Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Na Tashi Cikin Talauci, Amma Yanzu Ni Mai Arziki Ne

Na Tashi Cikin Talauci, Amma Yanzu Ni Mai Arziki Ne

An haife ni a wani gidan katako mai ɗaki ɗaya a garin Liberty da ke jihar Indiana a Amirka. Iyayena suna da yara uku kafin su haife ni. Daga baya, suka haifi ƙannena maza biyu da kuma ƙanwata.

Gidan katakon da aka haife ni

A LOKACIN da nake makaranta, abubuwa ba su canja sosai a makarantarmu da kuma garinmu ba. Mun kammala makaranta tare da yaran da muka soma makaranta da su. Kuma hakan ya sa yawancin mutane a garin sun san juna.

Iyayena sun haifi yara bakwai kuma a lokacin da nake ƙarami na koyi aikin gona

Ainihin aikin da mutanen garin Liberty suke yi shi ne noma kuma masara ne aka fi nomewa. A lokacin da aka haife ni, mahaifina yana yi ma wani manomi aiki. Sa’ad da na zama matashi, sai na koyi tuƙa motar noma da kuma aikin gona.

A lokacin da aka haife ni, shekarun mahaifina 56 ne, mahaifiyata kuma shekarunta 35. Mahaifina mutum ne mai kuzari da kuma ƙoshin lafiya sosai, yana son yin aiki kuma ya koya wa yaransa yin aiki tuƙuru. Duk da cewa ba ya samun kuɗi sosai, muna da wurin kwana da abinci da kuma sutura. Ban da haka ma, yana kasancewa tare da mu. Shekarun mahaifina 93 ne sa’ad da ya rasu, mahaifiyata kuma shekarunta 86. Babu wani a cikinsu da ya bauta wa Jehobah, amma ƙanena dattijo ne tun daga shekara ta 1972, kuma yana bauta wa Jehobah da aminci.

LOKACIN DA NAKE ƘARAMI

Mahaifiyata mai ibada ce sosai. Mukan je cocin Baptist kowace ranar Lahadi da ita. Na fara ji game da koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya a lokacin da nake ɗan shekara 12. Amma da yake ina son in san abin da hakan yake nufi, sai na tambayi mahaifiyata: “Yaya za a ce Yesu shi ne Ɗa da kuma Uba?” Ta ba ni amsa cewa: “Ɗana, wannan sirri ne da ba za mu iya fahimta ba.” Hakika a gare ni, abu ne da ba za a iya ganewa ba. Duk da haka, a lokacin da na kusan shekara 14, an yi mini baftisma a rafi ta wajen nitsar da ni a ruwa sau uku, cikin jituwa da koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya!

Lokacin da nake ɗan shekara 17 a shekara ta 1952 kafin in shiga soja

A lokacin da nake makarantar sakandare, ina da wani aboki ɗan dambe, kuma ya ƙarfafa ni in soma dambe. Sai na shiga yin dambe, kuma na zama memban ƙungiyar ’yan dambe da ake kira Golden Gloves. Amma bai daɗe ba, sai na daina don ban iya dambe sosai ba. Bayan haka, aka tilasta mini in shiga soja a Amirka kuma aka tura ni ƙasar Jamus. A wurin, shugabanninmu suka tura ni makarantar soja don suna gani zan iya shugabanci sosai. Suna son wannan aikin ya zama sana’ata, amma ba na son in yi aikin soja. Saboda haka, bayan na yi aiki shekara biyu, sai na bar soja a shekara ta 1956. Amma ba da daɗewa ba, sai na soma wani aiki dabam.

Na yi shekara biyu a soja a Amirka daga 1954-1956

NA SOMA BAUTA WA JEHOBAH

Kafin in soma bauta wa Jehobah, ina da ra’ayin da bai dace ba game da yadda mutum zai zama namijin ƙwarai. Fina-finai da kuma mutanen da nake cuɗanya da su ne suka cusa mini wannan ra’ayin. A dā, ina ganin cewa maza da ke koyar da Littafi Mai Tsarki ragwaye ne. Amma sai na soma koyan wasu abubuwan da suka canja ra’ayina. Wata rana na shiga cikin gari da motata mai jar kala, sai wasu ’yammata biyu suka kira ni. Na san su, don su ’yan’uwan mijin ’ya’yata ne kuma sun taɓa ba ni mujallun Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! Amma na ji kamar Hasumiyar Tsaro tana da wuyan fahimta. Ban da haka, sai suka gayyace ni taron Rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya kuma a gidansu ake taron. Na gaya musu cewa zan zo kuma suka ce: “Ka yi alkawari?” Na ce musu: “E, na yi alkawari!”

