Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

In “Kun San Wadannan Abubuwa, Za Ku Zama Masu Albarka Idan Kun Yi Su”

In “Kun San Wadannan Abubuwa, Za Ku Zama Masu Albarka Idan Kun Yi Su”

“Abincina shi ne in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.”​—YOH. 4:34.

WAƘOƘI: 80, 35

1. Ta yaya halin son kai na mutanen duniya zai iya shafan mu?

ME YA sa yake mana wuya mu riƙa yin abin da muke koya a Kalmar Allah? Dalili ɗaya shi ne, muna bukatar mu zama masu tawali’u kafin mu iya yin abin da ya dace. A wannan “kwanakin ƙarshe,” yana da wuya mu zama masu tawali’u domin muna zama tare da “masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai” da mutanen da ba sa “kame kansu.” (2 Tim. 3:​1-3) A matsayinmu na bayin Allah, mun san cewa irin waɗannan halayen ba su dace ba, amma a wasu lokuta muna iya ganin cewa mutanen da ke da irin waɗannan halayen suna samun ci gaba. (Zab. 37:1; 73:3) Muna iya soma tunani: ‘Shin ya dace in yi ƙoƙarin biyan bukatun wasu kafin nawa? Idan na ƙaskantar da kaina, mutane za su ci gaba da daraja ni?’ (Luk. 9:48) Idan muka bar halayen mutanen duniya su shafe mu, hakan zai ɓata dangantakarmu da ’yan’uwa. Ƙari ga haka, zai yi wa mutane wuya su san cewa mu Kiristoci ne. Amma za mu sami albarka sosai idan muka yi nazarin misalan mutane masu tawali’u da ke Littafi Mai Tsarki kuma muka bi su.

2. Mene ne za mu iya koya daga bayin Allah masu aminci?

2 Mene ne ya taimaka wa mutane masu aminci su zama abokan Allah? Ta yaya suka yi abin da ya faranta wa Allah rai? Kuma ta yaya suka sami ƙarfin yin abin da ya dace? Idan muka karanta labarinsu kuma muka yi bimbini a kai, hakan zai ƙarfafa bangaskiyarmu.

ABUBUWAN DA KE ƘARFAFA BANGASKIYARMU

3, 4. (a) Ta yaya Jehobah yake koyar da mu? (b) Me ya sa muka ce ba samun ilimi kaɗai muke bukata don ƙarfafa bangaskiyarmu ba?

3 Jehobah yana yi mana tanadin abubuwan da suke ƙarfafa bangaskiyarmu. Don ya koyar da mu, yana yin amfani da Littafi Mai Tsarki da littattafan da ke bayyana Kalmarsa da dandalin jw.org da Tashar JW da taron ikilisiya da kuma manyan taro. Amma abin da Yesu ya ambata a littafin Yohanna 4:34 ya nuna cewa ba samun ilimi kaɗai muke bukata ba. Ya ce: ‘Abincina shi ne in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.’

4 A wajen Yesu, yin nufin Allah kamar abinci ne. Ta yaya? Kamar yadda muke samun ƙoshin lafiya idan muka ci abinci mai kyau, haka ma yin nufin Allah yake sa bangaskiyarmu ta yi ƙarfi. Alal misali, wataƙila ka gaji ainun kafin ka halarci taron fita wa’azi, amma bayan ka dawo daga wa’azin sai ka ji ka sami ƙarfi kuma ka warware.

5. Ta yaya za mu amfana idan muna da hikima?

5 Mu masu hikima ne idan muna yin abin da Jehobah yake so. (Zab. 107:43) Waɗanda suke da hikima suna amfana sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba abin da za a gwada da ita. . . . Itacen rai ce ga waɗanda suka same ta, masu albarka ne waɗanda suka riƙe ta.” (K. Mag. 3:​13-18) Yesu ya ce: In kun “san waɗannan abubuwa za ku zama masu albarka idan kun yi su.” (Yoh. 13:17) Mabiyan Yesu za su yi farin ciki idan suka ci gaba da yin abubuwan da ya gaya musu. Suna bukatar su riƙa yin abubuwan da ya koya musu a rayuwarsu na yau da kullum.

