Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Haƙuri Yana Sa Mu Kasance da Bege

Haƙuri Yana Sa Mu Kasance da Bege

DA YAKE muna “kwanakin ƙarshe,” rayuwa tana daɗa wuya sosai. Don haka, bayin Jehobah suna bukatar su daɗa zama masu haƙuri. (2 Tim. 3:​1-5) Muna rayuwa a duniyar da mutane suke son kansu da riƙe juna a zuciya kuma ba sa nuna kamun kai. Mutane masu irin waɗannan halayen ba su da haƙuri. Saboda haka, kowane Kirista yana bukatar ya tambayi kansa: ‘Ni marar haƙuri ne kamar mutanen duniya? Mene ne zama mai haƙuri yake nufi? Me zan yi don in zama mai haƙuri?’

ABIN DA YIN HAƘURI YAKE NUFI

Mene ne kalmar nan haƙuri da aka ambata a Littafi Mai Tsarki take nufi? Ba ta nufin jimre wata matsala kawai. Mutum mai haƙuri yana yin hakan ne da begen cewa abubuwa za su gyaru. Me ya sa? Domin mai haƙuri yakan dafa dutse ya sha romonsa. Ƙari ga haka, ba ya mai da hankali ga kansa kaɗai, amma yana la’akari da ra’ayin wasu kuma yana nuna ya damu su, har ma da waɗanda suka yi masa laifi. Yana da begen cewa dangantakarsa da mutumin za ta gyaru. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ambata “haƙuri” a cikin halaye masu kyau da ƙauna take sa mu kasance da su. * (1 Kor. 13:4) “Haƙuri” yana cikin “halin da ruhun Allah yake haifar” da su. (Gal. 5:​22, 23) Amma me muke bukatar mu yi don mu zama masu haƙuri?

YADDA ZA MU ZAMA MASU HAƘURI

Don mu zama masu haƙuri, muna bukatar mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhunsa mai tsarki. Allah yana ba waɗanda suka dogara gare shi ruhu mai tsarki. (Luk. 11:13) Ruhun Allah yana da iko sosai, amma muna bukatar mu yi aiki tuƙuru don mu yi abin da muka yi addu’a a kai. (Zab. 86:​10, 11) Hakan yana nufin cewa muna bukatar mu yi ƙoƙari don mu riƙa nuna haƙuri kowace rana. Amma a wasu lokuta, kasancewa masu haƙuri yana da wuya. Me kuma zai taimaka mana?

Muna iya zama masu haƙuri ta wajen bin misalin Yesu. A lokacin da manzo Bulus yake magana game da ‘sabon hali’ wanda ya ƙunshi “haƙuri,” ya ƙarfafa mu cewa mu ‘bari salama ta Almasihu ta yi mulki a zuciyarmu.’ (Kol. 3:​10, 12, 15) Idan muna so mu yi hakan, muna bukatar mu bi misalin Yesu kuma mu kasance da bangaskiya cewa Jehobah zai daidaita al’amuran da ke damunmu. Idan muna bin misalin Yesu, ba za mu yi rashin haƙuri ba ko da mene ne ya faru.​—Yoh. 14:27; 16:33.

Duk da cewa mun ƙosa ganin cikar alkawuran Jehobah, idan muka tuna yadda Jehobah yake yin haƙuri da mu, hakan zai sa mu zama masu haƙuri. Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbaci cewa: Jehobah ba ya “jan jiki game da cika alkawarinsa. Ai, ba haka ba ne. Haƙuri yake yi da ku. Ba ya so wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.” (2 Bit. 3:9) Idan muka yi tunanin yadda Jehobah yake haƙuri da mu, hakan zai motsa mu mu riƙa haƙuri da wasu. (Rom. 2:4) A waɗanne lokuta ne muke bukatar mu zama masu haƙuri?

LOKUTAN DA MUKE BUKATAR HAƘURI

Abubuwa da yawa suna iya sa mu kasa kasancewa da haƙuri. Alal misali, idan kana da abu mai muhimmanci da kake so ka faɗa, kana bukatar ka yi haƙuri don kada ka katse wa wasu magana. (Yaƙ. 1:19) Ban da haka, kana bukatar haƙuri idan wani yana yin abin da ke ci maka rai. Maimakon barin hakan ya sa ka fushi, kana bukatar ka yi la’akari da yadda Jehobah da Yesu suke bi da mu duk da kasawarmu. Ba sa mai da hankali ga kurakuren mu. A maimakon haka, suna mai da hankali ga halayenmu masu kyau. Suna lura da ƙoƙarin da muke yi don mu guji yin abin da bai dace ba.​—1 Tim. 1:16; 1 Bit. 3:12.

Wani abu kuma da zai iya sa mu fushi shi ne idan wani ya ce mun yi ko kuma mun faɗi abin da bai dace ba. Hakan yana iya sa mu fushi kuma mu so kāre kanmu. Amma Kalmar Allah ta ambata wani abu dabam da muke bukatar mu yi. Ta ce: “Kada ka zama mai saurin fushi, gama wawa ne mai cike da fushi.” (M. Wa. 7:​8, 9) Saboda haka, ko da abin da aka faɗa game da mu ba gaskiya ba ne, muna bukatar mu yi haƙuri kuma mu yi tunani sosai kafin mu mayar da martani. Abin da Yesu ya yi ke nan a lokacin da wasu suka yi ƙarya game da shi.​—Mat. 11:19.