Na yi da-na-sanin yin wannan alkawarin, amma dole ne in cika shi. Don haka a daren, na halarci taron kuma yadda yara a taron suka san Littafi Mai Tsarki ya burge ni sosai! Duk da cewa ina zuwa coci da mahaifiyata kowace ranar Lahadi, ban san Littafi Mai Tsarki sosai ba. Hakan ya sa na yarda a yi nazari da ni. Na koya cewa Jehobah ne sunan Allah Maɗaukaki. Shekaru da yawa kafin wannan lokacin, na taɓa tambayar mahaifiyata game da Shaidun Jehobah, kuma ta ce: “Suna bauta ma wani tsohon mutum mai suna Jehobah.” Amma yanzu na san su sosai!

Na sami ci gaba sosai, don na san abin da nake koya gaskiya ne. Bayan watanni tara da na halarci wannan taron, sai na yi baftisma a watan Maris na 1957. Na canja halina kuma ina farin ciki sosai cewa na koyi abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da zama namijin ƙwarai. Yesu kamili ne kuma yana da kuzari da ƙarfi fiye da kowane mutum a duniya, amma bai yi faɗā da mutane ba. A maimakon haka, ya amince ya sha “wahala.” (Isha. 53:​2, 7) Hakan ya sa na koyi cewa mabiyin Yesu yana bukatar ya “zama mai kirki ga kowa.”​—⁠2 Tim. 2:⁠24.

Na soma hidimar majagaba a 1958. Amma sai na daina hidimar na ɗan lokaci. Me ya sa? Domin na yanke shawara cewa zan auri Gloria, ɗaya daga cikin ’yammatan da suka gayyace ni taro! Ban taɓa yin da-na-sanin auren Gloria ba, domin a gare ni tana da tamani sosai fiye da lu’u’lu’u mafi tsada. Ina farin ciki cewa na aure ta. Bari Gloria ta ɗan ba ku labarinta:

“Iyayena sun haifi yara 17, kuma mahaifiyata ta bauta wa Jehobah da aminci. A lokacin da nake ’yar shekara 14 ne ta rasu, sai mahaifina ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Da yake mahaifiyarmu ta rasu, mahaifinmu ya nemi izini daga shugaban makarantarmu don ni da yayata da ta kusan kammala makarantar sakandare a lokacin mu riƙa yin musanyar zuwa makaranta. Ya yi hakan ne don ɗaya daga cikinmu ya zauna a gida ya riƙa kula da ƙannenmu. Ban da haka, za ta dafa abincin yamma da za mu ci bayan babanmu ya dawo daga aiki. Shugaban makarantar ya amince da wannan shirin, kuma muka yi hakan har lokacin da yayata ta kammala makaranta. Wasu iyalai biyu ne suka yi nazari da mu kuma 11 daga cikin ’yan’uwana suna bauta wa Jehobah. Ina jin daɗin yin wa’azi duk da cewa ni mai jin kunya ce sosai, amma mijina ya taimaka mini.”

Ni da Gloria mun yi aure a watan Fabrairu na 1959, kuma mun ji daɗin yin hidimar majagaba tare. A watan Yuli na shekarar, mun cika fom na yin hidima a Bethel, don burinmu shi ne mu yi hidima a hedkwatarmu. Ɗan’uwa Simon Kraker ne ya yi mana intabiyu, kuma ya gaya mana cewa ba a gayyatar ma’aurata a Bethel a lokacin. Duk da haka, ba mu manta da burin yin hidima a Bethel ba, amma sai bayan shekaru da yawa ne muka cim ma hakan.

Mun tura wasiƙa zuwa hedkwatarmu cewa muna so a tura mu yin hidima a inda ake bukatar masu shela sosai. Sai aka tura mu birnin Pine Bluff a jihar Arkansas. A lokacin, ikilisiyoyi biyu ne kaɗai a birnin, ɗaya na fararen fata ne ɗayan kuma na baƙaƙe. An tura mu zuwa ikilisiyar baƙaƙen fata kuma masu shela wajen 14 ne kaɗai a ikilisiyar.

