Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka San Gaskiyar Lamarin Kuwa?

Ka San Gaskiyar Lamarin Kuwa?

“Duk wanda ya amsa magana tun bai ji gaskiyar batun ba, wawanci ne a gare shi da abin kunya.”​—K. MAG. 18:​13, New World Translation.

WAƘOƘI: 126, 95

1, 2. (a) Wane hali mai muhimmanci ne ya kamata mu koya, kuma me ya sa? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

DUKANMU muna bukatar mu riƙa bincika wani batu sosai kafin mu san gaskiyar lamarin. (K. Mag. 3:​21-23; 8:​4, 5) Idan ba mu yi hakan ba, Shaiɗan da kuma wannan duniyar za su hana mu yin tunanin kirki. (Afis. 5:6; Kol. 2:8) Amma idan mun san gaskiyar lamarin, za mu tsai da shawarwari masu kyau. Littafin Karin Magana 18:13 ta ce, “duk wanda ya amsa magana tun bai ji gaskiyar batun ba, wawanci ne a gare shi da abin kunya.”

2 A wannan talifin, za mu tattauna abubuwan da suke sa ya yi wuya mu san gaskiyar wani batu kuma mu tsai da shawara mai kyau. Ƙari ga haka, za mu koyi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da kuma misalan da za su taimaka mana mu san yadda za mu riƙa sanin gaskiyar wani batu.

KADA KU GASKATA DA “KOME”

3. Me ya sa muke bukatar mu bi ƙa’idar da ke Karin Magana 14:15? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

3 A yau, muna samun bayanai daga wurare dabam-dabam. Mukan sami labarai daga intane ko talabijin da kuma wasu kafofin yaɗa labarai, kuma hakan ba shi da iyaka. Ban da haka, mutane da yawa suna yawan samun saƙo ta imel ko waya da kuma labarai daga abokansu. Amma muna bukatar mu mai da hankali sosai kuma mu riƙa tunani a kan wani labari don mu san ko labarin gaskiya ne. Yin hakan ya dace domin yaɗa labarin ƙarya ya zama ruwan dare gama gari. Wace ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ce za ta iya taimaka mana? Karin Magana 14:15 ta ce: “Marar tunani yakan gaskata kome, amma mai hankali yakan yi tunani kafin ya fara wani abu.”

4. Ta yaya Filibiyawa 4:​8, 9 zai taimaka mana sa’ad da muke zaɓan abin da muke son mu karanta, kuma me ya sa ya dace mu san gaskiyar wani batu? (Ka kuma duba akwatin nan “ Abubuwan da Za Su Taimaka Mana Mu San Gaskiya.”)

4 Muna bukatar mu san gaskiyar wani batu don mu tsai da shawarwari masu kyau. Saboda haka, ya kamata mu riƙa mai da hankali sosai sa’ad da muke zaɓan abin da za mu karanta. (Karanta Filibiyawa 4:​8, 9.) Bai kamata mu riƙa ɓata lokaci muna karanta labaran ƙarya a sashen labarai na intane ba ko kuma saƙon imel da ke yaɗa jita-jita. Ƙari ga haka, yana da muhimmanci mu guji dandalin da ake faɗin ra’ayin ’yan ridda. Me ya sa? Domin suna so su sa bayin Allah su daina bauta masa. Bayanin da ba gaskiya ba zai sa mu tsai da shawarar da ba ta dace ba. Saboda haka, kada mu yi tunanin cewa labarin ƙarya ba zai iya shafar mu ba.​—1 Tim. 6:​20, 21.

5. Wane labarin ƙarya ne Isra’ilawa suka ji, kuma yaya hakan ya shafe su?

5 Gaskata da labarin ƙarya zai iya jawo mummunan sakamako. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya faru a zamanin Musa sa’ad da ya aiki mutane 12 su je leƙen asirin Ƙasar Alkawari kuma mutane 10 cikinsu suka dawo da labarin ƙarya. (L. Ƙid. 13:​25-33) Labarin ya sa mutanen Jehobah sanyin gwiwa sosai. (L. Ƙid. 14:​1-4) Me ya sa mutanen suka yi sanyin gwiwa? Wataƙila suna ganin cewa tun da yake yawancin mutanen da suka je leƙen asirin ne suka ba da labarin, abin da suka faɗa gaskiya ne. Sun ƙi su saurari labarin da maza biyu masu aminci suka kawo, wato Joshuwa da Kaleb. (L. Ƙid. 14:​6-10) Maimakon su ji gaskiyar lamarin kuma su amince da Jehobah, sun zaɓi su gaskata da labarin ƙarya. Babu shakka, wannan wawanci ne!

