Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Abubuwan da Allah Zai Yi

Abubuwan da Allah Zai Yi

Idan kana cikin damuwa, za ka bukaci abokinka ya taimaka maka, ko ba haka ba? Haka ne ya sa wasu suka ce Allah ba amini na gaskiya ba ne domin a ganinsu bai ɗauki wani mataki don ya magance matsalolinsu ba. Amma gaskiyar ita ce, Allah ya yi abubuwa da yawa da muke morewa kuma zai ɗau mataki don ya magance matsalolin da muke fama da su a yau. Mene ne Allah zai yi?

BA ZA A ƘARA YIN MUGUNTA BA

Allah zai cire mugunta ta wurin halaka ainihin mai haddasa ta. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana ainihin wanda yake haddasa mugunta, ya ce: “Duniya duka tana a hannun mugun nan.” (1 Yohanna 5:19) “Mugun” shi ne Shaiɗan Iblis, wanda Yesu ya kira shi “mai mulkin duniyar nan.” (Yohanna 12:31) Yaudarar da Shaiɗan yake yi wa ’yan Adam ne take haddasa wahalolin da muke sha a yau. Me Allah zai yi game da hakan?

Jehobah Allah zai yi amfani da Ɗansa Yesu Kristi don ya “halakar da wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato Shaiɗan.” (Ibraniyawa 2:14; 1 Yohanna 3:8) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Shaiɗan da kansa ya san cewa “lokacinsa ya rage kaɗan” kafin a halaka shi. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:12) Allah zai kuma halakar da duk masu aikata mugunta.​—Zabura 37:9; Karin Magana 2:22.

DUNIYA ZA TA ZAMA ALJANNA

Bayan Allah ya halaka masu aikata mugunta, zai mai da duniya ta zama aljanna inda mutane za su yi rayuwa a ciki har abada. Waɗanne abubuwa ne za mu sa rai cewa za mu gan su?

Cikakkiyar zaman lafiya. “Masu sauƙin kai za su gāji ƙasar, su sami farin cikinsu cikin salama a yalwace.”​—Zabura 37:11.

Abinci masu gina jiki a yalwace. “Bari a sami hatsi a yalwace a ƙasar, a sa amfanin gona ya rufe kan tuddai.”​—Zabura 72:16.

Gidaje masu kyau da kuma aiki na gari. “Za su gina gidaje, su zauna a cikinsu, za su shuka gonakin inabi, su ci amfaninsu. . . . Mutanena da na zaɓa za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu.”​—Ishaya 65:​21, 22.

Kana marmarin ganin lokacin da alkawuran nan za su cika? Nan ba da daɗewa ba, za su zama abubuwan da muke mora a yau da kullum.

BA ZA A ƘARA YIN CIWO KO MUTUWA BA

A yau, dukanmu mukan yi ciwo kuma mu mutu, amma hakan zai zama labari nan ba da daɗewa ba. Allah zai sa mu amfana daga hadayar da Yesu ya yi “domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya halaka, amma ya sami rai na har abada.” (Yohanna 3:16) Me zai zama sakamakon hakan?

Za a daina yin ciwo. “Ba mazaunin ƙasar da zai ce, ‘Ina ciwo,’ mutane masu zama a wurin, za a gafarta musu zunubansu.”​—Ishaya 33:24.

Mutuwa ba za ta ƙara kasancewa ba. “Zai halaka mutuwa har abada! Zai kuma share hawaye daga dukan fuskoki.”​—Ishaya 25:8.

Mutane za su yi rayuwa har abada. “Kyautar Allah ita ce rai na har abada ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu.”​—Romawa 6:23.

Za a ta da mutanen da suka mutu. “Za a tā da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.” (Ayyukan Manzanni 24:15) Za su amfana daga hadayar da Allah ya yi da Ɗansa Yesu.

Ta yaya Allah zai cim ma waɗannan abubuwan?

ZAI KAFA GWAMNATI TA GARI

Ta wurin mulkinsa wanda Yesu ne sarki, Jehobah zai mai da duniya aljanna inda mutane za su yi rayuwa har abada. (Zabura 110:​1, 2) Mulkin ne Yesu ya gaya wa almajiransa su yi addu’a a kai, ya ce: “Ubanmu wanda yake cikin sama, . . . Mulkinka ya zo.”​—Matiyu 6:​9, 10.

Yesu wanda shi ne sarkin Mulkin Allah, zai sarauci dukan duniya kuma zai dakatar da dukan wahaloli da ke duniya. Wannan Mulkin ita ce gwamnati da ta fi dukan gwamnatocin ’yan Adam. Shi ya sa lokacin da Yesu yake duniya, ya yi iya ƙoƙarinsa don ya yaɗa “labari mai daɗi na Mulkin” kuma ya umurci almajiransa su ma su yi hakan.​—Matiyu 4:23; 24:14.

Allah yana ƙaunar ’yan Adam shi ya sa ya yi musu waɗannan alkawuran. Mai yiwuwa hakan ya sa ka marmarin ƙara koya game da shi. Wane amfani ne za ka samu idan ka ƙara koya game da shi? Talifi na gaba zai bayyana hakan.

ABUBUWAN DA ALLAH ZAI YI Allah zai cire ciwo da mutuwa, zai haɗa kan ’yan Adam kuma zai mai da duniya ta zama aljanna