Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

‘Wane ne Na Jehobah?’

‘Wane ne Na Jehobah?’

“Sai ku ji tsoron Yahweh Allahnku, shi ne za ku yi masa sujada, shi ne za ku manne masa.”​—M. SHA 10:20.

WAƘOƘI: 28, 32

1, 2. (a) Me ya sa ya kamata mu zama na Jehobah? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

KASANCEWA na Jehobah abu ne mai muhimmanci sosai. Babu wata halitta a sama ko a duniya da ta fi Jehobah iko da hikima da kuma ƙauna! Babu shakka, dukanmu muna so mu zama bayin Jehobah. (Zab. 96:​4-6) Duk da haka, wasu sun daina bauta wa Jehobah sa’ad da suka fuskanci jarrabawar da ta bukaci su goyi bayansa.

2 A wannan talifin, za mu tattauna misalan wasu da suka yi da’awa cewa suna bauta wa Jehobah, amma duk da haka, suna ɓata masa rai. Misalan za su taimaka mana mu kasance da aminci sosai ga Jehobah.

JEHOBAH YANA BINCIKA ZUCIYARMU

3. Me ya sa Jehobah ya gargaɗi Kayinu, kuma me ya gaya masa?

3 Ku yi la’akari da misalin Kayinu. Jehobah ne kaɗai Kayinu yake bauta wa. Amma duk da haka, Jehobah bai amince da bautarsa ba. Me ya sa? Jehobah ya ga cewa Kayinu yana riƙe da mugunta a cikin zuciyarsa. (1 Yoh. 3:12) Jehobah ya gargaɗe shi cewa: “Idan ka yi abin da yake daidai, ba za ka saki fuskarka ba? Amma idan ba ka yi abin da yake daidai ba, to zunubi yana a ɓoye a bakin ƙofa yana marmari ya kama ka, amma dole ne ka yi mulki a kansa.” (Far. 4:​6, 7) A wannan ayar, Jehobah yana ja wa Kayinu kunne cewa, “Idan ka tuba kuma ka kasance kusa da ni, ni ma zan kasance kusa da kai.”

4. Mene ne Kayinu ya yi sa’ad da ya sami damar daidaita tunaninsa?

4 Jehobah zai amince da bautar Kayinu idan ya daidaita tunaninsa. Amma Kayinu bai bi shawarar ba. Tunani marar kyau da sha’awar banza sun motsa shi ya yi zunubi. (Yaƙ. 1:​14, 15) Sa’ad da Kayinu yake matashi, wataƙila bai taɓa tunanin cewa zai yi tsayayya da Jehobah ba. Amma da sannu a hankali, ya yi abin da bai taɓa mafarkin yi ba. Ya karya dokar Allah kuma ya kashe ƙanensa!

5. Wane irin tunani ne zai iya motsa mu mu yi zunubi?

5 A yau, Kirista zai iya bin misalin Kayinu ta wajen bauta wa Jehobah amma duk da haka, yana yin abubuwa da Jehobah ba ya so. (Yahu. 11) Alal misali, zai iya kasance da ƙwazo sosai a wa’azi kuma ya riƙa halartan taro a kai a kai. Amma duk da haka, zai iya ƙyale tunanin yin lalata da hadama da kuma ƙiyayya ga ’yan’uwansa Kiristoci su mamaye shi. (1 Yoh. 2:​15-17; 3:15) Yin irin wannan tunanin zai iya jawo zunubi. Wataƙila mutane ba su san tunaninmu ko kuma ayyukanmu ba. Amma Jehobah ya sani idan ba ma bauta masa da dukan zuciyarmu.​—Karanta Irmiya 17:​9, 10.

6. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana mu magance sha’awoyin banza?

6 Duk da kurakuren da muke yi, Jehobah ba ya saurin yasar da mu. Idan mun soma nisanta kanmu da shi, yana gaya mana cewa: “Ku juyo gare ni, ni kuwa zan koma gare ku.” (Mal. 3:7) Jehobah ya san cewa muna da wasu halayen da muke fama da su, amma zai dace mu guji yin munanan ayyuka. (Isha. 55:7) Idan mun yi hakan, ya yi alkawari cewa zai taimaka mana mu magance sha’awoyin banza.​—Far. 4:7.

“KADA FA A RUƊE KU!”