MUN FUSKANCI WARIYAR LAUNIN FATA

Kana iya yin mamaki cewa Shaidun Jehobah suna nuna wariya. Amma ba su da zaɓi a wannan lokacin domin gwamnati ta kafa doka cewa ba a son fararen fata su yi cuɗanya da baƙaƙe. Ban da haka, yin cuɗanya yana iya jawo cin zarafin mutum. A wurare da yawa, ’yan’uwa suna jin tsoro cewa za a halaka Majami’arsu idan farare da baƙaƙe suka yi taro kuma irin waɗannan abubuwa sun faru. Ƙari ga haka, ana iya kama baƙaƙe kuma wataƙila a yi musu dūka idan suka yi wa’azi a yankin da turawa suke. Saboda haka, da yake muna son mu yi wa’azi, mun bi dokokin da fatan cewa abubuwa za su gyaru a nan gaba.

Mun fuskanci ƙalubale sosai a hidimarmu. Idan muna wa’azi a yankin baƙaƙe, wani lokaci mukan yi kuskure mu ƙwanƙwasa ƙofar turawa. Idan hakan ya faru, mukan tsai da shawara nan da nan ko za mu ɗan yi musu wa’azi ko mu ba su haƙuri mu yi gaba. Haka ne muke wa’azi a wasu wurare a lokacin.

Ƙari ga haka, da yake mu majagaba ne, mun yi aiki don mu biya bukatunmu. Ana biyanmu dala uku a yawancin aikin da muka yi. Matata ta yi aikin sharan ɗaki, kuma akwai lokacin da na taimaka mata don ta gama aikin da wuri. Sai mutanen gidan suka ba mu abincin rana kuma muka ci kafin mu tafi. A kowane mako, matata takan yi ma wata iyali aikin guga, ni kuma in yi aikin lambu da wanke tagogi da kuma wasu ayyuka a gidan. A gidan wasu fararen fata, ni da matata mun wanke tagogi, ita tana wankewa daga ciki, ni kuma ina wankewa daga waje. Mun yi wannan aikin daga safe har yamma. Saboda haka, sun ba mu abincin rana. Matata ta ci nata a cikin gida, ni kuma na ci nawa a gareji. Hakan bai dame ni ba don na ji daɗin abincin. Masu gidan mutanen kirki ne, amma abin da mutane suke yi ne ya shafe su. Na tuna wata rana da muka tsaya shan māi, da muka gama, na tambayi baturen da ke sayar da mān ko matata za ta iya yin amfani da bayan gidansu. Sai ya harare ni, ya ce, “A rufe yake.”

ALHERIN DA BA ZA MU TAƁA MANTAWA BA

Duk da dukan matsalolin nan, mun ji daɗin yin tarayya da ’yan’uwa kuma mun ji daɗin hidimarmu! Sa’ad da muka isa birnin Pine Bluff, da farko mun zauna a gidan wani ɗan’uwa wanda shi ne bawan ikilisiya. A lokacin, matarsa ba Mashaidiya ba ce kuma matata ta soma nazari da ita. Ni kuma na soma nazari da ’yarsu da mijinta. Mahaifiyar da kuma ’yarta suka soma bauta wa Jehobah kuma suka yi baftisma.

Muna da abokai sosai a ikilisiyar turawa. Sukan gayyace mu cin abincin dare a gidansu, amma muna yin hakan a ɓoye. Don a lokacin, akwai wata ƙungiya da ke ƙarfafa wariya sosai da kuma yin mugunta. Ana kiran su Ku Klux Klan. Akwai wata rana daddare da ake bikin Halloween, sai na ga wani mutum zaune a gaban gidansa yana sanye da kayan ’yan ƙungiyar Ku Klux Klan. Irin wannan yanayin bai hana ’yan’uwa nuna karimci ba. Ban da haka, akwai lokacin rani da ba mu da kuɗin halartan taron yanki, sai muka sayar ma wani ɗan’uwa motarmu ƙirar Ford na shekara ta 1950. Amma bayan wata guda, sai muka dawo gida daga wa’azi wata rana a gajiye don mun yi wa’azi gida-gida da kuma nazari da mutane. Sai muka yi mamaki sosai da muka ga motar da muka sayar a fake a gidanmu! An rubuta wasiƙa kuma aka saka a madubin motar cewa: “Ga motarku na ba ku kyauta. Ni ne ɗan’uwanku.”

