Kana Zuba Ido ga Jehobah Kuwa?
“A gare ka na ta da idanuna, ya kai mai zama a kujerar mulki cikin sammai.”—ZAB. 123:1.
WAƘOƘI: 143, 124
1, 2. Mene ne yake nufi mu zuba ido ga Jehobah?
MUNA rayuwa a “kwanakin ƙarshe” kuma muna shan “wahala sosai.” Rayuwa za ta ma daɗa wuya kafin Jehobah ya cire mugaye kuma ya mayar da duniya aljanna. (2 Tim. 3:1) Saboda haka, ya kamata mu yi wa kanmu wannan tambayar, ‘Ga wane ne nake dogara?’ Muna iya cewa, “Ina dogara ga Jehobah,” kuma amsar daidai ce.
2 Mene ne yake nufi mu zuba ido ga Jehobah? Kuma ta yaya za mu iya tabbatar da cewa muna dogara gare shi don ya magance matsalolinmu? Ƙarnuka da yawa da suka shige, wani marubucin zabura ya ambata muhimmancin zuba ido ga Jehobah don ya taimaka mana. (Karanta Zabura 123:1-4.) Ya ce idan muna zuba ido ga Jehobah, muna kamar bawan da ke dogara ga maigidansa. Mene ne marubucin zabura yake nufi da wannan furucin? Bawa yana dogara ga maigidansa don ya tanadar masa da abinci kuma ya kāre shi. Ƙari ga haka, yana bukatar ya riƙa kallon fuskar maigidansa a kowane lokaci don ya san abin da maigidansa yake bukata kuma ya yi su. Hakazalika, muna bukatar mu riƙa bincika Kalmar Allah don mu san abin da Jehobah yake bukata a gare mu kuma mu bi umurninsa. Yin hakan ne kaɗai zai sa mu tabbata cewa Jehobah zai taimaka mana sa’ad da muke da bukata.—Afis. 5:17.
3. Mene ne zai iya janye hankalinmu daga zuba ido ga Jehobah?
3 Ko da yake mun san cewa muna bukatar mu riƙa zuba ido ga Jehobah a kowane lokaci, amma wani abu yana iya janye hankalinmu a wasu lokuta. Abin da ya taɓa faruwa da Martha abokiyar Yesu ke nan. “Aikin abinci ya ɗauke mata hankali.” (Luk. 10:40-42) Idan hakan ya faru da wannan mace mai aminci a lokacin da Yesu yake tare da ita, kada mu yi mamaki cewa hakan zai iya faruwa da mu. Waɗanne abubuwa ne za su iya ɗauke hankalinmu daga zuba ido ga Jehobah? A wannan talifin, za mu tattauna yadda halayen wasu zai iya ɗauke hankalinmu. Za mu kuma koya yadda za mu ci gaba da zuba ido ga Jehobah.
WANI MUTUM MAI AMINCI YA RASA GATARSA
4. Me ya sa za mu iya mamaki cewa Musa ya rasa gatansa?
4 Babu shakka, Musa yana bin ja-gorancin Jehobah a kowane lokaci. Littafi Mai Tsarki ya ce Musa ya “jimre saboda yana ganin wanda ido ba ya iya gani.” (Karanta Ibraniyawa 11:24-27.) Ya ƙara da cewa “tun daga lokacin ba a taɓa yin wani annabi a Isra’ila kamar Musa ba, wanda Yahweh ya san shi fuska da fuska.” (M. Sha 34:10) Amma duk da cewa Musa yana da dangantaka mai kyau da Jehobah, ya rasa gatar shiga Ƙasar Alkawari. (L. Ƙid 20:12) Mene ne ya sa Musa ya rasa gatansa?
5-7. Wace matsala ce ta taso jim kaɗan bayan Isra’ilawa sun fita daga Masar, kuma yaya Musa ya bi da yanayin?
5 Isra’ilawa sun faɗa cikin babbar matsala wajen wata biyu da suka fita daga ƙasar Masar, kafin su kai Dutsen Sinai. Sai mutanen suka soma gunaguni game da rashin ruwa. Sun yi gunaguni ga Musa kuma yanayin ya yi tsanani sosai har Musa ya yi kuka ga Jehobah, ya ce: “Me zan yi wa jama’ar nan? Ga shi, suna a shirye su jejjefe ni da duwatsu.” (Fit. 17:4) A sakamakon haka, Jehobah ya ba Musa wani umurni kai tsaye. Ya gaya masa cewa ya ɗauki sandarsa ya bugi dutsen Horeb, kuma ruwa zai fito daga dutsen. Nassi ya ce: “A gaban dattawan Isra’ila Musa ya yi abin da Yahweh ya faɗa.” Sai Isra’ilawa suka sha suka ƙoshi kuma hankulansu ya kwanta.—Fit. 17:5, 6.