7. Ta yaya Sulemanu ya ɓata dangantakarsa da Jehobah?

7 Za mu iya koyan darussa sosai daga misalin Sarki Sulemanu. Sa’ad da yake matashi, ya nemi taimakon Jehobah. Saboda haka, Allah ya ba shi hikima sosai kuma ya ce ya gina masa babban haikali a Urushalima. Amma daga baya, dangantakarsa da Jehobah ta yi tsami. (1 Sar. 3:12; 11:​1, 2) Jehobah ya riga ya ba da doka cewa kada sarakunan Isra’ilawa su ‘tara wa kansu mata, domin kada su juya zuciyarsu daga Yahweh.’ (M. Sha 17:17) Sulemanu bai bi dokar nan ba, kuma daga baya ya auri mata 700. Ƙari ga haka, ya ƙaro ƙwarƙwara guda 300. (1 Sar. 11:3) Yawancin matansa ba Isra’ilawa ba ne kuma suna bauta wa allolin ƙarya. Haka ya nuna cewa Sulemanu ya karya dokar Allah da ta ce kada su auri matan da ba Isra’ilawa ba.​—M. Sha 7:​3, 4.

8. Waɗanne zunubai ne Sulemanu ya yi?

8 A kwana a tashi, sai Sarki Sulemanu ya daina bin dokokin Jehobah kuma ya soma yin munanan ayyuka. Sulemanu ya gina bagadi ga gunkin nan Ashtoret da Kemosh kuma shi da matansa suka soma bauta musu. Abin baƙin ciki, Sulemanu ya gina bagaden nan a wani dutse da ya fuskanci haikalin da ya gina wa Jehobah a Urushalima! (1 Sar. 11:​5-8; 2 Sar. 23:13) Wataƙila ya yi tunani cewa Jehobah ba zai yi fushi ba muddin ya ci gaba da miƙa masa hadaya a haikalinsa.

9. Mene ne ya faru don Sulemanu bai bi dokar Allah ba?

9 Amma Jehobah ba ya rufe idanunsa idan muna yin zunubi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh kuma ya yi fushi da Solomon saboda Sarki Solomon ya juya zuciyarsa daga bin Yahweh . . . , wanda ya bayyana a gare shi sau biyu. Yahweh kuma ya gargaɗi Solomon musamman kada ya yi sujada ga waɗansu alloli, amma Solomon bai yi biyayya da umarnin Yahweh ba.” A sakamakon haka, Jehobah ya yasar da shi. Daga baya, ’ya’yansa suka fuskanci mummunar sakamako. Ƙasarsu ta zama ƙabilu biyu kuma sun kwashi ɗarurruwan shekaru suna samun saɓani saboda filaye.​—1 Sar. 11:​9-13.

10. Mene ne zai iya ɓata dangantakarmu da Jehobah?

10 Misalin Sulemanu ya nuna cewa idan mun yi abokantaka da mutanen da ba su san dokar Allah ba ko kuma ba sa daraja ta, za su iya rinjayar mu. Zai iya yiwu cewa mutanen masu shela ne, amma ba su da dangantaka mai kyau da Jehobah. Wasu cikinsu danginmu ne da maƙwabtanmu da abokan aikinmu ko kuma abokan makarantarmu da ba sa bauta wa Jehobah. Idan mutanen da muke cuɗanya da su ba sa bin ƙa’idodin Jehobah, za su iya ɓata dangantakarmu da Allah.

Ta yaya abokanka suke shafan dangantakarka da Jehobah? (Ka duba sakin layi na 11)

11. Me zai taimaka mana mu san ko ya kamata mu rage yin cuɗanya da wasu mutane?

11 Karanta 1 Korintiyawa 15:33. Yawancin mutane suna da wasu halaye masu kyau, kuma mutane da yawa da ba Shaidun Jehobah ba ba sa yin munanan ayyuka. Idan ka san irin waɗannan mutanen, shin hakan yana nufin cewa su abokan kirki ne? Ka tambayi kanka: Ta yaya yin cuɗanya da su zai shafi dangantakata da Jehobah? Suna taimaka mini in daɗa kusantar Jehobah? Mene ne ya fi muhimmanci a gare su? Alal misali, suna yawan magana ne game da tufafin da ake yayinsa da kuɗi da na’urori da shaƙatawa ko kuma biɗan kayan duniya? Shin suna yawan yin baƙar magana game da mutane ko kuma maganganun batsa? Yesu ya yi gargaɗi cewa: “Ai, abin da yake cikin zuciya, shi yake fitowa a baki.” (Mat. 12:34) Idan ka lura cewa abokanka za su ɓata dangantakarka da Jehobah, ka rage yin cuɗanya da su ko kuma ka daina yin cuɗanya da su gabaki ɗaya.​—K. Mag 13:20.