Iyaye musamman suna bukatar su kasance masu haƙuri sa’ad da suke so su taimaka wa yaransu su canja ra’ayinsu ko kuma su guji sha’awar banza. Ka yi la’akari da labarin wani ɗan’uwan mai suna Mattias da ke hidima a Bethel a Turai. A lokacin da yake matashi, abokan makarantarsa suna yawan zolayar sa domin imaninsa. Da farko, iyayensa ba su san abin da ke faruwa ba, amma sun lura cewa ɗansu ya soma shakkar abin da ya yi imani da shi. Gillis mahaifin Mattias ya ce: “Ni da matata mun bukaci haƙuri sosai a wannan yanayin.” Mattias yakan yi wa iyayensa irin waɗannan tambayoyin, “Wane ne Allah? Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ne kuwa? Ta yaya kuka san cewa Allah yana son mu yi wannan ko wancan?” Ban da haka ma, yakan gaya wa mahaifinsa cewa: “Me zai sa a shari’anta ni domin ban gaskata da abin da kuka gaskata da shi ba?”

Gillis ya ce: “A wasu lokuta, da fushi ne ɗanmu ke yin waɗannan tambayoyin. Amma ba da ni ko mahaifiyarsa yake fushi ba, yana fushi ne domin yana ganin cewa imaninmu yana sa a tsananta masa.” Ta yaya Gillis ya magance wannan matsalar? Ya ce: “Ni da ɗana mukan ɗau sa’o’i muna tattaunawa. Amma a yawanci lokaci, saurarar sa nake yi sa’an nan in yi masa tambayoyi don in fahimci yadda yake ji. A wasu lokuta ina bayyana masa wasu abubuwa, sai in bar shi ya yi tunani na kwana ɗaya ko fiye da hakan kafin mu sake tattauna batun. A wasu lokuta kuma nakan gaya masa ina bukatar lokaci don in yi tunani a kan abin da ya faɗa. Ta irin wannan tattaunawa da muke yi a kai a kai, Mattias ya soma fahimtar koyarwa game da fansa da abin da ya sa Jehobah ne ya cancanci yin sarauta da kuma irin ƙaunar da yake mana. Duk da cewa yin hakan ya ɗau lokaci, a hankali ɗanmu ya soma ƙaunar Jehobah. Ni da matata muna farin ciki cewa haƙurin da muka yi sa’ad da muke taimaka wa ɗanmu bai bi ruwa ba.”

Gillis da matarsa sun dogara ga Jehobah yayin da suke ƙoƙarin taimaka wa ɗansu. Gillis ya ce: “Nakan gaya wa Mattias cewa ƙauna ce ke motsa ni da mahaifiyarsa mu roƙi Jehobah ya taimaka masa ya fahimci gaskiya.” Babu shakka, waɗannan iyayen suna farin ciki domin sun kasance da haƙuri!

Muna bukatar haƙuri yayin da muke kula da wani a iyalinmu ko kuma abokinmu da ke rashin lafiya mai tsanani. Ka yi la’akari da labarin wata mai suna Ellen * da take zama a Turai.

Wajen shekaru takwas da suka shige, mijin Ellen ya yi rashin lafiyar da ta shafi ƙwaƙwalwarsa. A sakamakon haka, ya daina jin tausayi da yin farin ciki da kuma baƙin ciki. Kula da shi ya yi wa Ellen wuya. Ta ce: “Na bukaci yin haƙuri da kuma addu’a sosai.” Ta ƙara da cewa: “Ayar da take ƙarfafa ni sosai ita ce Filibiyawa 4:13 da ta ce: ‘Zan iya yin kome ta wurin . . . wanda yake ƙarfafa ni.’” Da taimakon Jehobah, Ellen ta yi haƙuri kuma ta jimre da wannan yanayin.​—Zab. 62:​5, 6.

KU ZAMA MASU HAƘURI KAMAR JEHOBAH

Babu shakka, Jehobah ne ya fi kafa misali mai kyau na yin haƙuri. (2 Bit. 3:15) Da akwai labarai da yawa a Littafi Mai Tsarki da suka nuna lokutan da Jehobah ya kasance da haƙuri. (Neh. 9:30; Isha. 30:18) Alal misali, mene ne Jehobah ya yi a lokacin da Ibrahim ya tambaye shi dalilin da ya sa yake so ya halaka Saduma? Da farko, Jehobah bai katse wa Ibrahim magana ba. A maimakon haka, ya yi haƙuri kuma ya saurari dukan tambayoyin da Ibrahim ya yi. Bayan haka, Jehobah ya nuna masa cewa ya ji abin da ya faɗa. Ya tabbatar masa da cewa ba zai halaka Saduma ba idan aka sami mutane masu adalci guda goma a cikinta. (Far. 18:​22-33) Hakika, wannan misali ne mai kyau na nuna haƙuri ba tare da yin fushi ba!

Haƙuri yana cikin sababbin halaye masu muhimmanci da Kiristoci suke bukatar su kasance da su. Idan muka yi aiki tuƙuru don mu zama masu haƙuri, hakan zai nuna cewa muna daraja Ubanmu na sama, wato Jehobah. Ƙari ga haka, za mu kasance cikin mutanen da “suka yi haƙuri har suka karɓi abin da Allah ya yi alkawari zai ba su.”​—Ibran. 6:​10-12.

^ sakin layi na 4 An tattauna game da ƙauna a talifi na farko cikin jerin talifofi guda tara game da ’ya’yan ruhu.

^ sakin layi na 15 An canja wasu sunaye.