6 Littafi Mai Tsarki ya ci gaba da cewa Musa ya “kira wurin da suna ‘Massa,’ wato wurin gwaji, da kuma ‘Meriba,’ wato wurin muhawwara, saboda Isra’ilawa sun yi muhawwara da Musa sun gwada amincin Yahweh suna cewa, ‘Yahweh yana tare da mu ko babu?’” (Fit. 17:7) Sunayen sun dace domin suna nufin “Gwaji” da “Muhawwara.”
7 Yaya Jehobah ya ji game da abin da ya faru a Meriba? Ya ɗauki gunagunin a matsayin ƙalubale ga ikonsa, ba kawai gunaguni a kan Musa ba. (Karanta Zabura 95:8, 9.) Abin da Isra’ilawa suka yi bai dace ba ko kaɗan. Amma Musa ya yi abin da ya dace domin ya tuntuɓi Jehobah kuma ya nemi ja-gorancinsa.
8. Wace matsala ce ta faru jim kaɗan kafin Isra’ilawa su kammala yawo a cikin jeji?
8 Amma mene ne ya faru wajen shekara 40 sa’ad da irin wannan yanayin ya sake kunno kai? A lokacin, Isra’ilawa * A wurin, Isra’ilawa suka sake yin gunaguni game da rashin ruwa. (L. Ƙid 20:1-5) Amma a wannan lokacin, Musa ya yi kuskure mai tsanani.
sun kusan kammala yawo a cikin jeji. Sai Isra’ilawa suka sake kai wani wurin da aka soma kiran sa Meriba. Amma wannan wuri ne dabam da ke kusa da Kadesh, a iyakar Ƙasar Alkawari.9. Wane umurni ne aka ba Musa, amma mene ne ya yi? (Ka duba hoton da ke shafi na 12.)
9 Mene ne Musa ya yi sa’ad da mutanen suka soma gunaguni? Ya sake zuba ido ga Jehobah don ya ja-gorance shi. Amma a wannan lokacin, Jehobah bai gaya masa cewa ya bugi dutse ba. Jehobah ya gaya wa Musa cewa ya ɗauki sandarsa, ya tattara mutanen a gaban dutse kuma ya yi wa dutsen magana. (L. Ƙid 20:6-8) Amma Musa bai yi wa dutsen magana ba. Maimakon haka, cike da fushi ya ta da muryarsa ya ce: “Ya ku ’yan tawaye! Daga wannan dutse kuke so mu fito muku da ruwa?” Sai ya ɗaga sandarsa ya bugi dutsen sau biyu.—L. Ƙid 20:10, 11.
10. Yaya Jehobah ya ji sa’ad da Musa bai bi umurninsa ba?
10 Hakan ya sa Jehobah fushi sosai da Musa. (M. Sha 1:37; 3:26) Me ya sa Jehobah ya yi fushi? Akwai abubuwa da dama da wataƙila suka sa shi fushi. Kamar yadda aka ambata a baya, wataƙila Jehobah ya yi fushi domin Musa bai bi umurninsa ba.
11. Ta yaya yadda Musa ya bugi dutsen ya sa mutanen suka yi tunanin cewa ba Jehobah ne ya sa ruwa ya fito ba?
11 Da akwai wani dalili kuma da wataƙila ya sa Jehobah fushi. Duwatsun da ke wurin da Musa ya fara yin wannan mu’ujizar suna da ƙwari sosai. Ko da mutum ya bugi dutsen da dukan ƙarfinsa, ruwa ba zai fito ba. Amma ba haka yake da duwatsun da ke wancan Meriba ba. Yawancinsu farar ƙasa ce kuma tana yawan riƙe ruwa. Idan mutane suka haƙa rami a farar ƙasar, ruwa yana yawan fitowa. Saboda haka, sa’ad da Musa ya bugi dutsen maimakon ya yi masa magana, wataƙila Isra’ilawa sun yi zato cewa ruwan ya fito ne kawai daga farar ƙasa ba don Jehobah ya yi mu’ujiza ba. * Ba mu san ainihin gaskiyar lamarin ba.