Akwai wani alherin da aka mana da ba za mu taɓa mantawa ba. An gayyace ni halartan Makarantar Hidima ta Mulki a birnin South Lansing da ke jihar New York. A makarantar, za a horar da masu kula da ikilisiyoyi da da’irori da kuma gunduma. Amma ba ni da kuɗi da yake ba na aiki a lokacin da aka gayyace ni zuwa makarantar. Kafin wannan lokacin, wani kamfanin tarho da ke Pine Bluff sun yi mini intabiyu. Idan suka ɗauke ni aiki, zan zama baƙin fata na farko da zai yi aiki a wannan kamfanin. Daga baya, suka gaya mini sun ɗauke ni aiki. To me zan yi don ba ni da kuɗin zuwa New York? Na tsai da shawarar soma aikin amma ba zan je makarantar ba. Har na soma shirin rubuta wasiƙa cewa ba zan samu damar zuwa makarantar ba. Sai wani abin da ba zan taɓa mantawa ya faru.

Wata ’yar’uwa a ikilisiyarmu da mijinta ba Mashaidi ba ne ta zo gidanmu wata rana da sassafe, kuma ta ba ni wani ambulan cike da kuɗi. Ita da yaranta sukan tashi da sassafe su je yankan ciyawa a gonar auduga don su sami kuɗin da zan je New York da shi. Sai ta ce, “Ka tafi makaranta ka koyi abubuwa da yawa don ka dawo ka koyar da mu!” Saboda haka, na tambayi kamfanin ko zan iya soma aiki bayan mako biyar. Suka ce “a’a!” Amma hakan bai dame ni ba don na riga na tsai da shawarata. Na yi farin ciki sosai da ban soma wannan aikin ba!

Bari matata ta ba da labarin abin da ta tuna game da hidimar da muka yi a Pine Bluff: “Na ji daɗin wa’azi sosai a wannan yankin! Ina nazari da mutane 15 zuwa 20. Mukan yi wa’azi gida-gida da safe kuma a wani lokaci mu yi nazari da mutane har ƙarfe 11 na dare. Mun ji daɗin wa’azi sosai! Da zan so a bar mu a wannan hidimar. A gaskiya, ban so yin hidimar kula da da’ira ba, amma hidimar da Jehobah yake so mu yi ke nan.”

LOKACIN DA MUKE HIDIMAR MAI KULA MAI ZIYARA

Mun cika fom na zama majagaba na musamman sa’ad da muke hidima a birnin Pine Bluff. Muna sa rai cewa za a ce mu soma hidimar domin mai kula da gunduma yana son mu taimaka ma wata ikilisiya da ke jihar Texas. Kuma yana so mu je wurin a matsayin majagaba na musamman. Mun so hakan sosai, amma mun yi ta jira mu samu wasiƙa daga hedkwatarmu amma hakan bai faru ba. Wata rana muka sami wasiƙa cewa mu soma hidimar mai kula da da’ira! Hakan ya faru a watan Janairu na 1965, kuma mu da Ɗan’uwa Leon Weaver mun soma hidimar a lokaci ɗaya. Yanzu Ɗan’uwa Weaver ne mai tsara ayyukan Kwamitin da Ke Kula da Ofisoshinmu a Amirka.

Na ji tsoron zama mai kula da da’ira don kafin wannan lokacin, mai kula da gunduma Ɗan’uwa James A. Thompson Ƙarami, ya bincika ko na cancanci yin wannan hidimar. Sai ya gaya mini inda nake bukatar in yi gyara, ya ambata halayen da nake bukatar kasancewa da su don in zama mai kula da da’ira da ya ƙware. Ban daɗe da zama mai kula da da’ira ba, sai na lura cewa wannan gargaɗin ya dace. Ɗan’uwa Thompson ne mai kula da gunduma na farko da muka yi hidima tare sa’ad da na soma kula da da’ira. Na koyi abubuwa da yawa daga wurin wannan ɗan’uwa mai aminci.

Ina godiya don yadda ’yan’uwa masu aminci suka taimaka mini

A wannan lokacin, ba a horar da masu kula da da’ira sosai. Na yi mako guda ina koya daga wurin mai kula da da’ira sa’ad da ya ziyarci wata ikilisiya. Bayan haka, shi ma ya yi mako ɗaya yana lura da yadda nake tafiyar da ikilisiyar sa’ad da na kai ziyara. Ya ba ni shawarwari kuma ya gaya mini abubuwan da za su taimaka mini, sai ya tafi ya bar mu. Na tuna cewa bayan ya tafi, na gaya wa matata cewa: “Bai kamata ya tafi yanzu ba don muna bukatar taimako.” Amma da shigewar lokaci, na fahimci cewa a kowane lokaci, za mu iya samun ’yan’uwan da za su taimaka mana idan mun ba su damar yin hakan. Har yanzu, ina godiya don taimakon ’yan’uwa kamar su J. R. Brown wanda yake hidimar kula da da’ira a lokacin da kuma Fred Rusk da ke hidima a Bethel.