6. Me ya sa bai kamata mu yi mamaki ba idan muka ji mugun labari game da mutanen Jehobah?

6 Me ya sa muke bukatar mu yi hattara sosai sa’ad da muka ji labari game da mutanen Jehobah? Domin Shaiɗan yana sūkar bayin Allah masu aminci. (R. Yar. 12:10) Shi ya sa Yesu ya yi mana gargaɗi cewa masu hamayya za su ‘tsananta muku, su kuma yi muku mugunta iri-iri saboda ni.’ (Mat. 5:11) Idan mun bi wannan gargaɗin, ba za mu yi mamaki ba sa’ad da muka ji mugun labarai game da mutanen Jehobah.

7. Me muke bukatar mu yi la’akari da shi kafin mu tura wani saƙo ta imel ko waya?

7 Kana yawan son tura wa abokanka saƙo ta imel ko waya? Idan haka ne, za ka iya so ka zama mutum na farko da zai tura labari mai ƙayatarwa da zarar ka gan shi a kafofin yaɗa labarai ko kuma ka ji shi a wani wuri. Amma kafin ka tura wannan saƙon, ka tambayi kanka: ‘Na tabbata cewa wannan labarin da nake so na yaɗa gaskiya ne? Na san gaskiyar lamarin kuwa?’ Idan ba ka tabbata ba, za ka yaɗa labarin ƙarya ga ’yan’uwanmu. Saboda haka, idan ba ka tabbata da wani labari ba, kada ka tura wa wani, amma ka share shi kawai.

8. Mene ne masu hamayya suka yi a wasu ƙasashe, kuma ta yaya za mu iya goyon bayansu?

8 Da akwai wani dalili kuma da ya sa bai dace mu riƙa saurin tura saƙo ta imel ko waya ba. An hana mu yin wa’azi a wasu ƙasashe, kuma masu hamayya a waɗannan ƙasashen suna iya yaɗa labarai da za su sa mu tsoro kuma mu daina amincewa da juna. Alal misali, a ƙasar Rasha ta dā, ’yan sandan ciki, wato KGB sun yaɗa ƙarya cewa ’yan’uwa maza masu ja-goranci a ƙungiyar Jehobah sun daina bauta wa Jehobah. * Abin baƙin ciki ne cewa ’yan’uwa da yawa sun gaskata da wannan ƙaryar, kuma suka bar ƙungiyar Jehobah. Da yawa cikinsu sun dawo daga baya, amma wasu ba su dawo ba don sun rasa bangaskiyarsu. (1 Tim. 1:19) Ta yaya za mu guji samun irin wannan mugun sakamako? Ya kamata mu guji yaɗa labarin ƙarya ko kuma rahoton da ba mu tabbatar da shi ba. Maimakon haka, ya kamata mu tabbata cewa mun san gaskiyar labarin da muke turawa.

RABIN GASKIYA

9. Mene ne kuma ya sa yake da wuya mu sami cikakken bayani?

9 A wasu lokuta, mukan ji labaran da ba a faɗi dukan abin da ya faru ba. Hakan zai sa ya yi mana wuya mu tsai da shawara mai kyau. Saboda haka, ba za mu iya tabbata da wani labarin da ba mu san ainihin abin da ya faru ba. Amma, me za mu iya yi don kada a yaudare mu da irin waɗannan labaran?​—Afis. 4:14.