YADDA MUSA YA YI RASHIN BIYYAYA
12. Mene ne kuma wataƙila ya sa Jehobah fushi da Musa da Haruna?
12 Akwai wani dalili kuma da wataƙila ya sa Jehobah ya yi fushi da Musa da kuma Haruna. Ka lura da abin da Musa ya gaya wa mutanen: ‘Daga wannan dutse kuke so mu fito muku da ruwa?’ Ta wajen yin amfani da kalmar nan “mu,” wataƙila Musa yana nufin cewa shi da Haruna ne suka yi mu’ujizar. Furucin Musa rashin kunya ne ga Jehobah don shi ne ya sa Musa ya yi mu’ujizar. Littafin Zabura 106:32, 33 ya ce: ‘Suka jawo fushin Yahweh a wajen ruwayen Meriba, Musa kuwa ya shiga uku saboda su, gama sun sa shi ɓacin rai har magana marar hankali ta fita daga bakinsa.’ * (L. Ƙid 27:14) Ko da yaya abin ya faru, Musa bai ɗaukaka Jehobah ba. Sai Jehobah ya gaya wa shi da Haruna cewa: “Kai da shi, kuka tayar wa umarnin da na ba ku.” (L. Ƙid 20:24) Hakan laifi ne babba!
13. Me ya sa yadda Jehobah ya yi wa Musa horo ya dace?
13 Jehobah yana bukatar Musa da Haruna su riƙa bin umurninsa domin su ne suke yi wa mutanensa ja-goranci. (Luk. 12:48) Akwai lokacin da Jehobah ya hana Isra’ilawa masu shekara ashirin zuwa sama shiga Ƙasar Alkawari saboda taurin kansu. (L. Ƙid 14:26-30, 34) Saboda haka, ba laifi ba ne cewa Jehobah ya hana Musa shiga Ƙasar Alkawari sa’ad da ya ƙi bin umurninsa. Jehobah ya yi masa horo yadda ya yi wa waɗancan Isra’ilawan.
ABIN DA YA JAWO MATSALAR
14, 15. Me ya sa Musa ya yi rashin biyayya?
14 Mene ne ya sa Musa ya yi rashin biyayya ga Jehobah? Ku sake lura da abin da Zabura 106:32, 33 ta ce: ‘Suka jawo fushin Yahweh a wajen ruwayen Meriba, Musa kuwa ya shiga uku saboda su, gama sun sa shi ɓacin rai har magana marar hankali ta fita daga bakinsa.’ Ko da yake Jehobah ne Isra’ilawa suka ɓata wa rai, amma Musa ne ya yi fushi. Rashin kamun kai ya sa ya yi magana a garaje ba tare da ya yi tunani a kan sakamakon ba.
15 Musa ya ƙyale halayen wasu ya hana shi zuba ido ga Jehobah. A lokaci na farko da batun rashin ruwa ya taso, Musa ya bi da batun yadda ya dace. (Fit. 7:6) Amma wataƙila ya gaji ne domin Isra’ilawa sun kwashi shekaru da yawa suna taurin kai. Wataƙila a lokacin, Musa ya soma tunani kawai a kan yadda yake ji, maimakon a kan yadda zai ɗaukaka Jehobah.
16. Me ya sa ya kamata mu yi bimbini a kan labarin Musa?
16 Idan annabi mai aminci kamar Musa ya yi laifi mai tsanani, babu shakka, hakan zai iya faruwa da mu. A lokacin, Musa yana gab da shigan Ƙasar Alkawari. Mu ma a yau muna gab da shigan aljannar da Jehobah ya yi mana alkawarin ta. (2 Bit. 3:13) Babu shakka, ba za mu ƙyale kome ya hana mu samun wannan gatan ba. Amma idan muna so mu cim ma hakan, wajibi ne mu zuba idanunmu ga Jehobah, mu riƙa yin nufinsa a kowane lokaci. (1 Yoh. 2:17) Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Musa?