A lokacin, nuna wariya ruwan dare gama gari ne. Akwai wata rana da ’yan ƙugiyar Ku Klux Klan suka zagaya wurin da muka kai ziyara a garin Tennessee. Ban da haka ma, na tuna wata rana da muka shiga gidan cin abinci sa’ad da muke wa’azi, sai na je bayan gida amma wani mutum ya biyo ni. Mutumin yana da zane-zane a jikinsa da ya nuna cewa ba ya son baƙaƙen fata. Amma wani ɗan’uwa da ya fi wannan mutum jiki ya bi mu kuma ya tambaye ni, “Ɗan’uwa Herd, lafiya ko?” Sai wannan mutumin ya fice ba tare yin amfani da bayan gidan ba. Da shigewar lokaci, na fahimci cewa ba launin fatar mutumi ne ainihi ke sa a nuna masa wariya ba, amma don zunubin da dukanmu muka gāda ne daga Adamu da Hauwa’u. Ƙari ga haka, na koyi cewa dukanmu ’yan’uwa ne ko da yaya launin fatarmu take kuma muna iya sadaukar da ranmu don juna.

SAKAMAKO MAI KYAU

Mun yi shekara 12 muna hidimar mai kula da da’ira, kuma mun yi shekara 21 a hidimar mai kula da gunduma. Mun ji daɗin hidimarmu kuma mun koyi abubuwa da yawa da suka ƙarfafa mu. Ban da haka, akwai wata albarka da muka samu. A watan Agusta na 1997, mun yi farin ciki sosai da aka gayyace mu hidima a Bethel da ke Amirka, bayan shekaru 38 da muke so mu yi hidimar. Mun soma hidima a Bethel a watan Satumba. Na yi tsammanin cewa ’yan’uwan da ke kula da ayyuka a Bethel suna so ne in yi hidima na ɗan lokaci, amma ba haka ba ne.

Har yanzu, Gloria tana da daraja sosai

A Sashen Kula da Hidima ne na soma aiki a Bethel kuma na koyi abubuwa da yawa a wurin. Rukunin dattawa da kuma masu kula da da’ira da ke ƙasar suna turo wa ’yan’uwan da ke aiki a wurin tambayoyi masu wuya sosai. Amma ina godiya don yadda ’yan’uwan da suka horar da ni suka yi haƙuri da ni kuma suka taimaka mini. Duk da haka, idan aka sake tura ni yin aikin a wurin, da akwai abubuwa da yawa da zan koya.

Ni da matata muna jin daɗin hidima a Bethel sosai. Da yake mun saba tashiwa da sassafe, hakan ya taimaka mana a Bethel. Bayan wajen shekara ɗaya, sai na soma hidima a matsayin Mataimakin Kwamitin Hidima na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Ƙari ga haka, a shekara ta 1999, aka naɗa ni memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. A wannan hidimar, na koyi abubuwa da yawa. Amma abin da ya fi muhimmanci da na koya shi ne cewa Yesu Kristi ne shugaban ikilisiya ba ɗan Adam ba.

Tun daga 1999, na sami gatar yin hidima a matsayin memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah

Idan na tuna yadda rayuwata take a dā, a wasu lokuta ina ji kamar yadda annabi Amos ya ji. Jehobah ya lura da wannan makiyayi mai tawali’u, wanda aikinsa shi ne kula da itatuwan durumi, wato abincin talakawa. Amma Allah ya zaɓe shi ya zama annabi, kuma ya albarkace shi sosai. (Amos 7:​14, 15) Hakazalika, duk da cewa ni ɗan manomi talaka ne daga garin Liberty a Indiana, Jehobah ya lura da ni kuma ya yi mini albarka sosai har da ba zan iya ambata su ba. (K. Mag. 10:22) Babu shakka, a cikin talauci na yi girma, amma yanzu, ni mai arziki ne sosai, wato ina da dangantaka mai kyau da Jehobah!