10. Ta yaya Isra’ilawa suka kusan kai ma ’yan’uwansu hari, amma me ya sa ba su yi hakan ba?

10 Ka yi la’akari da abin da ya faru da Isra’ilawa da ke zama a yammacin Kogin Urdun a zamanin Yoshuwa. (Josh. 22:​9-34) Sun ji labari cewa Isra’ilawa da ke zama a gabashin Urdun, wato zuriyar Ruben da Gad da kuma rabin zuriyar Manasse sun gina babban bagadi kusa da Urdun. Gaskiya ne cewa sun gina bagadin. Amma da yake ba su san dalilin da ya sa suka gina shi ba, Isra’ilawan da ke zama a yammacin Urdun sun ɗauka cewa ’yan’uwansu sun karya dokar Jehobah. Saboda haka, Isra’ilawa da ke zama a yammacin Urdun suka taru don su yaƙi waɗanda suke zama a gabashin Urdun. (Karanta Joshuwa 22:​9-12.) Amma kafin su kai musu hari, sun tura wasu maza amintattu su je su ji gaskiyar lamarin. Mene ne mazan suka binciko? Sun gano cewa zuriyar Ruben da Gad da kuma rabin zuriyar Manasse sun gina bagadin ne don abin tunawa ba don miƙa hadayu ba. Ƙari ga haka, sun yi hakan domin a nan gaba, kowa ya sani cewa su ma sun kasance da aminci ga Jehobah. Babu shakka, waɗannan Isra’ilawan sun yi farin ciki sosai cewa rabin gaskiyar da suka ji bai sa su kashe ’yan’uwansu ba, amma sun yi bincike don su san gaskiya!

11. (a) Me ya sa aka yi wa Mefiboshet rashin adalci? (b) Mene ne zai hana Dauda yin wannan rashin adalcin?

11 Wataƙila mutane sun taɓa faɗin ƙarya game da kai kuma hakan ya ɓata maka rai. Ka yi la’akari da misalin Sarki Dawuda da Mefiboshet. Dawuda ya nuna wa Mefiboshet alheri da karimci ta wurin mai da masa dukan filayen kakansa, Saul. (2 Sam. 9:​6, 7) Amma daga baya, Dawuda ya ji labarin ƙarya game da Mefiboshet. Dawuda bai yi bincike don ya san gaskiyar labarin ba, sai ya ƙwace dukan dukiyar Mefiboshet. (2 Sam. 16:​1-4) Daga baya, Dawuda ya tattauna da Mefiboshet kuma Dawuda ya gano cewa ya yi kuskure. Sai ya mayar masa da wasu cikin dukiyarsa. (2 Sam. 19:​24-29) Da a ce Dawuda ya yi bincike don ya san gaskiyar lamarin, da bai ɗauki mataki a garaje ba.

12, 13. (a) Mene ne Yesu ya yi sa’ad da mutane suka yi ƙarya game da shi? (b) Me za mu iya yi idan wani ya yaɗa ƙarya game da mu?

12 Me za ka iya yi idan wani ya yaɗa ƙarya game da kai? Hakan ya faru da Yesu da kuma Yohanna Mai Baftisma. (Karanta Matiyu 11:​18, 19.) Mene ne Yesu ya yi? Bai yi amfani da duk lokacinsa da kuzarinsa don ya riƙa kāre kansa ba. Maimakon haka, ya ƙarfafa mutane su fi mai da hankali ga ayyukansa da koyarwarsa. Yesu ya ce: “Ana gane hikima . . . a ayyukanta.”​—Mat. 11:19.

13 Za mu iya koyan darasi mai kyau daga Yesu. A wasu lokuta, mutane suna iya faɗin abin da bai dace ba game da mu, kuma hakan yana iya ɓata sunanmu. Ƙari ga haka, muna iya neman a wanke sunanmu ko kuma son mu ɗauki wani mataki. Akwai wani abu ne za mu iya yi? Idan wani ya yaɗa ƙarya game da mu, muna iya yin rayuwa a hanyar da za ta sa mutane su ƙi gaskata da wannan ƙaryar. Kamar yadda muka koya daga Yesu, halinmu zai share dukan ƙaryace-ƙaryacen da aka yaɗa game da mu.

KA GASKATA DA KANKA AINUN?

14, 15. Me ya sa dogara ga kanmu zai iya zama mana tarko?

14 Mun ga cewa sanin gaskiyar wani batu yakan yi wuya ainun. Amma, wata matsala kuma ita ce ajizancinmu. Idan mun daɗe muna bauta wa Jehobah kuma fa? Wataƙila mun san yadda za mu bi da wasu batutuwa yadda ya dace. Kuma wasu suna daraja mu domin mun iya tsai da shawarwari masu kyau. Amma hakan zai iya zama mana tarko kuwa?

15 Ƙwarai kuwa, idan mun soma dogara da kanmu ainun. Ƙari ga haka, muna iya barin yadda muke ji da kuma ra’ayinmu su riƙa yi mana ja-goranci. Muna iya soma gaskata cewa mun fahimci wani yanayi ko da ba mu san gaskiyar lamarin ba. Hakan yana kawo mugun sakamako! Littafi Mai Tsarki ya yi mana kashedi cewa kada mu dogara ga ganewarmu.​—K. Mag. 3:​5, 6; 28:26.

