Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Me ya sa bai dace mu saka littattafan da Shaidun Jehobah suka wallafa a dandalin sada zumunta da dai sauransu ba?

Domin ba ma sayar da littattafanmu, wasu suna ganin ba laifi ba ne a kofa ko kuma a saka su a wasu dandalin yanar gizo ko kuma dandalin sada zumunta. Amma yin hakan ya taka Sharuɗɗan Amfani * na dandalinmu kuma ya jawo matsaloli sosai. Ban da haka, kamar yadda aka ambata a Sharuɗɗan, bai dace ba mutum ya “saka zane-zane ko littattafai ko tambari ko waƙoƙi ko hotuna ko bidiyoyi ko kuma talifofi da aka kofa daga dandalinmu zuwa wani dandalin Intane ba (wato dandalin tura littattafai, ko bidiyo ko kuma na sada zumunta).” Me ya sa aka hana yin waɗannan abubuwan?

Ba a yarda ba wani ya saka littattafanmu da aka kāre da hakkin mallaka a wani dandali ba

An kāre dukan abubuwan da ke dandalinmu da hakkin mallaka. ’Yan ridda da wasu masu adawa da mu suna amfani da littattafanmu a dandalinsu don su rinjayi Shaidun Jehobah da kuma wasu. Sun shirya wannan dandalin don su sa masu karantawa su soma shakkar abin da suka yi imani da shi. (Zab. 26:4; K. Mag. 22:5) Wasu kuma sun yi amfani da abin da ke littattafanmu ko kuma alamar jw.org don su yi tallar abubuwan da suke sayarwa da kuma manhajar wayoyi. Da yake mun yi rajistar hakkinmu, muna da ikon kai ƙara a kotu don mu hana mutane yin waɗannan abubuwan a dandalinmu. (K. Mag. 27:12) Amma idan muna barin mutane har ’yan’uwa su saka abin da ke dandalinmu a cikin wasu dandali ko kuma su yi amfani da tambarin jw.org don kasuwancinsu, kotu ba za ta saurari ƙarar da muka kai na hana masu adawa da mu da kuma masu kasuwanci ba.

Saukar da littattafanmu daga wani wurin da ba jw.org ba yana da haɗari sosai. Jehobah ya ba “bawan nan mai aminci, mai hikima” kaɗai hakkin yi mana tanadin littattafan da za su sa mu ƙarfafa dangantakarmu da shi. (Mat. 24:45) Wannan “bawan” yana amfani da dandalin www.pr418.com, da tashar tv.pr418.com da kuma wol.pr418.com don wallafa abubuwan da suke taimaka mana a bautarmu ga Jehobah. Ƙari ga haka muna da manhaja guda uku kawai da za mu iya amfani da su a na’urorinmu. Kuma su ne JW Language® da JW Library® da kuma JW Library Sign Language®. Ba a yin talla a waɗannan manhajar kuma mugayen mutane ba su ɓata manhajar ba. Saboda haka, idan muka saukar da littattafai daga wani dandali, wataƙila an riga an canja su ko kuma an ɓata abin da ke cikinsu.​—Zab. 18:26; 19:8.

Ban da haka, saka littattafanmu a wani dandalin da wasu za su iya yin kalami zai sa ’yan ridda da wasu masu sūkar mu su faɗi abubuwan da ba daidai ba game da ƙungiyar Jehobah. Hakan ya sa wasu ’yan’uwa yin mahawwara a dandalin sada zumunta, kuma hakan yana ƙara ɓata sunan Jehobah. Dandalin sada zumunta ba wuri ba ne da ya dace a riƙa koyar da waɗanda suke gāba da koyarwarmu “a cikin sauƙin kai.” (2 Tim. 2:​23-25; 1 Tim. 6:​3-5) Ƙari ga haka, mun lura cewa wasu sun buɗe dandalin sada zumunta da wasu shafuffuka a Intane da sunan ƙungiyar Jehobah da kuma Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu da membobinta. Amma, babu wani memban Hukumar da Ke kula da Ayyukanmu da yake da asusu a dandalin sada zumunta ko kuma nasa shafin Intane.

Gaya wa mutane game da jw.org yana taimaka mana mu yaɗa “labari mai daɗi.” (Mat. 24:14) A kai a kai, ana kyautata littattafan da ke cikin dandalinmu da muke amfani da su a yin wa’azi. Za mu so dukan mutane su amfana ta yin amfani da waɗannan littattafan. Saboda haka, kamar yadda aka ambata a Sharuɗɗan Amfani, kana iya tura wani littafinmu ta imel ko kuma nuna ma mutum wani shafi da ke dandalin jw.org. Ta wurin gaya wa mutane da masu son saƙonmu game da dandalinmu, muna nuna musu cewa “bawan nan mai aminci, mai hikima” ne kaɗai suke koyar da mu gaskiya game da Jehobah.

^ sakin layi na 1 Za a iya ganin waɗannan Sharuɗɗan Amfani a ƙasan shafin farko a dandalin jw.org/ha, kuma abin da ambata a waɗannan sharuɗɗan ya shafi kome a dandalinmu.