shi mai tawali’u ne kuma yana wa Ubansa biyayya. Ƙari ga haka, shi mai juyayi ne kuma yana nuna wa mutane alheri. (Karanta Luka 4:22.) Furucinsa ya ƙarfafa masu sanyin gwiwa da waɗanda suka karaya. (Mat. 12:20) Yesu ya bi da manzanninsa cikin ƙauna har a lokacin da suka sa shi fushi domin suna gardama a kan wanda ya fi girma. Yesu ya yi musu gyara cikin ƙauna.​—Mar. 9:​33-37; Luk. 22:​24-27.

17. Waɗanne halaye ne za su taimaka wa dattawa su riƙa kula da garken Allah?

17 Dattawa suna bukatar su yi koyi da Kristi a duk lokacin da suke horar da mutane. Yin hakan na nuna cewa suna son ja-gorancin Allah da kuma Yesu. Manzo Bitrus ya ce: “Ku yi kiwon garken Allah wanda ke wurinku, kuna yin shugabanci, ba kamar na tilas ba, amma da yardan rai, bisa ga nufin Allah; ba kuwa domin riba mai-ƙazanta ba, amma da karsashin zuciya; ba kuwa kamar masu-nuna sarauta bisa abin kiwo da aka sanya a hannunku ba, amma kuna nuna kanku gurbi ne ga garken.” (1 Bit. 5:​2-4) Hakika, dattawan da ke bin dukan umurnin Allah da Kristi, wanda shi ne shugaban ikilisiya, za su amfana sosai. Kuma waɗanda suke ƙarƙashinsu ma za su amfana.​—Isha. 32:​1, 2, 17, 18.

18. (a) Mene ne Jehobah yake son iyaye su yi? (b) Ta yaya Allah yake taimaka wa iyaye?

18 Wannan ƙa’idar ta shafi horarwa da kuma koyarwa a cikin iyali. Jehobah ya ce wa magidanta: “Kada ku yi wa ’ya’yanku cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:4) Hakan yana da muhimmanci kuwa? Misalai 19:18 ta ce: “Ka yi ma ɗanka horo, da shi ke ana kafa zuciya gare shi: kada ka ƙalafa ranka kuma ga hallakarsa.” Hakika, Allah ya ba iyaye aikin horar da yaransu. Idan ba su yi hakan ba, za su ba da lissafi ga Allah! (1 Sam. 3:​12-14) Amma Jehobah yana ba iyaye hikima da ƙarfin da suke bukata idan suka nemi taimakonsa. Ƙari ga haka, ya kamata su dogara ga ja-gorancin da yake mana ta Kalmarsa da ruhu mai tsarki.​—Karanta Yaƙub 1:5.

KOYAN YADDA ZA MU YI ZAMAN LAFIYA DA MUTANE HAR ABADA

19, 20. (a) Wace albarka ce za mu samu idan muka amince da horon Allah? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

19 Za mu sami albarka sosai idan muka amince da horon Allah kuma muka yi koyi da yadda Jehobah da Yesu suke horar da mutane. Hakan zai sa iyalinmu da ikilisiyoyi su zauna lafiya. Kowa zai ji cewa ana ƙaunarsa, ana daraja shi kuma zai kasance da kwanciyar hankali. Ƙari ga haka, abubuwan nan soma taɓi ne na salama da farin cikin da za mu more a nan gaba. (Zab. 72:7) Horarwar da Jehobah yake mana tana koya mana yadda za mu zauna da juna har abada cikin kwanciyar hankali a aljanna. (Karanta Ishaya 11:9.) Idan muka kasance da ra’ayin da ya dace game da horon da Jehobah yake mana, za mu riƙa ganin cewa yana ƙaunar mu sa’ad da ya horar da mu.

20 A talifi na gaba, za mu ƙara koya game da horo a cikin iyali da kuma ikilisiya. Za mu tattauna yadda za mu horar da kanmu da kuma mummunan sakamakon ƙin amincewa da horon da aka mana.