6. Me ya sa muke bukatar mu riƙa yin amfani da abubuwan da muke koya?

6 A yau, ya kamata mu riƙa yin amfani da abubuwan da muke koya. Alal misali, makaniki yana da ilimi da kuma kayan aiki da yawa. Duk da haka, ba zai amfana ba idan ba ya amfani da waɗannan abubuwan. Wataƙila ya daɗe yana yin wannan aikin, amma yana bukatar ya ci gaba yin aikin idan yana so ya ƙware sosai. Hakazalika, mun yi farin ciki sosai a lokacin da muka koyi gaskiya domin mun yi amfani da abubuwan da muka koya. Amma idan muna son mu ci gaba da yin farin ciki, muna bukatar mu riƙa yin abubuwan da Jehobah yake koya mana.

7. Mene ne za mu iya koya daga labaran Littafi Mai Tsarki?

7 A wannan talifin, za mu tattauna wasu abubuwa da za su iya sa kasancewa da tawali’u ya yi mana wuya. Ban da haka, za mu ga yadda bayin Allah a zamanin dā suka yi nasara sa’ad da suka fuskanci irin yanayin. Amma muna bukatar mu yi tunani sosai a kansu don mu san yadda za mu yi amfani da darussan a rayuwarmu.

KADA KA ƊAUKAKA KANKA

8, 9. Mene ne labarin da ke Ayyukan Manzanni 14:​8-15 ya nuna game da Bulus? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)

8 Allah yana son “dukan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:4) Yaya kake ɗaukan mutanen da ba su san gaskiya ba? Manzo Bulus ya yi wa Yahudawan da suka san wasu abubuwa game da Jehobah wa’azi. Amma ya yi wa mutane da suke bauta wa gumaka ma wa’azi. Yadda mutanen suka ɗaukaka Bulus zai nuna ko shi mai tawali’u ne da gaske.

9 A lokaci na farko da Bulus ya je wa’azi a ƙasar waje, shi da Barnaba sun je birnin Listira. Mutanen Likoniya da ke zama a birnin sun ɗauki Bulus da Barnaba a matsayin alloli har suka soma kiran su da sunayen allolinsu, wato Zafsa da Harmasa. Shin hakan ya burge Bulus da Barnaba ne? Sun ɗauki wannan yanayin a matsayin canji daga tsanantawar da suka fuskanta a wasu biranen da suka je ne? Bulus da Barnaba sun yi tunanin cewa yadda mutanen ke ɗaukaka su zai taimaka ma wasu su ji wa’azi ne? A’a! Abin ya ɓata musu rai har suka yayyage tufafinsu kuma suka ce wa mutanen: “Don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kamarku.”​—A. M. 14:​8-15.

10. Me ya sa Bulus da Barnaba suke ganin ba su fi mutanen Likoniya daraja ba?

10 Sa’ad da Bulus da Barnaba suka ce “mu ma mutane ne kamarku,” suna nufin cewa su ajizai ne. Ba sa nufin cewa bautarsu da na mutanen Likoniya ɗaya ne. Allah ne ya tura Bulus da Barnaba su je wa’azi a ƙasar waje. (A. M. 13:2) Allah ya shafe su da ruhu mai tsarki kuma suna da begen zuwa sama. Amma hakan ba ya nufin cewa sun fi mutanen daraja. Sun san cewa mutanen ma za su iya samun begen yin rayuwa a sama idan suka gaskata da abin da suka ji.

11. Sa’ad da muke wa’azi, ta yaya za mu yi koyi da yadda Bulus ya nuna tawali’u?

11 Ta yaya za mu iya bin misalin Bulus? Da farko, muna bukatar mu guji neman ɗaukaka don abubuwan da Jehobah ya taimaka mana mu cim ma. Kowannenmu yana bukatar ya tambayi kansa: ‘Yaya nake ɗaukan mutanen da nake ma wa’azi? Shin ina nuna bambanci ga wasu mutane a yankinmu?’ A dukan faɗin duniya, Shaidun Jehobah suna iya ƙoƙarinsu don su san yarukan da ake yi a yankunansu domin suna so su taimaka wa mutane da yawa su san gaskiya. A wasu lokuta, hakan yana nufin koyon yare da al’adar mutanen da ake musu kallon reni. Ba zai dace su riƙa ganin sun fi irin waɗannan mutane daraja ba. A maimakon haka, sun yi ƙoƙari don su fahimci kowane mutum kuma su koya masa game da Mulkin Allah a hanyar da za ta ratsa zuciyarsa.