JEHOBAH YANA SO MU BAUTA WA SHI KAƊAI

12. (a) Mene ne Jehobah ya bayyana wa Isra’ilawa jim kaɗan da barin ƙasar Masar? (b) Me suka ce sa’ad da Jehobah ya ce su bauta wa shi kaɗai?

12 Za mu kuma iya koyan darasi daga abin da ya faru bayan Jehobah ya ’yantar da Isra’ilawa daga ƙasar Masar. Mutanen sun taru a gaban Dutsen Sinai kuma Jehobah ya nuna musu ikonsa! Jehobah ya sa haɗari mai duhu ya bayyana. Bayan haka, aka soma walƙiya da hayaki kuma suka soma jin ƙarar ƙaho. (Fit. 19:​16-19) Sai Jehobah ya gaya musu cewa shi ‘Allah ne mai bukatar cikakkiyar ƙauna.’ Ya tabbatar musu da cewa zai nuna aminci ga waɗanda suke ƙaunar sa kuma suke kiyaye dokokinsa. (Karanta Fitowa 20:​1-6.) Wato Jehobah yana gaya wa Isra’ilawa cewa, “Idan kun kasance tare da ni, ni ma zan kasance tare da ku.” Da a ce kana wurin, za ka manne wa Jehobah kuwa? Babu shakka za ka yi abin da Isra’ilawa suka yi. Sun “amsa da murya ɗaya suka ce, ‘Dukan abubuwan da Yahweh ya faɗa, za mu yi.’” (Fit. 24:3) Amma ba da daɗewa ba, wani abu ya faru da ya jarraba amincinsu ga Jehobah. Wane abu ke nan?

13. Wane yanayi ne ya jarraba amincin Isra’ilawa?

13 Abubuwan da Isra’ilawa suka gani a dutsen ya tsorata su sosai har suka ce Musa ya hau dutsen ya ji abin da Jehobah zai faɗa. (Fit. 20:​18-21) Sa’ad da Musa ya hau dutsen, ya ɗan jima a wurin. Shin mutanen sun rasa na-yi ne da yake mai yi musu ja-goranci bai dawo ba? Babu shakka, mutanen sun dogara ainun da shugaba ɗan Adam. Sai hankalinsu ya tashi kuma suka ce wa Haruna: “Ka yi mana allolin da za su yi mana ja-gora, gama wannan Musa mutumin da ya fitar da mu daga ƙasar Masar, ba mu san abin da ya same shi ba.”​—Fit. 32:​1, 2.

14. Wane wawan tunani ne Isra’ilawa suka yi, kuma wane mataki ne Jehobah ya ɗauka?

14 Isra’ilawa sun san cewa bautar gumaka zunubi ne. (Fit. 20:​3-5) Amma ba da daɗewa ba, suka soma bauta wa ɗan maraƙi na zinariya! Ko da yake sun yi rashin biyayya ga Jehobah, amma sun yi zato cewa suna goyon bayan Jehobah. Har ma Haruna ya ce ɗan maraƙin da suke bauta wa “bikin sujada ga Yahweh” ne! Yaya Jehobah ya ji? Ransa ya ɓace. Jehobah ya gaya wa Musa cewa mutanen sun “ƙazantar da kansu. Sun yi saurin kaucewa daga hanyar da [Ya] umarce su su bi.” Jehobah ya yi ‘fushi’ sosai har ya so ya halaka Isra’ilawa gabaki ɗaya.​—Fit. 32:​5-10.

15, 16. Ta yaya Musa da Haruna suka nuna cewa suna goyon bayan Jehobah? (Ka duba hoton da ke shafi na 17.)

15 Amma Jehobah Allah ne mai jinƙai. Ya yanke shawara cewa ba zai halaka al’ummar ba. A maimakon haka, ya ba su damar nuna cewa suna so su kasance da shi. (Fit. 32:14) Sa’ad da Musa ya ga mutanen suna yin ihu da waƙa da kuma rawa a gaban gunkin, ya farfasa gunkin kuma ya niƙa shi. Sai ya ce: “A cikinku, wane ne na Yahweh? Ya zo wurina!” Sai ‘dukan Lawiyawa suka tattaru a wurin’ Musa.​—Fit. 32:​17-20, 26.