16. A wannan misalin, mene ne ya faru a gidan cin abinci, mene ne Tanko ya kammala a zuciyarsa?

16 Ga misalin yadda hakan zai iya faruwa. A ce wata rana da yamma, wani dattijo mai suna Tanko ya yi mamaki sosai sa’ad da ya ga wani dattijo mai suna Yahaya ya zauna da wata a gidan cin abinci. Tanko ya lura cewa suna dariya kuma suna rungumar juna. Hakan ya dame shi sosai kuma ya soma tunani cewa: Yahaya yana so ya kashe aurensa ne? Mene ne zai faru da matar Yahaya? Yaran Yahaya kuma fa? Tanko ya taɓa ganin wasu da hakan ya faru da su da kuma sakamakon da hakan ya jawo. Yaya za ka ji da a ce kai ne Tanko?

17. A wannan misalin, mene ne Tanko ya gano daga baya, kuma wane darasi ne hakan ya koya mana?

17 Tanko ya san gaskiyar lamarin kuwa kafin ya kammala cewa Yahaya ya ci amanar matarsa? Da yammar, sai Tanko ya kira Yahaya a waya kuma ya gano cewa matar da ya gani ’yar’uwar Yahaya ce da ta ziyarce shi daga wani gari. Sun yi shekaru da yawa ba su ga juna ba. Amma tun da yake ba ta so ta daɗe a wurinsu, shi ya sa Yahaya ya je ya same ta don su ci abinci tare a gidan abinci. Kuma matar Yahaya ba ta iya raka shi zuwa wurin ba. Tanko ya yi farin ciki cewa bai gaya wa kowa abin da yake tunani ba. Mene ne muka koya daga wannan labarin? Ko mun daɗe muna bauta wa Jehobah, muna bukatar mu san gaskiyar wani batu kafin mu tsai da shawara.

18. Mene ne zai sa mu gaskata da labarin ƙarya game da ɗan’uwanmu?

18 Zai iya yi mana wuya mu bincika mu san gaskiyar lamarin idan batun ya shafi wani ɗan’uwa da muka sami saɓani da shi. Idan mun ci gaba da tunani game da matsalolinmu, za mu soma shakkar ɗan’uwanmu. Saboda haka, idan mun ji labarin ƙarya game da wannan ɗan’uwan, za mu gaskata da labarin. Mene ne hakan ya koya mana? Idan muka riƙe ’yan’uwanmu a zuciya, hakan zai sa mu gaskata da labarin ƙarya game da su. (1 Tim. 6:​4, 5) Bai kamata mu riƙe mutane a zuciya ba don muna kishin su. Maimakon haka, ya kamata mu san cewa wajibi ne mu riƙa ƙaunar ’yan’uwanmu kuma mu gafarta musu da dukan zuciyarmu.​—Karanta Kolosiyawa 3:​12-14.

BIN ƘA’IDODIN LITTAFI MAI TSARKI ZAI TAIMAKA MANA

19, 20. (a) Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka mana mu san gaskiyar wani labari? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

19 A yau yana da wuya mu san gaskiyar wani batu kuma mu tsai da shawarwari masu kyau. Me ya sa? Domin yawancin bayanai rabin gaskiya ne kuma mu ajizai ne. Mene ne zai taimaka mana? Wajibi ne mu san ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma mu bi su. Alal misali, wata ƙa’ida ita ce, duk wanda ya amsa magana tun bai ji gaskiyar batun ba, wawanci ne a gare shi da abin kunya. (K. Mag. 18:13) Wata kuma ta ce kada mu gaskata kome ba tare da sanin gaskiyar labarin ba. (K. Mag. 14:15) Ƙari ga haka, kada mu dogara ga kanmu ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah. (K. Mag. 3:​5, 6) Bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki zai kāre mu idan mun binciko gaskiyar wani batu kafin mu tsai da shawara.

20 Amma muna fuskantar wani ƙalubale. Ƙalubalen shi ne shari’anta mutane bisa abin da muka gani. A talifi na gaba, za mu bincika wasu hanyoyin da za mu iya yin wannan kuskuren da kuma yadda za mu guji yin sa.

^ sakin layi na 8 Ka duba littafin nan 2004 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 111-112, da kuma 2008 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 133-135.