KA AMBATA SUNAYEN WASU SA’AD DA KAKE ADDU’A

12. Ta yaya Abafaras ya nuna cewa ya damu da wasu?

12 Wata hanya kuma da za mu nuna cewa mu masu tawali’u ne ita ce ta wajen yin addu’a a madadin “waɗanda suka sami bangaskiya mai daraja kamar yadda mu ma muka samu.” (2 Bit. 1:1) Abin da Abafaras ya yi ke nan. Sau uku ne kaɗai aka ambata sunansa a littattafan da Bulus ya rubuta. A lokacin da aka tsare Bulus a gida a Roma, ya rubuta wasiƙa ga Kiristocin da ke Kolosi cewa Abafaras ‘yana kokawa cikin addu’a ga Allah domin ku tsaya daram.’ (Kol. 4:12) Abafaras ya san ’yan’uwan sosai kuma ya damu da su. Duk da cewa Abafaras yana “cikin kurkuku tare da” Bulus, hakan bai hana shi damuwa da wasu ba. (Fil. 23) Kuma ya yi iya ƙoƙarinsa don ya taimaka musu. Hakan ya nuna cewa ba ya son kansa kawai. Yin addu’a a madadin bayin Allah yana da muhimmanci sosai musamman ma idan muka ambata sunayensu.​—2 Kor. 1:11; Yaƙ. 5:16.

13. Ta yaya za ka iya bin misalin Abafaras a addu’arka?

13 Ka yi tunanin waɗanda za ka ambata sunayensu a addu’arka. Kamar Abafaras, ’yan’uwa da yawa suna yin addu’a a madadin abokansu da kuma wasu iyalai da ke fuskantar matsaloli. Don wataƙila suna da wata shawara mai wuya da suke bukatar su yanke ko kuma suna fuskantar gwaji. Ƙari ga haka, da yawa suna addu’a don Jehobah ya taimaka wa ’yan’uwan da aka ambata sunayensu a talifin da ke jw.org mai jigo, “Shaidun Jehobah da Aka Tsare a Kurkuku Saboda Imaninsu.” (Ka duba ƊAKIN WATSA LABARAI > LABARAN SHARI’A.) Ban da haka ma, zai dace mu tuna waɗanda aka yi musu rasuwa da waɗanda bala’i ta shafe su da waɗanda ake yaƙi a ƙasarsu da kuma waɗanda suke fama da talauci. Babu shakka, da akwai ’yan’uwa da yawa da suke bukatar mu yi addu’a a madadinsu. Yin hakan yana nuna cewa mun damu da su ba kanmu kaɗai ba. (Filib. 2:4) Jehobah yana amsa irin waɗannan addu’o’in.

KA ZAMA “MAI SAURIN JI”

14. Ta yaya Jehobah ya kafa misali mai kyau a saurarar wasu?

14 Wani abu kuma da zai nuna cewa mu masu tawali’u ne shi ne saurarar mutane yayin da suke magana. Littafin Yaƙub 1:19 ya ƙarfafa mu cewa mu ‘kasance masu saurin ji.’ Jehobah ya kafa misali mai kyau a wannan batun. (Far. 18:32; Josh. 10:14) Bari mu yi la’akari da darussan da za mu iya koya daga abin da ke littafin Fitowa 32:​11-14. (Karanta) Duk da cewa Jehobah ba ya bukatar shawarar Musa, ya saurare shi yayin da yake gaya masa abin da ke zuciyarsa. Shin za ka iya saurarar mutumin da ke yin kuskure har ma ka bi shawararsa? Jehobah yana saurarar mutanen da ke addu’a da bangaskiya.