16 Ko da yake Haruna ne ya ƙera musu gunkin, amma ya tuba kuma ya bi Lawiyawan wajen goyon bayan Jehobah. Ba goyon bayan Jehobah kaɗai waɗannan mutane masu aminci suka yi ba, sun ware kansu daga masu yin munanan ayyukan. Sun yanke shawara mai kyau domin a ranar, dubban Isra’ilawa sun mutu. Amma mutanen da suka kasance da Jehobah sun tsira kuma ya ce zai albarkace su.​—Fit. 32:​27-29.

17. Wane darasi ne muka koya daga abin da Bulus ya faɗa a 1 Korintiyawa 10:​6, 7, 11, 12?

17 Wane darasi ne za mu iya koya daga wannan labarin? Manzo Bulus ya ba da gargaɗi cewa: “Waɗannan abubuwa sun zama mana misali ne domin kada mu . . . zama masu bautar gumaka yadda waɗansunsu suka zama.” An rubuta misalansu “don a yi mana gargaɗi, mu da ƙarshen zamani ya same mu. Saboda haka idan kana tsammani kana tsaye daram, to, sai ka yi hankali kada ka fāɗi.” (1 Kor. 10:​6, 7, 11, 12) Kamar yadda manzo Bulus ya ambata, bayin Jehobah ma za su iya yin munanan ayyuka. Bayan sun yi zunubi, suna iya yin tunanin cewa har ila, Jehobah yana amincewa da su. Amma son zama abokin Jehobah ko kuma yin da’awar cewa muna da aminci gare shi ba ya nufin cewa Jehobah ya amince da mu.​—1 Kor. 10:​1-5.

18. Mene ne zai iya sa mu nisanta kanmu daga Jehobah, kuma wane sakamako ne hakan zai iya jawowa?

18 Hankalin Isra’ilawa ya tashi sa’ad da suka lura cewa Musa bai sauko daga Dutsen Sinai ba. Hakazalika a yau, hankalin Kiristoci zai iya tashi domin ranar da Jehobah zai halaka miyagu da kuma lokacin da zai sabonta sama da duniya suna jinkirin zuwa. Muna kuma iya ganin cewa alkawuran da Jehobah ya yi mana tatsuniya ne. Idan ba mu yi hankali ba, wannan tunanin zai iya sa mu soma yin abin da muka ga dama, maimakon yin nufin Jehobah. Bayan haka, sai mu soma nisanta kanmu daga Jehobah kuma mu yi zunubin da ba mu taɓa tsammanin cewa za mu yi ba.

19. Me ya kamata mu riƙa tunawa, kuma me ya sa?

19 Ya kamata mu riƙa tunawa cewa Jehobah yana so mu bauta wa shi kaɗai kuma mu ba shi cikakkiyar ƙaunarmu. (Fit. 20:5) Idan ba mu yi hakan ba, to mu san cewa muna yin nufin Shaiɗan, kuma hakan zai jawo mana mummunar sakamako. Shi ya sa Bulus ya tunasar da mu cewa: “Ba dama ku sha kwaf na Ubangiji, ku kuma sha a na aljanu. Ba dama ku ci abinci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a na aljanu.”​—1 Kor. 10:21.

KU KUSACI JEHOBAH!

20. Ta yaya Jehobah zai iya taimaka mana ko da mun yi kuskure?

20 Kayinu da Sulemanu da kuma Isra’ilawa a Dutsen Sinai suna da zarafin yin ‘tuba su juyo ga Allah.’ (A. M. 3:19) Babu shakka, Jehobah ba ya saurin yasar da mutumin da ke zunubi. Ku tuna cewa Jehobah ya gafarta wa Haruna. A yau ma, Jehobah yana iya gargaɗe mu ta wajen yin amfani da labaran Littafi Mai Tsarki da littattafan da ke bayyana Nassosi ko kuma shawara daga ’yan’uwanmu Kiristoci. Idan mun bi gargaɗin, Jehobah zai nuna mana jinƙai domin idan kunne ya ji, to jiki ya tsira.

21. Me ya kamata mu ƙudurta cewa za mu yi idan an jarraba amincinmu ga Jehobah?

21 Da akwai dalilin da ya sa Jehobah yake nuna mana alheri. (2 Kor. 6:1) Alherinsa na ba mu zarafin nisanta kanmu daga “rayuwa marar halin Allah, da sha’awace-sha’awacen duniya.” (Karanta Titus 2:​11-14.) Da yake muna rayuwa a “duniyar nan,” dole ne mu fuskanci yanayin da zai jarraba amincinmu ga Jehobah. Saboda haka, mu ƙudurta cewa za mu ji tsoron Jehobah, mu ‘yi masa sujada, mu kuma manne masa.’​—M. Sha 10:20.