Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Me ya taimaka wa Istifanus ya natsu sa’ad da ake tsananta masa?

ISTIFANUS yana gaban mutane masu adawa da shi. Yana gaban Majalisa, wato kotu mafi girma a Isra’ila kuma alƙalai 71 mafi iko a al’ummar ne suke shari’ar. Babban Firist Kayafa ne ya tara su, kuma shi ne ya ja-goranci shari’a da aka yi wa Yesu ’yan watanni da suka shige kuma aka yanke wa Yesu hukuncin mutuwa. (Mat. 26:​57, 59; A. M. 6:​8-12) Mutane masu shaidar ƙarya suna zuwa ɗaya bayan ɗaya suna ba da shaida. Amma mutane da suke majalisar sun lura da wani abin ban-mamaki game da Istifanus. Sun ga cewa “fuskarsa ta zama kamar ta mala’ika.”​—A. M. 6:​13-15.

Me ya taimaka wa Istifanus ya natsu a irin wannan yanayin? Kafin a kai Istifanus gaban Majalisa yana hidimarsa da ƙwazo kuma ruhu mai tsarki ne yake taimaka masa. (A. M. 6:​3-7) Sa’ad da yake fuskantar wannan gwajin, ruhu mai tsarki yana tare da shi kuma ya taimaka masa. (Yoh. 14:16) Istifanus ya furta abin da ke rubuce a Ayyukan Manzanni sura 7 da gaba gaɗi sa’ad da yake kāre kansa. Kuma ruhu mai tsarki ya sa ya tuna abin da ke cikin ayoyi 20 ko kuma fiye da hakan a cikin Nassosin Ibrananci. (Yoh. 14:26) Ƙari ga haka, Istifanus ya sami ƙarfafa sosai sa’ad da ya ga wahayi game da Yesu yana tsaye a hannun dama na Allah.​—A. M. 7:​54-56, 59, 60.

Wata rana wataƙila mu ma za a yi mana barazana kuma a tsananta mana. (Yoh. 15:20) Amma ruhun Jehobah zai taimaka mana idan muna karanta Kalmar Allah a kai a kai kuma muna ƙwazo a hidima. Hakan zai sa mu sami ƙarfin jimre tsanantawa kuma mu natsu.​—1 Bit. 4:​12-14