15. Ta yaya daraja mutane zai nuna cewa muna yin koyi da Jehobah?

15 Kowannenmu yana bukatar ya tambayi kansa: ‘Idan har Jehobah zai iya ƙasƙantar da kansa don ya saurari mutane kamar su Ibrahim da Rahila da Musa da Yoshuwa da Manowa da Iliya da kuma Hezekiya, shin ba zai dace ni ma in riƙa yin hakan ba? Akwai wani a ikilisiya ko kuma a iyalinmu da nake bukatar in riƙa saurara? Wane mataki ne nake bukatar in ɗauka?’​—Far. 30:6; Alƙa. 13:9; 1 Sar. 17:22; 2 Tar. 30:20.

“WATAƘILA YAHWEH ZAI DUBA WANNAN WULAƘANCINA”

Dawuda ya ce: “Ku bar shi!” Mene ne za ka yi da a ce kai ne? (Ka duba sakin layi na 16, 17)

16. Mene ne Sarki Dawuda ya yi sa’ad da Shimeyi ya ɓata masa rai?

16 Tawali’u yana taimaka mana mu kame kanmu sa’ad da wani ya ɓata mana rai. (Afis. 4:2) Za mu iya ganin misalin hakan a littafin 2 Sama’ila 16:​5-13. (Karanta) Dawuda da bayinsa sun fuskanci rashin adalci daga hannun Shimeyi ɗan’uwan Sarki Saul wanda ya zagi Dawuda har da kai masa hari. Dawuda ya haƙura duk da cewa yana da ikon ɗaukan mataki. Ta yaya Dawuda ya sami ƙarfin kame kansa? Za mu iya samun amsar idan muka yi nazarin Zabura sura ta uku.

17. Mene ne ya taimaka wa Dawuda ya kame kansa, kuma ta yaya za mu iya yin koyi da shi?

17 Rubutu na sama a littafin Zabura sura ta uku ya bayyana cewa Dawuda ya rubuta Zaburar ne a “lokacin da ya gudu daga ɗansa Absalom.” Aya ta 1 da 2 sun yi daidai da abin da ke littafin 2 Sama’ila sura 16. A littafin Zabura 3:​4, Dawuda ya ce: “Ga Yahweh nakan yi kira don taimako yakan kuwa amsa mini daga Tudunsa Mai Tsarki.” Mu ma muna iya yin addu’a sa’ad da aka yi mana rashin adalci. Jehobah zai ba mu ruhun mai tsarki don ya taimaka mana mu jimre. Shin za ka kame kanka idan wani ya ɓata maka rai kuma ka gafarta masa? Kana da gaba gaɗi cewa Jehobah yana ganin wulaƙancin da kake fuskanta kuma zai taimaka maka, ya albarkace ka kuma?

“MUHIMMIN ABU SHI NE SAMUN HIKIMA”

18. Ta yaya za ka amfana idan kana yin amfani da abubuwan da kake koya?

18 Za mu sami albarka sosai idan muna yin abubuwan da muka san sun dace. Shi ya sa littafin Karin Magana 4:7 ya ce: “Muhimmin abu shi ne samun hikima”! Ko da yake zama mai hikima ya dangana ne ga abubuwan da muka sani, shawarwarin da muke yankewa ne za su nuna ko mu masu hikima ne. Kiyashi ma suna da hikima domin suna tara abinci a lokacin rani. (K. Mag. 30:​24, 25) Kristi wanda shi ne “hikimar Allah” yana yin abin da ke faranta wa Allah rai a koyaushe. (1 Kor. 1:24; Yoh. 8:29) Allah zai yi mana albarka idan mu ma muka kasance masu tawali’u kuma muka ci gaba da nuna hikima ta wajen yin abin da ya dace. (Karanta Matiyu 7:​21-23.) Don haka, ka ci gaba da yin iya ƙoƙarinka don ka taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya su kasance masu tawali’u. Yin amfani da abubuwan da muke koya yakan ɗauki lokaci sosai kuma yana bukatar haƙuri, amma idan muka zama masu tawali’u hakan zai sa mu farin ciki yanzu da kuma har abada.