KADA KU BAR HALAYEN WASU YA RABA HANKALINKU
17. Mene ne zai hana mu ramawa sa’ad da aka ɓata mana rai?
17 Kada ka yarda taƙaici ya shawo kanka. A wasu lokuta, muna iya fuskantar wata matsala sau da yawa. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada mu gaji da yin abin da yake da kyau. Gama idan ba mu gaji muka bar ƙoƙari ba, lokaci zai zo da za mu yi girbi mai albarka.” (Gal. 6:9; 2 Tas. 3:13) Idan wani abu ko kuma wani yana sa mu takaici a kai a kai, muna yin tunani kafin mu yi magana kuwa? (K. Mag 10:19; 17:27; Mat. 5:22) Idan wasu suka ɓata mana rai, mu ‘bar wa Allah ya rama mana da fushinsa.’ (Karanta Romawa 12:17-21.) Mene ne yin hakan yake nufi? Yana nufin cewa maimakon ramawa sa’ad da wani ya ɓata mana rai, mu bar Jehobah ya ɗauki mataki a daidai lokaci. Idan muka rama maimakon jiran Jehobah ya ɗauki mataki, hakan zai zama rashin kunya a gare shi.
18. Mene ne ya kamata mu tuna idan ya zo ga batun bin umurni?
Ibran. 13:17) Ƙari ga haka, za mu yi hankali don kada mu “wuce abin da aka rubuta.” (1 Kor. 4:6) Idan muna yin hakan, za mu nuna cewa muna zuba idanunmu ga Jehobah.
18 Mu bi sabon umurnin da aka ba mu. Shin muna bin sabon umurnin da Jehobah ya ba mu? Idan hakan ne, ba za mu riƙa yin abu yadda muka saba ba. Maimakon haka, za mu riƙa saurin bin duk sabon umurnin da Jehobah ya ba mu ta ƙungiyarsa. (19. Ta yaya za mu guji barin kurakuren wasu ya ɓata dangantakarmu da Jehobah?
19 Kada ka bari kurakuren wasu ya ɓata dangantakarka da Jehobah. Idan muna zuba idanunmu ga Jehobah, ba za mu yarda abubuwan da wasu suka yi ya ɓata mana rai ba ko kuma ya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Ya kamata ’yan’uwan da ke da gata a ƙungiyar Jehobah kamar Musa su fi mai da hankali sosai. Gaskiya ne cewa dukanmu muna bukatar mu yi aikin da zai sa mu sami ceto kuma mu yi shi “cikin tsoron Allah da kuma rawar jiki.” Amma mu tuna cewa Jehobah ba ya amfani da ƙa’ida guda wajen hukunta mu. (Filib. 2:12) Maimakon haka, idan mun sami ƙarin gata, Jehobah yana bukatar mu riƙa nuna misali mai kyau. (Luk. 12:48) Idan muna ƙaunar Jehobah da gaske, babu abin da ya isa ya sa mu yi tuntuɓe ko kuma ya hana shi ƙaunarmu.—Zab. 119:165; Rom. 8:37-39.
20. Mene ne ya kamata mu duƙufa cewa za mu riƙa yi?
20 Yanzu muna rayuwa a lokaci mai wuya sosai da ke cike da ƙalubale. Saboda haka, yana da muhimmanci mu riƙa zuba ido ga Jehobah wanda ke “zama a kujerar mulki cikin sammai.” Yin hakan zai sa mu san abubuwan da yake bukata a gare mu. Kada mu taɓa yarda halayen wasu ya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Abin da ya faru da Musa ya tabbatar mana da hakan. Maimakon haka, mu duƙufa cewa za mu zuba idanunmu a kan Jehobah “Allahnmu har sai ya yi mana jinƙai.”—Zab. 123:1, 2.
^ sakin layi na 8 Wannan Meriba dabam ne da wanda ke kusa da Rephidim da ake kira Massa. Amma an kira wuraren nan biyu Meriba saboda gunagunin da ya faru a wurin.—Ka duba taswirar da ke sashe na 7, shafi na 37 a ƙasidar nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah.
^ sakin layi na 11 Wani farfesa mai suna John A. Beck ya ce game da labarin: “Yahudawa suna gaya wa yaransu cewa masu tawayen ba su yarda cewa Musa ya yi wata mu’ujiza ba. Sun ce: ‘Musa ya san yanayin wannan dutsen! Saboda haka, idan yana so su gaskata da mu’ujizar, ya sake yin ta a wani dutse dabam.’ ” Amma wannan labari ne kawai.
^ sakin layi na 12 Ka duba Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 1987.